Uwargidan gwamnan jahar Kebbi, Dr. Zainab Shinkafi Bagudu ta samu karramawa ta musamman yayin da lashe lambar yabo na Silverbird Man of The Year Award, Special Achievement a sakamakon ayyukanta na yaki da cutar daji. Dr Zainab dai ita ce ta samar da gudauniyar Medicaid mai fafutika akan yaduwar cutar daji a Nijeriya, kuma ita ke da mallakin cibiyar gwaji ta Medicaid. Gwamnan jahar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya kasance a taron karramawar, wanda aka yi a dakin manyan taro na otel din Eko da ke jahar Lagos domin ya mara wa matar shi baya.

click to rate

Comments

3 comments