Makalu

Blogs » Ra'ayoyi da Tahalili » Ire-iren cin zarafi da wasu iyaye ke fuskanta a wajen 'ya'yansu

Ire-iren cin zarafi da wasu iyaye ke fuskanta a wajen 'ya'yansu

 • Tun tsawon shekaru daruruwa da suka gabata ‘yan neman ‘yanci ke ta gwagwarmaya akan samun ‘yancin mutanen da ke fuskantar cin zarafi. ‘Kungiyoyin gwagwarmaya daban-daban sun yi aiki tukuru don ganin bayan cin zarafi daban-daban da ke faruwa a duniya. Irin wadannan gungiyoyi sun hada da ‘yan nemawa mata ‘yanci, wato feminist movement a Turance, da masu ikirarin neman 'yanci ga mutanen da ke fuskantar cin zarafi a cikin gida, wato domestic violence a Turance. Ko shakka babu wannan kokari da kungiyoyi ke yi ya rage da yawa daga cikin cin zarafi ko zali da ake yi ma wasu mutane a cikin al’umma sosai. To ammafa akwai wasu na’ukan cin zarafin da ko kusa ba a basu kulawan da ya cancanta ba, misali shi ne irin cin zarafi da iyaye ke fuskanta a wurin 'ya'yansu.

  Wata kila su wadannan cin zarafi da ake ta faman gani kawo karshensu a doron kasa basu da sarkakiya ne sosai koko saboda dai alaka da ke tsakanin mai cin zarafin da wadda ake ciwa, alaka ce ta “mai karfi” da kuma “mara karfi” wadda duk mutumin da ya tsaya yana fada akai akan mai da shi jarumi, wato hero a cikin al’umma. Wata kila shi yasa sauran cin zarafi aka manta da su ko kuma ba a basu kulawar da ya kamata ba duk da cewa suma sunan nan cikin al’umma.

  Kamar yadda na ambata a baya, daya da ga cikin irin cin zarafi da a maganarsu shine cin zarafi da wasu ‘ya’yan kan yi wa iyayensu. Irin wannan cin zarafi na faruwa ne a inda za ka ga da yana bawa iyayensa wahala ta hanyar musu dabara ko magudi da wayo ko kuma yi musu barazana. Wannan shima yana da ga cikin nau’in domestic abuse a Turance, amma ba a magana akan shi.

  Wani masani mai suna Cottrell B, ya bayyana cewa cin zarafin iyaye shine “any harmful act of a teenage child intended to gain power and control over parents.” Ma’ana shine, duk wani hanya da yara, musamman ma matasa kamar teenagers, ke bi don ganin sun nunawa iyayen na su fin karfi da kuma samun iko akan iyayen ba tare da son ran su ba.

  DubiRashin kulawa da tarbiyyar da namiji ba ya gyara na ya mace

  Duk da cewa ana ganin wannan ba wata matsala ba ce da ta ke bayyananiya, amma kuma dai ai duk wani mutum mai hankali da lura zai iya ganewa in har wani na aikata wannan aika-aikar kusa da shi. Saboda alaka da ke tsakani da da mahaifa za ka ga cewa yana da wuya mutane su iya shiga tsakani kuma ma su kan su iyayen yawa-yawan lokaci basa iya korafin wannan matsalar in ta na faruwa. Wannan yanayin a tunani kan kara jefa su iyayen a wani yanayi mai tsanani da kuma kunci.

  Shi wannan matsala na cin zarafin iyaye kan dauki salo kala-kala, kama daga cin zarafi da baki wajen fada musu mugayen kalamai, da kuntata musu ta hanyar nuna halayya na musgunawa wadda zai sa zuciya cikin bakin ciki, har izuwa ga hana taimakon su da abu kamar kudi ko makancin haka. Bara mu dauki ire-iren cin zarafin daya bayan daya kamar haka:

  Cin zarafi da baki (verbal abuse): Wannna irin cin zarafi ya kan kasance kamar musu da su cikin rashin ladabi da yi musu tsawa, da kuma yawan kwabe musu baki in suna magana da nuna halin ko in kula in anazance da su wajen bada amsa na mannin hauka da raini. Wani sa’in kuma za ka ga ‘ya’yan sun kasace masu zargin iyayen a duk lokacin da wani abu ya baci, ma’ana komai dai ya faru sai su ga laifin su iyayene ba wai su (‘ya’yan) ba.

