Rubutu

Blogs » Kiwon Lafiya » Ciwon kan migraine: Dalilai da alamun kamuwa da shi da kuma hanyoyin magance shi

Ciwon kan migraine: Dalilai da alamun kamuwa da shi da kuma hanyoyin magance shi

 • Ciwon kan da ake kira da migraine, cikin harshen Turanci, wani ciwon kai ne mai tsaninin gaske da ke kawo rashin jin dadi kamar su tashin zuciya da kuma jiri. Wannan kalma ta migraine ta samo asali ne daga harshen Faransanci wato daga kalmar ‘megrim’ wadda ma’anarta ke nufi matsaloli irinsu jiri da tashin zuciya, da kuma ciwon kai. A dalilin wannan ma’anar a yau aka samo wannan kalmar ta migraine wadda kuma ake kiran duk wadda ke dauke da ita ‘migraineur’.

  Masana sun yi imanin cewa wannan cuta na migraine na faruwa ne a sakamokon wani abu da ke aukuwa da mutum a waje, wato outside trigger ke nan a Turance. Ma’ana, wato faruwan wani lamari ne ke jawo shi. Idan abin ya faru sai abinnan da ke sa mutum ya ji zafi a cikin kwakwalwa ya faru. Wannan zafi na kwakwalwa sai ya haifar da tsukewar hanyar jinni. Idan hanyar jinin ya tsuke sai mutum ya fada cikin wannan ciwon kai mai tsanani na migraine.

  Wannan ciwon kan na migraine kan auku cikin karamin lokaci sannan kuma ya gushe. Sannan wani lokaci kuma yana daukan lokaci sosai. Idan ya dade abin bai da dadi ko kadan. Duk mai fama da migraine zai shaida hakan.

  Duk da tsanani da rashin dadi da kuma yawaitar wannan ciwon kai a tsakanin mutane amma masana kiwon lafiya basu da ilimi mai yawa game da shi. Sai baya-bayannan ne masu bincike a fannin lafiya suka fara gano asalin dalilan kamuwa da shi, da alamominsa da kuma hanyoyi da za a bi don magance shi.

  Yana kuma da muhimmanci a sani wannan matsala ya fi yawa ga mata. Amma tsananin shi ya danganta ne daga mutum zuwa mutum.

  Ana iya karanta: Magani da wasu alfanun ganyen Bi-ni-da-zuga (Jatropha Curcas)

  Abubuwan da ke kawo migraine

  A wani bincike da masana suke kan yi game da ciwon kan migraine, sun gano cewa wannan ciwon kan na faruwa ne a lokacin da hanyar jini a kwakwalwa ya budu. Duk da cewa masana kimiyyar basu tabbatar da lallai cewa wannan shine makasudin abinda ke haifar da wannan ciwon ba, amma lallai akwai shaida mai karfi na cewa dalililai irin su gado (hereditary) da muhalli (environment) suna daga cikin abubuwan da ke haddasa ciwon kai na migraine. Ana sa ran cewa yayin da ci gaban kimiyya ke bunkasa, haka nan ma dalilan kamuwa da ciwon za su rika bayyanuwa, kuma su ma magungunan su za su karu da kuma  ingancinsu zai karu ainun.  

  Kamar yadda muka fada a sama cewar wannan ciwon kan ana gadon shi sosai. Idan daya daga cikin iyaye suna fama da wannan ciwo to akwai hasashen cewa kashi 50% cikin 100a% da shima zai yi fama da migraine din a rayuwarsa. A sani cewa dalilai da ke jawo ciwon kan migraine shima ya danganta ne daga mutum zuwa mutum.

