Makalu

Yadda ake hada tuna cutlets

 • Barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya na yau. Zamu koyi yadda za ki hada tuna cutlets a ne a yau.

  Abubuwan hadawa

  1. Tuna cutlets
  2. Garin tafarnuwa
  3. Albasa
  4. Breadcrumbs
  5. Kwai
  6. Gishiri
  7. Baking powder
  8. Seasoning
  9. Mangyada

  Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki zuba flour da breadcrumbs a cikin bowl ki dama shi da ruwa da dan kauri yadda zai iya kama jikin abu.
  2. Ki zuba tuna dinki a cikin bowl ki fasa kwai ki saka, ki saka maggi da tafarnuwa da yaji idan kina ra'ayi.
  3. Sai ki dinga diban wannan hadin kina mulmulawa a hannunki kaman kwallo, idan ki ka gama baki daya sai ki saka shi cikin freezer kaman 10 minutes.
  4. Idan kin fitar ki dora mai a kan wuta idan ya yi zafi kina daukan wannan balls kina sakawa cikin hadin flour kina sawa a mai. Idan ya soyu ya yi brown sai a sauke. A ci lafiya.

  Za a iya dubayadda ake hada swedish pancake da yadda ake hada sausage scotch egg da sauransu.

  Picture credit:Jameela Sayeed

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake hada pineapple crush

  Posted Nov 10

  Assalamu alaikum,barka da sake saduwa a cikin shirinmu na yau, a yau kuma zamu duba yadda za ki hada pineapple crush. Abubuwan hadawa Nikakken abarba Lemu 4 Sugar Gishiri Ruwa Cup sprite Yadda ake hadawa Za ki hada abarba da lemu sai ki niKasu,. Sai ki ...

 • Yadda ake hada coconut balls

  Posted Nov 10

  Assalamu alaikum warahmatullah, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau zamu koyi yadda ake hada coconut balls. Abubuwan hadawa Desiccated coconut (kashi biyu) Condensed milk Butter 1 tblspn Yadda ake hadawa Farko za ki nemi...

 • GARIN NEMAN GIRA

  Posted Nov 1

  GARIN NEMAN GIRA...!* *ZULAIHAT HARUNA RANO* Ya faru a gaske. Cikin nutsuwa ta miƙe tana naɗe sallayar da ta yi sallah a kai, bakinta yana motsin da ke nuni da addu'a take yi. A hankali ta kai dubanta kan ƙaton agogon bangon falon, wanda ya nuna mata karfe goma...

 • Ra'ayoyin mazan Arewa game da kayan ni’ima na mata

  Posted Oct 31

  Bayan ra'ayoyin mata da mu ka ji da irin alfanu da kuma rashin alfanu da kayan mata ke da shi wanda mu ka tattauna a makalar da ta gabata, to yau kuma za mu kawo muku bayanin bincike da na yi dangane da ra’ayoyin maza akan lamarin. Mun ji ra'ayoyi ma bambanta kwar...

 • Yadda ake hada ring chocolate cookies

  Posted Oct 31

  Barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau zamu gabatar da yadda za ki hada ring chocolate cookies(doughnut cookies). Abubuwan hadawa Flour Sugar Butter Kwai Cocoa powder Chocolate chips Baking powder Yadda ake hadawa Farko za k...

View All