  Cin zarafin da ya shafi jiki (physical): Wannan irin hanyar amfi ganin shi a zahiri. Za ka tarar wasu iyayen na fuskantar matsalar cin zarafi daga ‘ya’yansu har ya kai ga sun (‘ya’yan) kai misali duka da kuma yi musu kulle da hana musu fita da kuma yi musu abubuwa da dai zai musu lahani ga jikinsu, kamar buge su ko kuma yi musu barazanar kashe su da makamantan hakan. Duk wannan na faruwa ga wasu iyaye, subhanallah!

  Cin zarafi ta hanyar kuntatawa (emotional abuse): Wani lokacin ‘ya’yan da kan ciwa iyayensu zarafi kan rikide su nunawa duniya cewar iyayenne kan ci musu zarafi alhali sune suke yi. Za ka tarar irin wadannan ‘ya’ya wani lokacin kan nunawa iyayen kamar sun haukace. Wani lokacin su rika nuna mummunan bacin rai suna tuma suna tashi duk dai don nunawa iyayen bacin ransu. Sukanyi hakan ne don ai kawai su kidima iyayen wajen musu duk abinda suke so. Wani lokacin kuma nunawa iyayen kaskanci suke yi da cewa ai su iyayen basu cimma komai a rayuwar su ba.

  Cin zarafi ta hayar dukiyarsu: Wani lokacin irin wadannan ‘ya’ya sukan saka iyaye gaba da sata na kudi kodai na wani abin da su iyayen suka mallaka. Wasu ‘ya’yan kan kai ga karbar bashi alhali ba su da abin biya dole ya sa sai iyayen sun biya musu. Wani salon cin zarafin kuma shine su rika neman iyayensu sai sun musu wani abunda suka san zahiri ya fi karfin iyeyen na su nesa ba kusa ba.

  Za a iya duba:Ingancin rayuwarka/ki shine amfani da dama da lokaci

  Dalilai da kan jawa cin zafin iyaye a wajen ‘ya’yansu

  1. Daukan fansa: Da yawa daga cikin ‘ya’yan da ke cin zarafin iyayensu na yin haka ne don daukan fansa. A ganin su wadannan yara ai suma iyayensu sunci zarafinsu lokacin da suke kanana saboda haka yanzu girma ya zo lokacin daukan fansa ya yi musamman ma idan su wadannan ‘ya’yan suna ganin sun samu ci gaban rayuwa.
  2. Ganin cin zarafin da ake yi a gida: A wasu gidajen cin zarafi kamar wani abin ado ne. Uba ya ci zarafin mahaifiyar ‘ya’yansa a kullum ba tunani bare tausayi. A irin wadannan gidajen ya zame musu sabo. To yaro in ya tashi a irin wannan yanayi sai ya ga abin kamar ba komai ba ne ko kuma wani sa’in yayyu ne ke cin zarafin iyayensu kannensu na gani, to suma kannen da sun tashi sai su dora a wurin da aka tsaya.
  3. Fama da ciwon da ya shafi kwakwalwa (mental illness): Wani lokacin za ka tarar yaro na fama da ciwon irin mental illness amma ba a kula ba (musamman a al’adunmu na Africa) har abin ya zamo ba dadi ya kai ga yaro ya shiga yanayi na bakin ciki da damuwa mai tsanani (depression and anxiety). To irin wannan kan haifar da cin zarafin iyaye a wajen irin wannan yaro saboda zai ga wannan hanyar ce kawai zai bi a kula da shi ko kuma ya ji dan sauki a jikinsa.
  4. Matsala ta tarbiya da wasu iyayen suke bayarwa ‘ya’yansu : Wani lokaci a kwai iyaye da kan sakewa ‘ya’yansu har sakewar ya yi yawa sai ka ga ‘ya’ya ba kwaba sam - sai abinda suka ga dama suke yi. To yawancin mutane kuma yadda Allah Ya yi su shine idan suka samu wuri su kan wuce gona da iri. Sun yi wani abu mara kyau yau kuma ba a tsawata musu ba ai sai su kara gobe har fiye da na baya. Da haka da haka sai su kai matsayin da ba su jin shakkan iyayen na su har kuma wani lokacin abin ya kai ga cin zarafi ba tare da sunma san suna yin ba dai-dai ba.
  5. Tsabar son kai (narcissism): Wannan shima yana alaka da tarbiya. Wasu lokaci wasu daga cikin iyaye da suka yi tarbiyar ‘ya’ya suna masu nuna musu cewa sun fi kowa kuma zasu iya aikata duk abinda suke so ba tare da jin tsoro ko shakka ba, to wannan yanayi kan mayar da wasu yaran su zama masu tsabagen son kansu. Su rika ganin kansu kamar sun fi kowa kuma dole kowa ya yi yadda suke so, aje-aje har wannan halinnasu ya kai ga juyowa kan iyayen suna ci musu zarafi da wulakanta su, domin, a ganinsu ba wadda ya isa sai su.
  6. Talauci/fiskantar cin zarafi a yaranta: Bincike-bincike da dama da aka yi sun tabbatar da cewa yaron da ya fiskanci talauci ko cin zarafi a yarantanshi kan tashi da kangararen zuciya. Wannan irin tausayi da kuma kawaici da dan adam ke da shi, su yawancin irin waddannan yara ba su da shi saboda haka ko da ma iyayensu ne basa tausaya musu. Za su iya cin zarafin iyayensu ba tare da abin ya dame su ba.
  7. Shaye-shayen kayan maye: Yaran da kan yi shaye-shaye suma sukan ci zarafin iyayen su mafi akasarin lokaci domin shi saye-shaye ba ta’ada ba ne da zai taimaka musu wajen jin kan iyayen na su ko tausaya musu.
  8. Al’ada: Duk da cewa ba wata al’ada ko inci ta’ada da gashi za a ce wai ya bawa ‘ya’ya daman cin zarafin iyayensu karara, amma al’adan nan da kan bawa da na miji fifiko fiye da mata na jawo wasu ‘ya’ya mazan su raina iyayensu mata har ya kai ga cin zarafi. Misali, wani lokacin idan uba ya mutu ya bar uwa da ‘ya’ya, za ka tarar da namiji shi kan zama uban a gidan, saboda kasan cewar shi kamar uba kuma shi yakan kawo yawancin abin bukata sai ya zamanto ya mai da mahaifiyarshi kamar ba komai ba, sai abinda ya ke so za a yi a gidan in kuma ta ki to abin sai ya zama cin zarafi da wulakanci.

