Makalu

Hanyoyi uku da za a magance illar ƙiba ga yara 'yan shekaru 13-18

 • Kamar yadda ƙungiyar kula da lafiya ta duniya (2012) ta nuna cewa, shekaru talatin (30) da suka gabata an samu ƙaruwar mutane miliyan ɗari da saba'in (170 million) da suka abka cikin matsalar ƙiba wanda kuwa mafiya yawa yara ne 'yan shekaru ƙasa da sha takwas ne (18). Wannan matsalar kuwa ta fi faruwa ne a ƙasashe da suka ci gaba, da masu tasowa har ma da waɗanda ba su ci gaba ba. An yi kiyasi, kashi 17% ko milyan goma sha biyu da ɗigo 7 (12.7M) na yara da waɗanda suka balaga duk suna da wannan matsalar ta ƙiba a ƙasashen Amurka.

  Manazarta guda bakwai sun yi binciken sama da makalun ilimi guda 75 wadanda suka yi bincike akan illar ƙiba a Najeriya, kuma binciken nasu ya gano cewa akasarin mutanen da suke da nauyi sun kama ne daga 20.3%–35.1%, sannan wadanda ƙiba ya musu yawa kuma sun kama ne daga 8.1%–22.2%. Kuna iya latsa nan don karanta cikakken binciken.

  Daga cikin wasu abubuwan da suke haifar da illar ƙiba, akwai matsalar cin abinci, wasu kuma nasaba daga iyaye, sannan akwai rashin samun isasshen hatisayi (exercise) ga yaran wanda shi ma ya taimaka gaya wajen haifar masu da ƙiba. Yara da suke da wannan matsala ta ƙiba suna cikin haɗari na kamuwa da cutar hawan jini, matsalar ɗaukewa ko toshewar numfashi, ciwon suga, ciwon gaɓoɓi da sauransu.

  Matuƙar ana son al'umma ta rayu cikin lafiya a kuma samu kariya daga irin wannan nau'i na cuta da ke addabar yara 'yan kasa da shekaru 18, akwai buƙatar samun gudummawa daga gwamnati,  da al'umma, da kuma iyaye.

  Mai karatu na iya duba makamancin wannan Makala da ya yi bayani akan amfanin man zaitun guda 5 ga lafiyar jikin ɗan Adam

  Ga hanyoyi uku da za a bi wajen magance wannan matsala ta ƙiba a cikin yara

  Da farko ana buƙatar gudummawar iyaye wajen rage wannan matsalar ga yaransu. Iyaye za su taimaka ne wajen kula da irin nau'in abinci da kayan sha da aka sarrafa masu alaƙa da calorie da yaran ke ci masu kawo musu wannan illar.

  Da haka ne cibiyar kula da kuma kare yaɗuwar cutuka suka zayyano wasu hanyoyi da za a bi don rage waɗannan matsalolin ƙiba musamman ga yara yan ƙasa da shekara 18 domin daidaita nauyin yara don gudun afkawa cikin wannan matsalar ta ƙiba.

  1. Taimaka wa yaro yadda zai kula da abinci masu inganci

   Muhimmin abu wajen abinci shi ne samun sinadarin gina jiki (nutrient). Iyaye za su taimaka wa yara ne da irin waɗannan abinci da za su inganta lafiyar yara ta waɗannan hanyoyi:

  1. Ƙarfafa wa yara (iyalai) gwuiwa da su yawaita shan ruwa lokaci-lokaci.
  2. Da yawaita cin abin da ba zai sanya kitse a jiki ba, (mono-saturated fat)
  3. Rage shan kayan da suke ɗauke da zaƙi
  4. Yawaita cin kayan marmari ('ya'yan itatuwa)
  5. A ci abinci matsakaici ba mai yawa ba
  6. A riƙa cin wake da kaji, da kifi da nama maras kitse waɗanda za su taimaka wa lafiyar jiki
  7. Da kuma tsayuwa kan waɗannan ƙa’idoji a ko da yaushe za su taimaka wa yara su kasance cikin ƙoshin lafiya

  2. Yara su kasance cikin kuzari kullum

  Hanya ta biyu ta rage matsalar ƙiba ga yara ita ce, yara su kasance cikin kuzari kullum. Hakan na samuwa ne in iyaye suka ƙarfafa wa yara gwuiwa da wasu wasannin motsa jiki, domin yana taimaka wa yara wajen ƙara wa ƙashinsu ƙwari, sannan ya rage masu nauyi, ya kuma ɗebe musu tunani da damuwa da sauransu. Ana son yara su kasance cikin wasanni na motsa jiki a ƙalla na tsawon awa guda kowace rana.

