Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Hanyoyi uku da za a magance illar ?iba ga yara 'yan shekaru 13-18

Hanyoyi uku da za a magance illar ?iba ga yara 'yan shekaru 13-18

 • Kamar yadda ?ungiyar kula da lafiya ta duniya (2012) ta nuna cewa, shekaru talatin (30) da suka gabata an samu ?aruwar mutane miliyan ?ari da saba'in (170 million) da suka abka cikin matsalar ?iba wanda kuwa mafiya yawa yara ne 'yan shekaru ?asa da sha takwas ne (18). Wannan matsalar kuwa ta fi faruwa ne a ?asashe da suka ci gaba, da masu tasowa har ma da wa?anda ba su ci gaba ba. An yi kiyasi, kashi 17% ko milyan goma sha biyu da ?igo 7 (12.7M) na yara da wa?anda suka balaga duk suna da wannan matsalar ta ?iba a ?asashen Amurka.

  Manazarta guda bakwai sun yi binciken sama da makalun ilimi guda 75 wadanda suka yi bincike akan illar ?iba a Najeriya, kuma binciken nasu ya gano cewa akasarin mutanen da suke da nauyi sun kama ne daga 20.3%–35.1%, sannan wadanda ?iba ya musu yawa kuma sun kama ne daga 8.1%–22.2%. Kuna iya latsa nan don karanta cikakken binciken.

  Daga cikin wasu abubuwan da suke haifar da illar ?iba, akwai matsalar cin abinci, wasu kuma nasaba daga iyaye, sannan akwai rashin samun isasshen hatisayi (exercise) ga yaran wanda shi ma ya taimaka gaya wajen haifar masu da ?iba. Yara da suke da wannan matsala ta ?iba suna cikin ha?ari na kamuwa da cutar hawan jini, matsalar ?aukewa ko toshewar numfashi, ciwon suga, ciwon ga?o?i da sauransu.

  Matu?ar ana son al'umma ta rayu cikin lafiya a kuma samu kariya daga irin wannan nau'i na cuta da ke addabar yara 'yan kasa da shekaru 18, akwai bu?atar samun gudummawa daga gwamnati,  da al'umma, da kuma iyaye.

  Mai karatu na iya duba makamancin wannan Makala da ya yi bayani akan amfanin man zaitun guda 5 ga lafiyar jikin ?an Adam

  Ga hanyoyi uku da za a bi wajen magance wannan matsala ta ?iba a cikin yara

  Da farko ana bu?atar gudummawar iyaye wajen rage wannan matsalar ga yaransu. Iyaye za su taimaka ne wajen kula da irin nau'in abinci da kayan sha da aka sarrafa masu ala?a da calorie da yaran ke ci masu kawo musu wannan illar.

  Da haka ne cibiyar kula da kuma kare ya?uwar cutuka suka zayyano wasu hanyoyi da za a bi don rage wa?annan matsalolin ?iba musamman ga yara yan ?asa da shekara 18 domin daidaita nauyin yara don gudun afkawa cikin wannan matsalar ta ?iba.

  1. Taimaka wa yaro yadda zai kula da abinci masu inganci

   Muhimmin abu wajen abinci shi ne samun sinadarin gina jiki (nutrient). Iyaye za su taimaka wa yara ne da irin wa?annan abinci da za su inganta lafiyar yara ta wa?annan hanyoyi:

  1. ?arfafa wa yara (iyalai) gwuiwa da su yawaita shan ruwa lokaci-lokaci.
  2. Da yawaita cin abin da ba zai sanya kitse a jiki ba, (mono-saturated fat)
  3. Rage shan kayan da suke ?auke da za?i
  4. Yawaita cin kayan marmari ('ya'yan itatuwa)
  5. A ci abinci matsakaici ba mai yawa ba
  6. A ri?a cin wake da kaji, da kifi da nama maras kitse wa?anda za su taimaka wa lafiyar jiki
  7. Da kuma tsayuwa kan wa?annan ?a’idoji a ko da yaushe za su taimaka wa yara su kasance cikin ?oshin lafiya

  2. Yara su kasance cikin kuzari kullum

  Hanya ta biyu ta rage matsalar ?iba ga yara ita ce, yara su kasance cikin kuzari kullum. Hakan na samuwa ne in iyaye suka ?arfafa wa yara gwuiwa da wasu wasannin motsa jiki, domin yana taimaka wa yara wajen ?ara wa ?ashinsu ?wari, sannan ya rage masu nauyi, ya kuma ?ebe musu tunani da damuwa da sauransu. Ana son yara su kasance cikin wasanni na motsa jiki a ?alla na tsawon awa guda kowace rana.