  Wasu karin dalilan sun hada da:

  1. Rashin girmama iyaye saboda rauni da suke da shi
  2. Mutum mai yawan zafin rai
  3. Kallace-kallacen wasanin tashin hankali kamar a TV, da wake-waken zamani na music da makamantansu kan sa yara su za ci wannan dabi’a ta cin zarafin iyaye ba wani abu ba ne
  4. Rashin bawa ‘ya’ya masu rauni kamar masu nakasa haka ko masu fama da cutar da ta shafi kwakwalwa cikakken kulawa

  Abin lura:

  Da na miji ko mace kan ci zarafin iyaye: Ba wani banbancin jinsi wajen cin zarafin ga da mai cin zarafin iyaye, zai iya kasancewa na miji ne ko mace ce.

  Iyaye mata ko kuma wasu daban masu hakkin kula da yara: Yawanci wadannan sunfi kowa fiskantar wannan irin cin zarafin.

  Banbance-bancen kabila ko kuma matsayi a cikin al’umma: Bincike ya nuna cewa ba bu wani alaka da matsayin mutum cikin al’aumma ko kabilarsa ke da shi da cin zarafin iyayensa – mai cin zarafin iyaye dai mai cin zarafin iyaye ne - sai dai kuma wata kila irin al’adannan mai bawa maza fifiko mai yawa akan mata.

  Ana iya dubaShawarwari guda 8 don inganta tarbiyyar yara

  Hanyoyin da za a bi a kiyayen cin zarafin iyaye, da kuma yadda za a magance su da kuma shawarwari

  Irin illar da cin zarafi kan yi wa iyayen da ke fiskantar cin zarafin ‘ya'yansu yana da girma da takaici mai yawa. Yawancin iyayen da kan tsincin kansu cikin irin wannan hali sukan ji tamkar su kan sun gaza ne kuma ma abin kunya ne a gare su a ce ‘ya’yansu na cikinsu suna cin zarafinsu. Wannan dalili kan sa da yawa daga cikin irin iyayen da ke cikin wannan yanayi su yi shiru su ki yin magana. Kuma ko da sun yi yawanci ba a taimaka musu sai dai ma a zarge su.

  Kamar ko wani irin cin zarafi, abu mai  muhimmanci shine iyaye su sani cewa basu kadai ke fiskantar wannan matsala ba kuma ba a kansu aka fara ba sanna ba akansu za a kare ba, saboda haka su sani cewa basu cancanci halin da suke ciki ba. Sannan ina kara tabbatar musu da cewa za su iya samun ‘yancinsu.

