Hafsat Moh'd Arabi's Album: Wall Photos

Photo 2 of 11 in Wall Photos

By:•Mimsqueen
Mrs.Isa
Hafsat Moh'd Arabi

https://www.wattpad.com/1036609770?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=HafsatMohdArabi&wp_originator=%2FXNEfjtPGSTmrR%2FIl287cx3qJw66GbSwi9MMBw%2BWYFSTh2kPuSDViE3cU7uEWqizbKxL94l7BxO3K8NcgqfBduTgVxYQ5rU%2FY4q2c85kOP%2FxiZqVdUXtp9JCcFEfZ19o

                Wasa Farin Girki ba'a Soma komai ba Boyayyar Masarauta...👌🅿️03

"Maad!".
Cak ya tsaya jin muryar mahaifinsa wanda baiyi tsamanin samu gida ba kasancewar irin wadan nan lokutan a mashaya ake samun sa.

" 'Dana yau naje fada". Da sauri Maad ya juyo yana duban mahaifin nasa. "Eh naje fada yau saboda mummunar labarin da naji dangane da guduwar matar waziri Sai dai...". Shiru yayi tare da sauke kansa kasa, Dan gyara tsayuwa Maad yayi haryanzu bai tanka ba.
" Natarar da Dalia da sar...tuf-tuf tirrrr". Mahaifin ya fada runtse idanunsa Maad yayi saboda wani irin radadi da zuciyarsa ke masa, kasa jurar tsayuwa yayi ya juya da niyar fita har yakai kofa mahaifinsa ya Kara Kiran sunansa.

"Ina maka magana kana tafiya?". Batare da yace komai ba juya ya kalla mahaifin nasa da jajayen idanunsa batare da yace komai ba yasa Kai fita. "Ikon 'Manaat' meke damun yaron nan haka?". Yayi maganar yana bin kofar da kallo.

FADAR SARKI AARON...

Zaune yake Kan kujerar mulkinsa yana dan karkada yar jaririyar wacce ta samu bacci. Tsura mata manyan idanunsa yayi kyawawa. "Ko meye sunanta?". Yayi maganar a hankali kamar rada.
"Ranka ya dade kabani ita a kwantar da it...". "Ba inda za'a kaita!". Yayi maganar Kamar tsawa. Da sauri baiwar taja da baya ganin yadda lokaci guda yanayinsa ya sauya sake maida dubansa kan jaririyar yayi, tuni baiwar tawuce.

"Mekikai ma Sarki Aaron naji yana daka miki tsawa?". Daya daga cikin bayin dake tsaye bakin kofar ta tambaya.
Tabe baki baiwar tayi tare da dan shafa kumatunta da hanunta. "Uhm, walh bakomai kawai dan nace yakawo yarinyar a kwantar naga tayi bacci". Ta basu amsa daidai lokacin da Maad ya shawo kwana amma Jin abunda suke fada yasa ya koma ya labe.

"Gaskiya na lura Sarki Aaron nada son yara musamman wannan yarinyar lallai tashiga ransa sos...". "Shhhh, yi Mana shiru baki San mekike fada ba". Daya baiwar ta dakatar da ita.

"Ae gaskiya nafada. Ke bakiga yadda yaketa lallaba jaririyar bane?". Ta fada cike da nuna abunda tafad'a hakan take nufi.
"Hakane amma...". Sai Kuma taja Baki tayi shiru.

"Amma me? kiyi magana mana". Dayar ta Kuma fada.

"Lawisa karki manta Dalia keda ikon komai a cikin wannan Masarautar ba sarki Aaron ba, idan taso Yar ta rayu tabbas zata rayu idan taki Kuma kunfi kowa sanin mezai faru". Wacce aka Kira da Lawisa shiru tayi jikinta yayi sanyi sosai.
"Amma latan kinfada haka ne Dan baki ga abunda nagani yanzu agun Sar...".

"Kuna nan Sai faman gulma kuke to yanzu dai zata shigo gwanda ku Kama gabanku tun wuri". Daya daga cikin bayin maza yafada Wanda yazo wucewa.
Nan take kuwa kowacce ta Kama gabanta ba wacce ta Kuma tanka ma dan uwanta.

Maad dake tsaye yana saurar abunda suke fada hankalinsa inyayi dubu yatashi, ba abunda yatsana irin yadda Dalia ke kashe mutane tana muzguna musu a wannan Masarauta ya zama dole ya kubutar da wannan Jaririyar daga hanun Dalia. Abunda yake fadi a zuciyarsa kenan a wannan lokacin haka ya juya yabar fadan.
Tunda ya dau yarinyar ya runguma yaji ya damu da lamuranta hakan yasa da ransa ya baci Kai tsaye yazo dan ganin ta Sai dai jin tana hanun Sarki Aaron ya juya yabar Fadar cike da damuwa. Ba abunda ke Kara tayar Masa da hankali illa Kisan wulakanci da Dalia tasa akaima mahaifin yarinyar yanzu ba uwa ba uba Dan me zata kasheta? Sai dai yasan tabbas Dalia bata da Imani zata iya kashetan.

Tunanin sane ya koma yadda zai ceci Yar jaririyar daga mutuwa. Da tunani yatafi.

Bayan lokaci me tsawo Bokanya Dalia ce ta bayyana a fadar Sai dai bata ga Sarki Aaron ba hakan ya tabbatar Mata ya kwanta. Kai tsaye dakinsa ta nufa cikin takunta na isa, Sai dai tana sa kanta d'akin taganshi kwance gefensa Yar jaririya ce yana rungume da ita wacce ta farka da alama baisani ba sai wasanni take ita daya.

