Recent Entries

 • Dabarun rubutun labari 01: Raunin labari a sikelin adabi

  Dabarun Rubutun Labari zai rinƙa kawo muku hanyoyin ko dabarun rubuta labaran Hausa ta amfani da salo mai armashi da karsashi. Idan aka bibiyi shafin daga farko har ƙarshe za a sami tagomashin rubuta labarin Hausa wanda zai ja hankalin mai karatu, musamman ga masu sha’awar shiga gasannin ƙagag...
  comments
 • Wa yake cin riba a hauhawar farashi, ‘yan kasuwa ko gwamnati?

  A ci gaba da kawo muku karon battar fasahar da marubuta ke yi a muhawarar da Bakandamiya ta shirya ta kuma ɗauki nauyin aiwatarwa, a yau za ku ga yadda Hazaƙa Writers Association da Yobe Authors Forum suka ɓarje guminsu tare da ruwan hujjoji a maudu’I mai taken Wa yake cin riba a hauhawar fara...
 • Yadda za ku kare kanku daga cutar sankara, wato cancer

  Cutar sankara, ko cancer a Turance, cuta ce dake haifar da wani tsiro a jikin bil'adama wanda ke shafan ƙwayoyin halitan bil'adama wanda kuma ke kaiwa ga nakasar wani ko dukkan ɓangaren na jikin bil'adama. Kuma sauda yawa ma dai hakan kan kai ga rasa rayukan masu ɗauke da wannan cuta. A shekara ta ...
 • Illar Furuci 7 Na Halima Abdullahi K/Mashi

  Ku latsa nan don karanta shafi na 14. Shafi Na 15 Fatima ta sauke ajiyar zuciya sannan ta dubi Fadila "Dan girman Allah ki min shiru muyi magana, wallahi dan ke ce amma bana tattauna maganar jinsin namiji in har shi din ba ahalina ba ne." Fadila ta numfasa cikin dashashshiyar murya ta c...
 • Gwagwarmayar Kiki Mordi, yar jarida mai binciken sex for grades

  Wata matashiya, haziƙa, ‘yar gwagwarmaya, jajirtacciya wacce yanayin rayuwa ya mayar da ita jaruma, wacce kuma ta samu ɗimbin nasarori da ƙalubale tun a shekarun ƙuruciya – wannan ita ce Nkiru Mordi wacce ake ambato da Kiki Mordi. An haifi Nkiru Mordi a ranar 12 ga watan Agusta, 1991 a ...
 • Alkalumar masana game da cutar sankarar mama (breast cancer)

  Sankara dai tana aukuwa ne a lokacin da ƙwayar halitta mai illa ta fara hayayyafa fiye da yadda ya kamata. Wannnan hayayyafar ƙwayar halittar ya kan kai ga matakin ciwo mai tsanani, kuma a wasu lokutan ya kan kai ga mutuwa. Sankara dai ta kan kama mata da maza a sassa daban-daban na jikinsu. Alkall...
 • Tekun Labarai: Sharri Jakada Ne

  Ku latsa nan don karanta labarin Afuwa ƙwaya Ce, Ka Shuka Ɗaya Ka Girbi Goma. An yi wani attajiri da ke da dukiya mai yawan gaske, ana kiransa Abu Tammamu. Saboda yawan dukiyarsa, bai san iyakacin abin da ya mallaka na daga gidaje da gonaki da dabbobi da bayi da sauran kadarori ba. B...
  comments
 • Illar Furuci 6 Na Halima Abdullahi K/Mashi

  Ku latsa nan don karanta shafi na 12 da 13. Shafi Na 14 Tana isowa ta dubi Mama tare da mika mata wayar "Ga mamansu Sumayya za kuyi magana." Mama ta amshi wayar ta saka akunne ta na fadin salamu alaikum jin shiru yasa ta dubi fuskar wayar tare da fadin "La kinga ta katse." Fati ta amshi wayar ta...
  comments
 • Yanayin so da bukatuwarmu gare shi

  Zamantakewar aure, zamantakewa ce mai wahala, matuƙar wahala kuwa. Sai dai da zarar ka fahimci tana da wahalar, sai ta zama mai sauƙi a gare ka. Domin fahimtar tana da wahalar shi zai ba ka damar neman iliminta. Shi kuma iliminta sai ya ba ka damar samun sauƙin ta. A shirinshi da ya saba gabatarwa ...
  comments
 • Takaitaccen tarihin Fela Kuti

  An haifi Olufela Olusegun Oludotun Ransome-Kuti a ranar Asabar 15-10-1938, a Abekuta ta jihar Ogun. Iyayensa manyan mutane ne domin Mahaifiyarsa Fummilayo Ransome-Kuti, 'yar gwagwarmaya ce, mai fafutukar kwato 'yancin mata. Mahaifinsa Isra'el Olodotun Ransome-Kuti, babban limamin coci ne, shugaban ...
  comments
 • Me ku ka sani game da cutar Hepatitis?

  Idan aka ce Hepatitis, to ana nufin ciwon hanta kenan a Hausance. Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta na...
  comments
 • Tekun Labarai: Afuwa ƙwaya Ce, Ka Shuka Ɗaya Ka Girbi Goma

  Ku latsa nan don karanta labarin Dogaro Ga Allah Jari. Cikin ƙasashen Mongol an yi wani babban Sarki mai yawan jarumai ana kiran sa Bihikatu. Shi wannan Sarki jarumi ne amma mugu ne na ƙin ƙarawa. Tun da yake bai taɓa yin afuwa ga wanda ya saɓa masa ba. Ba a taɓa ganin dariyarsa ba s...