Rabiu ibrahim's Album: Wall Photos

Photo 1 of 1 in Wall Photos

Ya Allah don albarkacin sunanka ALQAWIYYU ka Qarfafemu ka karemu daga sharrin maqiya da mahassada.

Don Albarkacin sunanka "ALHAFIZU" ka kiyayemu daga sharrin talauci da bashi da sharrin kowanne mugu daga cikin halittu baki daya.

Don albarkacin sunanka ALWADUDU Ya Allah ka ha'da kanmu, ka Qara mana Qaunar junanmu.

Don albarkacin sunanka ASH SHAFIY Ya Allah ka bamu lafiya daga kowacce chuta, ka warkas da majinyatanmu da gida dana asibiti.

Don albarkacin sunanka AL GAFFARU ka gafarta mana dukkan zunubanmu, ka bamu ikon tuba daga kowanne laifi.

Don albarkacin sunanka AR RAZZAQ ka azurtamu da arziki na halal, ka yalwata ka sanya albarka cikin duk abinda ka bamu.

Don albarkacin sunanka AL GANIYYU ka wadatamu da ni'imominka na fili dana boye.

Don albarkacin sunanka AL QADIRU ALMUQTADIRU ka yassare mana samun dukkan bukatunmu damu da dukkan masu Qaunarmu, ka sanya taimakonka da kariyarka da kulawarka ta musamman acikin dukkan motsinmu, Ya mafi karamcin masu karamci.

Allah yi salati marar farko, marar karshe bisa Shugabanmu Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa baki daya da dukkan Salihan bayinka har zuwa ranar sakamako.

Comments

1 comment