  Yayin da ka tsunduma cikin waɗannan wasannin sai ka janyo su ciki kuna yi tare misalan irin waɗannan wasannin motsa jiki sun haɗa da:

  • Iyo cikin ruwa
  • Wasan ƙwallon ƙafa
  • Raye-raye
  • Wasa da igiya ana tsallake ta
  • Da sauransu

  Kamar yadda cibiyar kula da kare kamuwa da cututtuka ta bayyana, cewa za ka iya taimaka wa yaranka wajen hana su zama haka kawai ba tare da suna aikata wani abu ba. Sannan su rage lokacin da suke ɓatawa wajen wasannin (games) da bincike-bincike a yanar gizo, da kuma yawan kallon talabijin.

  Kuna iya duba wannan makala da ta yi bincike akan dalilan dake yawan cusa damuwa ga matasa a yau.

  3. Gudummawar al'umma

  Ƙiba da ta kasance cuta ba ta lafiya ba, tana buƙatar gudummawar kowa a cikin iyalanka da ma al'umma baki ɗaya. Don haka, hanya ta uku ita ce ta gudummawar da al’umma za ta bayar. Al'umma za ta taimaka wajen yaƙar wannan matsala ta ƙiba ta hanyar kulawa da ingancin ilmin da karatun yara.

  Hanya ko dabara ta farko ita ce, ƙirƙirar hanyar samar da abinci da ga nau'in ganyayyaki wa yara a makarantu wanda zai zama haɗin gwuiwar makarantun gwamnati da da waɗanda ba na gwamnati ba, wanda masu faɗa a ji a gari zasu ɗauki nauyin hakan. Manufar ƙirƙiran wannan dabara ita ce don ta haska tare da inganta lafiyar yara, sannan yara su sami kuzari wajen gudanar da karatunsu a makarantu don ilmi ya ɗore.

  Kamar yadda cibiyar kula da cututtuka ta bayyana, al'umma za su iya taimakawa wajen inganta lafiya ta hanyar ƙara wa manoma ƙaimi da wasu dabaru da za su inganta kayakin da suke nomawa don samar wa yara abin da zai kara musu lafiya. Sannan su ma kasuwancinsu ta inganta lokacin da suka yawaita samar da irin waɗannan kayakin a wadanan wurare da ake buƙata.

  Sannan za su faɗakar da masu sai da abinci da su riƙa sanya ababe da suke ɗauke da sinadaran gina jiki na daga nau'o'in abinci daban-daban a wurin da ake kira ‘food menu’.

  Haka kuma al'umma za ta taimaka wajen ganin an inganta sinadaran cikin abinci, wato nutrition a makarantu, da asibitoci da wasu wuraren cin abinci na musamman. To idan al'umma ta taimaka wajen samun irin waɗannan ababen inganta lafiya cikin abincin yara a makarantu zai taimaka wa yara da kare su daga wannan matsala.

  Har ila yau, kuna iya karanta wata makalar da ta yi fashin baki akan yadda za a rage suga a cikin jinni ba tare da shan magani ba, wanda shima zai iya kasancewa daga cikin hanyoyin da za a bi don kara lafiyar yara da al’umma baki ɗaya.

  Daga ƙarshe, iyaye da al'umma baki ɗaya za su taimaka wajen ragewa da kawar da wannan matsala ta ƙiba da take afkuwa ga yara kasa da shekaru 18 in sun bi waɗanan hanyoyi da aka lissafa a sama. Amma in ba haka ba to ba za a rabu da samuwar yawaitar yara da za su faɗa cikin wannan matsalar ba daga yaran har manya ma balagaggu.

  Idan kuna da wasu ƙarin dabaru da ku ke gani za su yi amfani wajen kawar da wannan cuta ta ƙiba ga matasa a yau za ku iya yin tsokaci a wurin comment.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Nakasar Zuci

  Posted Dec 7

  "Ki tafi gidanku na sake ki!" Runtse idanu na yi jin sautin muryar Adamu a kaina, yana furta kalaman da suka kusan sanya ni haihuwar cikin da ke jikina. Da sauri na dago jajayen idanuwana da suka gajiya da kuka na sauke a saitin sa. Wani irin tashin hankali da ciwon r...

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All