  Ga kadan daga cikin abubuwan da ke kawo ciwon kan

  1. Abinci: Ya tabbata cewa abincin da mutum ke ci kan haddasa ciwon kai. Abinci irin su giya, da chocolate, da kayan madara wato dairy products a Turance, da wake, da irin su naman gwangwani mai dauke da sinadarin nitrates. Wasu karin abincin sun hada da su soy sauce, da kuma sinadarin caffeine, da aspartame da duk wani abincin da ake jika shi (fermented) ko busar da shi, dukkanninsu suna iya haifar da ciwon kan migraine.
  2. Dalilai na wajen zama ko muhalli (environmental factor): Wajen zama ma na iya taimakawa wajen haifar da ciwon kan. Kamar wuta mai haske ko kuma mai walkiya, da hasken rana, da kamshi ko wari mai karfi, da hayaki, da kuma  fenti da makamantansu da ke faruwa a wajejen da mutum ke zama.
  3. Hormone (wasu sinadarai ne da jikin dan adam ke samarwa): Pre-menstrual syndrome wato yanayin nan na rashin jin dadi da mata ke fama da shi lokacin al’ada na haddasa ciwon migraine. Maganin kwaya da ke hana daukan ciki shima na haddasa wannan ciwon kan. Hormone replacement therapy - wani jinya ne da matan da suka manyanta kanyi don dawo da kuzarinsu na kuruciya - shima yana kawo wannan ciwon kan.
  4. Yanayi na rashin natsuwa (stress levels): Rashin samun natsuwa wala Allah a gida ne ko kuma a wajen aiki ne yana daga cikin dalilan da ke kawo ciwon kan migraine.
  5. Dalilai na canjin yanayin mutum (physical factor): Abubuwa kamar canji yadda mutum ke samun bacci ko sauyi wajen motsa jiki ko kuma ciwon baya ko na wuya su ma kan haddasa wannan ciwon kan.
  6. Sauyin yanayi (weather changes): Canji weather shima wani abu ne da ke kawo ciwon kai sosai musamman lokacin zafi da kuma lokacin hunturu.

  Alamun ciwon kan migraine

  Abu mafi muhimmanci da ya kamata a sani game da migraine shine kowa da yadda yake jinsa ma’ana irin ciwon da zafin da ake ji sun danganta daga mutum zuwa mutum. Kamar yadda muka fada a baya dalilan da ke kawo shi sun banbanta haka zalika alamunsa.

  Akwai alamu da dama da ake danganta su da wannan ciwon kan na migraine shi yasa wani lokacin ba a iya ga no lallai ciwon kan da ke damun mutum migraine ne. Amma dai yawancin abinda aka sani shi ne idan ciwon kan migraine zai fara yakan fara da abinnan da ake kira migraine aura.  Aura wani haske ne mai kamar walkiya ko kuma ganin gizo-gizo ko wani yana-yana hakan nan kafin wannan ciwon kan ya fara damun mutum. Sannan bayan sakawa mutum ciwon kai, migraine na iya saka tashin zuciya harma ya kai ga haraswa kamar yadda muka fada a baya. Dadin dadawa bacin ciki na iya nuni ga alamun migraine, shi yasa ma yawancin lokaci ya kan sa mara lafiya amai.

  Sannan akwai lokutan da alamun migraine basa bayyana a fili a gane su. Abin lura anan shi ne kada ko da wasa a dauki migraine da wasa domin wani lokacin yakan kai ga shanyewar gabobi wato stroke.  Amma dai ita wannan cuta yawa-yawan lokaci ba ta kaiwa ga matsala mummuna ga mutum. Wani sa’in migraine nuni ya ke ga wata matsala ta rashin lafiya na daban. Ko ma dai mene ne duk lokacin da mutum rashin lafiya ya dame shi ya garzaya zuwa ganin likita.

  Mai karat una iya duba wannan makal: Abubuwan da ya kamata a sani game da ciwon hawan jini

  Maganin ciwon kan migraine

  Hanyar da ake bi don magance ciwon kan migraine sun hada da cin abinci masu dauke da B12 vitamins. Abinci masu B12 vitamins na rage yawan wannan ciwon kan nesa ba kusa ba. Wasu hanyoyin da ake bi don magance wannan matsala a gida sun hada da kula da cin abinci masu kyau kuma ba masu haddasa ciwon kan ba. A rage cin abinci irin su chocolate, da red wine, da caffeine da kuma tsohon cheese saboda ire-iren wadannan abincin suna daga cikin abinda ke iya haddasa ciwon kan.

  Sannan kuma saka kankara a dai-dai wajen da kan ke ciwo na taimakawa sosai wajen rage radadin wannan ciwon kan. Haka zalika tausan (massage) wajen shima yana taimakawa sosai. Tausan wajen a hankali yana taimakawa hanyar jini da ke wajen sakewa jinin ya rinka gudana ba tare da tangarda ba, da kuma samarwa ainihin muscles din wurin natsuwa  sosai. Tausan kuma yana taimakawa wajen rage damuwa da kuma tashin zuciya da yawancin lokaci ke tattare da wannan ciwon kan. Wani lokacin kuma zama a natsu a wuri mai duhu mara hayaniya na taimakawa sosai wajen yayewa mutum ciwon kan migraine.

  Kamar kullum, muna kara jan hankali makarantanmu da a duk lokacin da mutum ya fiskanci wani rashin lafiya to ya yi kokarin gani likita domin a tabbatar da ainihin matsalar da ke damunsa. Wannan makala mun rubuta ne don ilmantarwa ga al’umma, amma sanin rashin lafiya da ke damun mutuum, sai kwararru sun yi kwaji! Allah Ya kara mana lafiya, amin.

Comments

0 comments