Featured Create an Ad

Mukhtar Musa Karami Abu Hisham's Album: Wall Photos

Photo 50 of 51 in Wall Photos

WASA ƘWAKWALWA
20/11/2020

GABATARWA
MUKHTAR MUSA KARAMI
ZAHRADDEN NASIR
UMMYTER ABDALLAH


Tukwici
Kyautar manyan littattafan adabi ga waɗanda sukayi na ɗaya da na biyu har zuwa na uku.

Q1) Kawo sunan wanda ke gabatar da Shirin Adabi Madubin Rayuwa a Manhajar Bakandamiya.

a) Wace rana ya fara shirin?

b) Kawo misalan da ya bayar a shirinsa da ya wuce.
(Maki 20)

Q2. Kawo sunayen marubutan litattafan nan.
A) Malam Zalimu
😎 Dinkin Kwalba
C) Zuciyar Mutum
D) Rubutacciya
(Maki 20)


Q3. Ƙarasa jerin Karin Maganar da ke ƙasa.

A)Ina ruwan makaho...
😎Makaho baya shakkar...
C)Ruɓaɓɓun haƙora...
D)Gani da ido...
E)Ɗaurarriyar magana...
F)Ɗan Akuya...
G)Duk ɗaya...
H)Ƙaryar ƙasa...
I)Ina sani...
J)Gani ga wane
(Maki 20)


Q4)1. Waɗansu mata ne guda biyu:
A- Ta farko tana rayuwa ne ta hanyar cin abinci da shaƙar iska, amma da zarar ta sha ruwa to wa'adinta ya cika, za ta mutu!

B- Ta biyu kuma tana da ido guda ɗaya jal, amma fa duk da haka ba ta gani, makauniya ce.

Waɗanne mata ne?
(Maki 20)


Q5. A Hausa akwai KARIN MAGANA iri-iri, kawo iri uku da misalansu bibbiyu.
(Maki 20)

Za a tura amsoshin tambayoyin ne ta akwatin masu gabatarwa,sannan bayan ƙarfe bakwai na safiyar gobe Asabar kowa zai je group din Marubuta da ke manhajar Bakandamiya ya ɗora nasa.

Za a rufe ƙarɓar amsoshi da ƙarfe bakwai na safiyar gobe Asabar .

No Stickers to Show

X