Makalu

Bincike ya samar da hanyar buga sassan dan adam

 • Wani binciken kimiyyar lafiya dake cibiyar binciken kiwon lafiya na Jami’ar Wake Forest, watau Wake Forest Institute for Regenerative Medicine da ke North Carolina na kasar Amurka, ya samar da sabuwar hanyar buga sassan dan Adam. Kimiyyar wacce ake wa ambato da bio-printing na amfani ne da takanolojin nan na 3D printing don buga sassa kamar su kunne, koda da dan yatsa.

   

  Mai jagorantan wannan babban bincike na kimiyya, Dr. Anthony  Atala ya bayyana cewa samar da irin wannan kimiyya ya zama dole saboda karancin sassa dan Adam da ake fama dashi a duniya.

   

  A jawibinsa wanda yayi a TEDTalk, Dr. Anthony Atala ya ce, kashi 90 cikin 100 na marasa lafiya da ke bukatar sauyin wani sassa na jiki, suna bukatar koda ne, kuma samun koda wani abu ne mai wahala matuka. Don haka fito da wata hanya da za ta taimaka wa marasa lafiya irin wannan abu ne da ya zama dole.

   

  A halin yanzu, Dr. Anthony da sauran masu binciken wannan cibiya na ci gaba da aiki don ganin wannan kimiyya ya kara habaka kuma ya amfani marasa lafiya masu bukatarsa.

   

  Bidiyon dake kasa, jawabi ne na Dr. Anthony Atala game da wannan sabuwar hanyar ci gaba a bangaren kiwon lafiya.

   

  Video Credit: TEDTalk

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Physics: Darasi game da energy da kuma work 

  Posted Wed at 6:13 PM

  A wannan makala zamu yi bayani ne akan ENERGY da kuma WORK. Game da wannan darasi abubuwan da ake so dalibai su lura da su sune, energy, work, types of energy, sources of energy, classification of sources of energy, law of conservation of energy da mathematical problems...

 • Tekun Labarai: Idan Farauta ta Ki Ka

  Posted Wed at 3:26 PM

  Ku latsa nan don karanta farkon labarin. Ka sani ya kai Sarkin zamani, an yi wani bafatake mai nasibi a harkar saye da sayarwa, duk abin da ya kama sai ya yi daraja. Akwai lokacin da dirhami ɗaya ke jawo masa ribar dirhami hamsin. A kwana a tashi sai kasuwancin ya juya...

 • Yadda ake gashin hakarkari/awazun rago

  Posted Mon at 2:59 PM

  Ga yadda ake gashin hakarkari rago nan yau mun kawo muku. Wannan recipe daya ne daga cikin recipes da muka koyar a shirin girke-girkenmu na Free Rramadhan Classes with Umyuman. Ga yadda abu ya kasance daya bayan daya. Abubuwan hadawa Awazunki (hakarqari) na rago mai...

 • Duhun Damina: Babi na Shida

  Posted Mon at 2:45 PM

  Ku latsa nan don karanta babi na biyar. Jumma'a, 12:50Pm A tsakiyar gadonta take zaune rungume da ƙafafunta a ƙirjinta. Fuskarta na kallon harabar ɗakin, idanunta ya canja launi daga asalin kalarsu, numfashinta na fita a hankali. Numfashi ta ja ta sauk'e, a lokacin d...

 • Bita ta musamman akan rubutun gajerun labarai: Rana ta farko

  Posted Jul 5

  Bakandandamiya tare da hadin kan group din MARUBUTA ta shirya bita ta musamman akan rubutun gajerun labarai, wanda marubucin littafin TEKUN LABARAI, Danladi Z. Haruna, ya gabatar daga ranar 15 – 20 ga watan Yuni, 2020. Ku latsa nan don karanta cikakken bayan...

View All