Da sauri ta karasa gefen gadon. "Masoyina Masoyina!". Tafad'a cikin sauri tana dan tattabashi. Muryarta ne yatsorata yarinyar ta soma kuka, bud'e kyawawan idanunsa yayi akanta tare da da hamma yakai hannu yad'an murza idanunsa sakamakon baccin dake idonsa.

"Wacece wannan? Metake a nan?". Tajero masa tambayoyi Wanda Sai a lokacin hankalinsa yakai kan abunda ke gabansa, Nan take gabansa ya Yanke ya fadi dan Sam baiyi tunanin dawowarta fada a wannan daren ba.
"Ki kwanta gefe da safe zamu tattau...".
"Katashi yanzu nakeso mutattauna bazan hada gado da wannan abun ba!". Tafad'a tana nuna jaririyar wacce tayi shiru a yanzu saboda Dan karkard'ata da yake.

"Amma kinsan yanzu dare ne ko?". Ya Kuma fada tare da gyara kwanciyarsa.
Kai hannu tayi a zuciye zata fusgi yarinyar. "Ke!". Yafada cikin wani irin tsawa wanda baitaba Mata ba kusan tunda Suka taso bai taba Mata tsawa ba hasalima ita ke masa.
A tsorace taja da baya tana kallonshi da dara-daran idanunta masu ban tsoro tana zazzarosu a tsorace.

Tashi yayi zaune cikin Dana sanin tsawar daya mata. "Ki...". Kan ya Kai ga karasawa tuni ta bace a d'akin. Dafa kansa yayi da hanunsa tare da girgiza kansa, abunda baitaba zatan zai iya mata ba yau yamata hankalinsa inyayi dubu ya tashi musamman shida yake son lallabarta subar 'yar nan, kallon yar yarinyar yayi wacce ke cigaba da mimmikewa a jikinsa wacce bata San komai ba.

A d'akin bautar su ta bayyana banda huci ba abunda take da kaiwa da komowa duk da tsakar darene sosai. "Wacece yarinyar nan? A ina Aaron ya samo yarinya?". Ta Shiga jero ma kanta tambayoyi. Shiru tayi ta cigaba da kaiwa tana komowar.
'ko yar...to ina uwar meyasa yake tare da jaririyar?". Sai a lokacin ta tuna da tasa a dubo mata matar waziri da yarsu ba shakka wannan Jaririyar yar Waziri ce da matarsa. Wani Karin takaicine ya taso Mata. "Inhar hakane ina uwar?". Ta kuma ma kanta tambaya.

Shiru tayi nadan lokaci tana nazari. "Kai bazaiyuba dole su mutu daga 'yar har uwar Kamar yadda na kashe Waziri amma....". Kome ta tuna Sai ta Kara bacewa lokaci guda.

Kwance yake yana bacci da alama baccin nasa yayi nisa ta bayyana d'akin. Zatai magana amma ganin yanayin fuskarsa yasa ta kasa furta komai ta tsura mishi idanu.
Yayi kyau sosai especially yadda yake baccin Kamar haryana dan murmushi da alama Yana jin dadin mafarkin da yake.

Murmushi tayi me dan sauti tana cigaba da kallonsa zuciyarta na saka Mata abubuwa dayawa game dashi. Tana tsananin son Maad a rayuwarta Sai dai shi sam yaki amincewa da bukatarta tayi duk abunda zatai dan janyo hankalinsa amma ta kasa duk ta hanyar data bullo sai ya kauce gashi bataso tabi ta tsafi sam akansa.

Maad da Aaron da Dalia kusan tare suka taso su ukun duk da Maad bakowa bane haka ba dan kowa bane haka nan suka shaku da juna tun wani lokaci da suka hadu suna yara Dalia ta Kasance tana tsananin son Maad kusan da soyayyarsa ta taso a zuciyarta amma burin mahaifiyarta da nata tun tana yarinya shine Mulki wanda yafi tasiri a zuciyarta shine dalilin kasancewarta da Aaron Sai dai har yau ta kasa hakura da son da take ma Maad wanda tunda ya gano manufarta kansa yake janyewa da ita duk wata kofa ta sanayya tsakaninsu ya toshe. Shikuma Sai ya Kasance jarumi sosai a cikin Masarautar duk da karancin shekarunsa a yanzu in ana zancen Jarumai a Kasar Larza Sai ansa sunansa a ciki.

Juyi yazoyi Kamar wanda akace bud'e idonka ya bud'e sai ganinta tayi tsaye gabansa tana kallonsa tana murmushi, a dan firgice ya murza idonsa ba kowa bace itance dai wacce idonsa ke nuna masa, Da sauri ya ya tashi ya sauko daga kan dan gadon nasa ya da'ura gwiwowinsa a kasa. "Ki gafarceni ranki ya dade bansan da shigowarki ba". Ya fada da sauri tare da kaskantar da kansa kasa.

Maganarsa ce ta dawo da ita daga duniyar tunani data shiga da sauri ta gyara tsayuwarta tare da b'ata fuskarta a lokaci guda. " Ba wannan ya kawo ni ba ina Matar Waziri da jaririyar ta?". Tayi tambayar cikin dakiya.

Dan dagowa yayi da sauri ganin shi take kallo yasa yayi saurin sake maida  kansa kasa. "Kai nake saurare!". Tayi maganar ciki dan tsawa. Shirune ya ziyarci d'akin na dan lokaci tana kallon Maad wanda ke sunkuye.

Masha Allah! Nan zamu dakata a wannan Labari Sai mun sake haduwa in Allah yakaimu da Rai da lafiya...

Comments

0 comments