Featured Create an Ad

faridat sweery musa's Album: Wall Photos

Photo 2 of 2 in Wall Photos

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*
💘 *HUBBAN SHADIDAN* 💘Na
*Farida Musa Sweery*
_follow me on Wattpad Faridatswerry_

_~BISMILLAHIRRAHAMNURRAHIM~_

Wannan labarin nawa ƙirƙira na yi ban yi dan wani ko wata ba, ina wanda ya ga wani abun da ya zo ɗaya da na shi a rashi ne, fatana kawai shine ku ɗauki darasin ciki kuyi watsi da abun da bai kamata ba, har kullum kofa a buɗe ta ke idan har kun ga na gaza ko na kuskure saboda Ni ɗin ƴar adam ce, Allah ya bani ikon tsabtace alƙalamina.


_Gaisuwa a gare ku masoya Sweery na nesa da na kusa, na sadauƙar da wannan shafin gaba ɗayansa a gare ku, son so_🌹💋


Page 1-5Duniya cike take da abubuwa iri-iri wasu na ban mamaki wasu na ban tausayi wasu kuma na ban takaici.

Gida ne babba wanda ya tara dukkan ahali kaman yanda al'adar mutanen da yake, a cikin gida ɗaya sai ka samu zuri'a tare a waje guda saboda ƙarfafa zumuncinsu, saɓanin mutanen yanzu da za ka samu kowa da gidansa. Wanda hakan ba karamin nakasu ya ke
Kawowa ba, duk da kuwa kasantuwar shi ma babban gidan akwai irin na sa ƙalubalen, musamman idan aka tsani mutum, to fa ya shiga uku.


Maryam shine asalin sunanta zaune take a harabar gidan tana karatun Novel ɗin Hausa kaman yanda ta saba a duk lokacin da ba makaranta, ta yi nisa da karatunta, kawai taji an fizge littafin, da sauri ta ɗago, karaf idanuwanta suka haɗu da na shi, ji tayi wani abu ya tsirgar mata kaman yanda take ji a ko da yaushe idan har ta haɗa ido da shi.

Zama yayi a gefenta yana, mai duba bangon littafin ga dukkan alamu sunan yake karantawa, "Baby sis Wai ke a ko da yaushe baki gajiya da karatun nan ne? Bama haka ba menene abun daɗi a cikin litattafan da kike karantawa?".

"Humm! yaya kenan, kai ai ba zaka taɓa gane wa bane shi ya sa, amma akwai abubuwan ƙaruwa sosai a ciki".

"Haka dai kika ce amma me yasa baki shiga cikin ƴan uwanki, na tabbatar suna can ɗakin Aunty amarya suna chapter".

Bata Kai ga bashi amsa ba, Zainab ta zo wucewa ga dukkan alamu ta dawo daga anguwa ne, tsaki taja, kana ta wuce tana mai cewa "aikin kenan kullum ayi ta raɓe-raɓe a jikin garu, Allah dai ya sa a ƙulla abun kirki kar a jawo jalli joga aka mana abun faɗi a cikin dangi, duk da wasu abun kunya ba dame su ba tun da dama can gadarsa suka yi".

"Ke da waye kike yi?" A zuciya Yaya ya tashi zai dake ta, da sauri na tashi na shiga tsakaninsu.

"Ka rabu da ita kawai ka riga da kasan halinta, nema take a tanka taje ta faɗawa Iya, ita kuma ta ba zata tambayi dalilai ba sai dai kawai hau mutane da masifa".

"Au iyan ce kike cewa masifaffiya? Ai wallahi kaman a gabanta kika faɗa".

Fuuuuu! ta wuce gida, ina ganin hakan, nace da yaya zan shiga gida, littafina kawai ya bani ya fita waje Ni kuma na shiga zuciya ta tana dukan uku-uku dan na tabbatar ba karamin husuma Zainab zata haɗa ba.

A hanyar da zai sada ka da kofarmu na ci karo da Iya, Zainab na biye da ita.
"Zo nan tsohuwar munafuka, wato wuyanki har ya yi riƙar da za ki ce mun masifaffiya, mu je wajen uwar ta ki idan ita ta ɗaure miki gindi ma na sa ni".


Ta sani a gaba ta yi har wajen Umma da ke shirin yin alwala, tun daga nesa ta jiyo hayaniyar Iya, a take zuciyarta ta bata tabbacin wani abun ne ya faru, saboda a kullu yamma Iya bata taɓa zuwa shashen idan ba wani abun aka ƙulla ba tazo ta ci mutuncin ta ta tafi.


"wato tijarancin na ki gaba-gaba ya ke yi, tun da har kin fara koyawa jini na? Ke anya ma kuwa Maryam jini ta ce? Na tabbatar jinina ba zai buɗa baki yace mun masifaffiya ba, amma a wani wajen bana ganin lefinki, jinin yahudawar da ke jikinki dole tsatsonki ma su gaba, a fili mutum kaman na Allah amma a cikin zuciyarsa ta rin shaɗananci ne kawai, yo Allah na tuba me za a yi da musuluntar rana tsaka?. Ki jawa ƴar ki kunne idan ba haka ba zata ɗebo muku ruwan dafa kanku".

Tana gama maganar ta ja tsaki ta fita, ita kuwa Zainab wani irin daɗi ne ya ratsa zuciyarta, a duniya babu abun da ta ke so kaman ta ga an kumtatawa Maryam, bata son ta ganta a cikin farin ciki ko yaya ne.

Hawaye Masu zafi ne suka biyo ta kuncin maryam, bata san yaushe zasu samu ƴanci da ita da Ummanta ba a cikin wannan gidan.


Vote
Like
Comment
Share.


Faridatswerry follow me on Wattpad.

No Stickers to Show

X