Zaharadden Nasir's Album: Wall Photos

Photo 8 of 16 in Wall Photos

FARASHIN KASHE KAI YA KARA SAUKOWA...

Mutanen kasar Japan na daga cikin mutanen da suka fi yawan masu kashe kansu a fadin duniya, domin ko a shekarar 1997, lokacin da yanki Asiya yayi fama da matsalar tattalin arziki, a shekarar ance kaso 34.7% na adadin mutanen da suke kashe kansu a fadin Duniya, 'yan kasar Japan ne.
Hukuncin mutum ya kashe kansa, na daga cikin hukunce-hukuncen shari'a a kasar Japan. Wanda suke kira da "Seppuku" Ma'ana mutum ya yanke cibiyarsa, wanda yin hakan kuma mutuwa ce.
Ko a lokacin yakin duniya na biyu, sojojin kasar Japan din sunyi seppuku ga sojojin da suka juya baya wa abokan gaba.
Watakila wannan dalilin ne yasa mutanen kasar suka tasirantu da kashe kansu a yayin da suka gaza a inda suke ganin zasu iya, ko kunyata a inda bai kamata suji kunya ba. Su da kansu su kan bawa mutum shawarar ya kashe kansa kawai da zarar ya gaza cimma wani buri nasa.
A shekarar 2003, mutanen da suka kashe kansu a Japan sun kai 34,427.Bincike ya tabbatar da cewa 70% na masu kashe kansu a kasar maza ne da shekarunsu ke a tsakanin 20 zuwa 44.
A 2007 hukumar NPA ta fitar da wasu dalilai guda 50 da su ne dalilan da suke sa mutane ke kashe kansu.
49% dalili ne da ya shafi lafiya ta zahiri ko ta kwakwalwa, (kamar damuwa)
Sai kuma dalilin tattalin arziki (kamar talauci) wanda ya kwashi 17%.
Sai matsalar da ta shafi iyali yana da 3%
Sai matsalar wajen aiki wanda ke da 10%
Sai mu'amalar yau da gobe, wadda a ita aka fi samun bugawa zuciya, tana da 4%. Sai kuma sha'anin karatu. Wanda da zarar mutum ya gaza samun kyakkyawan sakamako, sai kawai ya kashe kansa.
Ko a shakarar nan ta 2020 da muka yi bankwana da ita, hukumar lafiya ta kasar ta sanar da cewa mutane 20,919 ne suka kashe kansu a kasar ta Japan.

_Ko a yankinmu, ana samun iyaye, yayye ko shugabanni da ke jifan na kasa da su da kalmomin tsoratarwa, irin su; "kashinka ya bushe" "ka mutu kawai!" Da zarar sunyi wani kuskure. Lallai ya kamata a kiyaye da irin wadannan kalmomin, don gudun kada yara su dinga jin cewa hukuncin mutum ya kashe kansa shi yafi sauki a kan abinda zai biyo bayan wata gazawarsa, ko jin kunya._

Zaharadden Nasir

Comments

5 comments