  Yayin da ka tsunduma cikin wa?annan wasannin sai ka janyo su ciki kuna yi tare misalan irin wa?annan wasannin motsa jiki sun ha?a da:

  • Iyo cikin ruwa
  • Wasan ?wallon ?afa
  • Raye-raye
  • Wasa da igiya ana tsallake ta
  • Da sauransu

  Kamar yadda cibiyar kula da kare kamuwa da cututtuka ta bayyana, cewa za ka iya taimaka wa yaranka wajen hana su zama haka kawai ba tare da suna aikata wani abu ba. Sannan su rage lokacin da suke ?atawa wajen wasannin (games) da bincike-bincike a yanar gizo, da kuma yawan kallon talabijin.

  Kuna iya duba wannan makala da ta yi bincike akan dalilan dake yawan cusa damuwa ga matasa a yau.

  3. Gudummawar al'umma

  ?iba da ta kasance cuta ba ta lafiya ba, tana bu?atar gudummawar kowa a cikin iyalanka da ma al'umma baki ?aya. Don haka, hanya ta uku ita ce ta gudummawar da al’umma za ta bayar. Al'umma za ta taimaka wajen ya?ar wannan matsala ta ?iba ta hanyar kulawa da ingancin ilmin da karatun yara.

  Hanya ko dabara ta farko ita ce, ?ir?irar hanyar samar da abinci da ga nau'in ganyayyaki wa yara a makarantu wanda zai zama ha?in gwuiwar makarantun gwamnati da da wa?anda ba na gwamnati ba, wanda masu fa?a a ji a gari zasu ?auki nauyin hakan. Manufar ?ir?iran wannan dabara ita ce don ta haska tare da inganta lafiyar yara, sannan yara su sami kuzari wajen gudanar da karatunsu a makarantu don ilmi ya ?ore.

  Kamar yadda cibiyar kula da cututtuka ta bayyana, al'umma za su iya taimakawa wajen inganta lafiya ta hanyar ?ara wa manoma ?aimi da wasu dabaru da za su inganta kayakin da suke nomawa don samar wa yara abin da zai kara musu lafiya. Sannan su ma kasuwancinsu ta inganta lokacin da suka yawaita samar da irin wa?annan kayakin a wadanan wurare da ake bu?ata.

  Sannan za su fa?akar da masu sai da abinci da su ri?a sanya ababe da suke ?auke da sinadaran gina jiki na daga nau'o'in abinci daban-daban a wurin da ake kira ‘food menu’.

  Haka kuma al'umma za ta taimaka wajen ganin an inganta sinadaran cikin abinci, wato nutrition a makarantu, da asibitoci da wasu wuraren cin abinci na musamman. To idan al'umma ta taimaka wajen samun irin wa?annan ababen inganta lafiya cikin abincin yara a makarantu zai taimaka wa yara da kare su daga wannan matsala.

  Har ila yau, kuna iya karanta wata makalar da ta yi fashin baki akan yadda za a rage suga a cikin jinni ba tare da shan magani ba, wanda shima zai iya kasancewa daga cikin hanyoyin da za a bi don kara lafiyar yara da al’umma baki ?aya.

  Daga ?arshe, iyaye da al'umma baki ?aya za su taimaka wajen ragewa da kawar da wannan matsala ta ?iba da take afkuwa ga yara kasa da shekaru 18 in sun bi wa?anan hanyoyi da aka lissafa a sama. Amma in ba haka ba to ba za a rabu da samuwar yawaitar yara da za su fa?a cikin wannan matsalar ba daga yaran har manya ma balagaggu.

  Idan kuna da wasu ?arin dabaru da ku ke gani za su yi amfani wajen kawar da wannan cuta ta ?iba ga matasa a yau za ku iya yin tsokaci a wurin comment.

Comments

0 comments