jamil Bashir's Album: Wall Photos

Photo 5 of 17 in Wall Photos

Kai Jama'a Yanzu Dan Allah haka Zaa cigaba a harkar samar da tsaro a fadin kasar nan ?

Ƴan Taadar nan kullum zuwa suke da sabon salo ita kuma Gwamnati kullum sai dai tace tayi Allah wadai ko tayi Gargadin su aje Makaman su ko ta nuna bacin ranta akan abunda yake faruwa.

Tun ana tare hanya ana ɗibar Jama'a tareda kar'bar kudaden fansa har ta kaiga yanzu Makarantu ma akebi ana kwasar Ɗalibai a tafi dasu bayan wahalarwa a kuma nemi kudin Fansa.

Bisa ga dukkan Alamu wasu Tsirarun Mutane sun Maida wannan Lamarin wata hanya ta neman Kudi a cikin Sauƙi kuma sunga suna samun nasara Dan haka babu ranar dainawa.

A koda yaushe rashin aiwatar da Hukunci ga wanda aka samu da laifi yana kara sanyawa wasu su aikata laifi irin wannan, Allah ya kyauta ya kawo mana karshen wannan Ibtila'in Amin.
Copied

Comments

0 comments