  Ga kadan daga cikin shawarwari da ya kamata iyayen su duba:

  1. Da farko dai shine kokari a cire wannan tunani na damuwa da cewa sun gaza ba za su iya taimako kansu ba koma ba mai taimaka musu. Su yi kokarin gaya wa wani da suka yarda da shi ko kuma a tuntubi kwararru masu bada taimakon sunanan in har an bincika.
  2. Fiskantar yaran da wannan zancen. Wani lokacin sai iyayen sun nunawa yaran bacin yansu kuma sun musu dalla-dalla akan yadda wannan halayyan na su ke bata musu rai. Dole iyayen su zamanto sun yi tsayuwar daka anan. A hana su abubuwan jin dadi kamar su computer da waya idan yaran kanana ne, a musu barazanar ba za mayar musu ba sai halayyarsu ya canza.
  3. A nemi taimakon kwararru idan aka zaci da na fiskantar matsalan ciwon da ya shifi kwakwalwa wato mental illness a Turance.
  4. Dole wani lokaci iyaye su tsaya-tsayuwan daka idan irin wa’yannan yara suka nemi su ci musu mutunci. Su nuna musu karara cewar baza su dauki wannan halayyar ba. Su kiyayi duka ko kuma idan ya kai ga har ‘ya’yan sun daga hanu za su duke su to su nemi mafaka  kada su yarda su hada jiki da su.
  5. Daga zaran abin ya kai ga duka, to su yi maza su gayama hukuma don nemarwa kansu ‘yanci da kuma kariya.
  6. Sannan kar iyaye su rika biya musu bashi idan har wannan hanyar suka dauka, domin biya musu bashin kamar an basu lasisin ci gaba da ciwo basukan ne don sun san za a biya.

   Ga wasu daga cikin hanyoyi da iyaye ya kamata su bi don kaucewa fiskantar cin mutunci daga ‘ya’yansu

  1. Jaddada dabi’ar son juna a tsakanin iyali
  2. Kula wajen bada tarbiya. Ya kasance iyaye sun zama tsayayyu wajen nunawa ‘ya’ya abin da za su yi, sannan su kasance masu yin hukunci cikin hikima idan an samu sabani. Kar a yawaita hayaniya da zage-zage.
  3. Nemarwa ‘ya’ya taimako daga zaran sun fara nuna wani dabi’a musamman na zafin rai da kuma dan hali haka nan ko kuma shiga damuwa da bacin rai.
  4. Yanke duk wani alaka (aure ko abota) da iyaye suke ciki wadda a kwai cin zarafi a ciki. Sannan a tabbatar an kare su daga kalace-kalace da ke nuni ga tashin hankali irin na cikin fina-finai da kuma na wake-waken zamani.
  5. Iyaye su kasance sun zama abin koyi wajen nuna dabi’a na kwarai ga ‘ya’yayensu

  Yadda za a taimakawa iyaye da ke cikin irin wannan hali

  1. Arika saurarensu idan sun zo suna maganar matsalolinsu
  2. Kar a rika dora musu laifi a yayin da suke cikin wannan bakin ciki. Ko da mutum ya fiskanci a matsalan a kwai laifinsu, a basu uzuri sai a hankali za a nuna musu cikin hikima.
  3. Ya kasance a rike sirrinsu. Duk mutumin da yazo yana gaya maka matsalarsa to ya yadda da kai ne, to kai kuma yana da kyau ka mutunta wannan aminci. Koda wasa kar aji kar a gani a bakinka.
  4. A basu karfin guiwa, a nuna musu cewa basu cancanci wulakanci daga wajen ‘ya’yansu ba sannan a kara jaddada musu basu kadai ke fama da wannan matsalar ba.
  5. A taimaka wajen hada su da mutanen da za su taimaka musu ko kuma hada su da kwararru a wannan fannin don su taimaka musu ko sa sake sanin darajar kansu.
  6. Aga yadda za a yabe su da wani kokari da suke da shi don su dan sami jin dadi a ransu

  Allah Ya taimake mu, Ya rufa mana asiri, Ya shirya mana zuri'a sannan Ya kuma bawa duk iyayen da ke fiskantar wannan matsala daga wajen ‘ya’yansu salama.

  Za a iya dubaTasirin camfe camfen Hausawa cikin tarbiyyar

Comments

8 comments