Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Labaran Duniya » Michael Wamaya ya zama cikin shahararrun malamai 10 a duniya

Michael Wamaya ya zama cikin shahararrun malamai 10 a duniya

 • Wani dan asalin kasar Kenya mai suna Michael Wamaya ya yi rawar gani a yayin da ya kasance cikin 10 na karshe wadanda a ka zaba don samun gasar karramawa na gwarzon malami na duniya, wato Global Teacher Award wanda a ka saba yi a kasar Dubai.

   

  Mr. Wamaya dai malami ne da ke karantar da darasin rawa a wani makaranta da ke kula da karatun yara wadanda ke cikin kuncin rayuwa wanda wata kungiyar tallafawa da ke Birtaniya mai suna Annos Africa ta wanzar.

   

  <script async src="//pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js"></script> <ins class="adsbygoogle" style="display:block; text-align:center;" data-ad-layout="in-article" data-ad-format="fluid" data-ad-client="ca-pub-5319298784785526" data-ad-slot="8125037927"></ins> <script> (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); </script>

   

  Shidai wannan karramawa na Global Teacher Award wanda a ke yinsa kowane shekara na baiwa wanda duk ya ci gasar Dolar Amurka har miliyan daya ($1, 000, 000). Kuma an kirkiro yin hakan ne don karrama malamai a ko ina suke a fadin duniya. A kan fara ne da tantancewa kasa-kasa har ya kai ga mutane goma kacal wadanda da ga cikinsu ne za a zabi guda wanda zai ci gasar.

   

  A ranar 19 ga watan Maris za kaddamar da wanda ya/ta ci gasar a Dubai wanda Sarkin Dubai Mai Martaba Sheikh Mohammad zai gabatar.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Uwargida ba za ki yi dana sanin koyan yadda ake yoghurt in fruits ba. Domin kuwa kayan dadi ne sosai da sosai kuma cikin mituna kalilan za ki hada. Ba a ba yaro mai kiwiya!!! Wannan recipe yana daya daga cikin recipes da muka koyar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman a nan Bakandamiya. Abu...
 • Hadin special salad nawa na musamman ne! Ga sauki ga dadi, uwargida sai kin gwada za ki bani labari! Wannan ma yana daya daga cikin recipes da muka koyar a Ramadan a shirin girke-girkenmu wadda aka gabatar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin ko kin tuna gashin tsokar kaza da muka koya...
 • Red velvet cake, cake ne da mutane da dama suke so kuma kuma suke son ci. Saboda haka, akwai hanyoyi daban-daban na yin red velvet cake, ga yadda na ke nawa cake din na kawo muku. Wannan yana daya daga cikin recipes da muka koyar lokacin Ramadan anan Bakandimya. Domin ganin duk jerin recipes din da...
 • Bismillahi rahmanir Rahim Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lalle haduwar Idi da Jumma’a wani abu ne da ya saba faruwa lokaci zuwa lokaci. Hakan ya taba faruwa a zamanin Manzon Allah (S.A.W...
 • Lemun zaki ko orange juice lemu ne mai dadi da kuma tarin amfani a jiki. Ga yadda na ke lemun zaki na a gida. Da farko wannan recipe mun koyar da shi ne a shirinmu na Ramadan cikin zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin yaya ki ke yin lemon zakinki? Ga yadda na ke nawa, ki gwada wannan!&nbs...
 • Bismillahi rahmanir Rahim Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai girma da daukaka. Salati da sallama su kara tabbata ga Manzon Allah, da iyalansa da Sahabansa. Mece ce layya? Layya ita ce: Abinda ake yankawa na dabbobin ni'ima (rakumi da shanu da rago da akuya) ranar idin babbar sallah, d...
View All