Makalu

Wa ya gaya mi ki cewa yana son ki har cikin zuciyarsa? Ki lura da wadannan alamomi

 • Abu ne mai matu?ar ciwo mace ta fahimci cewa namijin da take so, baya sonta. Baya son kasancewa da ita a rayuwarsa. 

  Abun takaici irin wadannan mazajen basa iya fadar cewa ba sa son mace a baki, bare har ta san inda dare ya yi ma ta. Sai ya zamo ke a zuciyar ki kin san cewa akwai wani abu, amma kin kasa fahimtar ina ya dosa. 

  Akwai lokuttan da za ki ji a zuciyar ki ina ma ya fito fili ya fada mi ki cewa baya sonki, ba shi bukatar rayuwa da ke, akan yanda yake nuna mi ki komi daidai ne. 

  Abu ne mai wahala irin wannan namijin ya fito fili ya fada mi ki, wani saboda baya son ya karya mi ki zuciya ko kuma dai yana ganin mutuncinki. 

  Duk da haka wani ba wai sonki ne baya yi ba, kawai dai yana bukatar ki ba shi wuri watakila yana cikin wata damuwa, ba lallai sai ya daina son ki ba.

  Kina iya duba wannan makala da ta yi nazari akan halayya da kuma dalilan da ke sa a so miskilin namiji. 

  Wadannan abubuwan da zan zayyana muku a gaba na daya daga cikin alamomin da ke nuna cewa ba ya sonki, ko kuma ya canza ra'ayi akan ki. 

  - Abu kadan ke bata ma shi rai da ke 

  A da akwai abubuwan da idan kika yi su ya kan ji dadi har ya yaba ma ki, saboda suna faranta ma sa rai. Daga baya sai ya zamo abu kadan za ki yi ya fara fada a kan shi, ya ji haushi. 

  Ko kuma idan kuna fira tambayar da za ki mi shi wadda zai iya dadewa yana ba ki amsa, sai ya zamo yanzu ya ba ki gajeruwar amsa ko kuwa ya amsata cikin jin haushi. 

  A irin wannan yanayi, ya kamata ki lura da cewa shin hakan da yake yi yana yi ne saboda ya daina sonki da ya yi, ko kuwa a dalilin wata matsala ce ta rayuwa da ya shiga wadda ta jawo hakan. Dole a nan ki yi taka tsan-tsan wajen ajiye kowane yanayi a muhallinsa. 

  Matukar ki ka tabbatar da cewa canzawar shi ba shi da hadi da yanayin rayuwarsa da ya shiga, to hakan zai tabbatar mi ki da cewa babu sonki a zuciyar sa. 

  - Yana janyewa a hankali

  A lokuttan baya da ku ke ganiyar soyayya, a kowace rana bai rasa tsayawa ba ki labarin yanda ranar shi ta kasance, abubuwan da su ka faru a ranar. Ko ma wani labari na daban da zai kara mu ku armashin hirar ku. 

  Kwatsam! Ya canza, babu wani dogon zance a tsakanin ku, duk yadda kika so ki ja shi da fira yana kaucewa. Hakan nada nasaba da cewa ya daina yayin ki, soyayyarku na gab da mutuwa. Matukar dai ba wani yanayi na rayuwa ya shiga ba wanda ka iya jawo hakan.

  Karanta: Manya-manyan kura-kurai da ma’aurata ke yi basu sani ba

  - Yana daukar lokaci mai tsawo kafin ya tura ma ki sako ko ya kira ki 

  A farkon soyayyar ku ya kan kira ko tura mi ki sakonni da yawa a rana, kema haka, ya zamo dai koda yaushe kuna tare da juna a zahiri ko a badini, a wannan lokacin soyayyar na da zafinta. 

  Sai ya zamo kuma baku yi yarjejeniya da shi na cewa ga iya adadin kiran da zai rika mi ki ba a rana, saboda ta yiwu shi din ba mai son kiran bane. A'a hakanan kawai kika ga dif! Ya dauke kafa, idan kin tura sako har sai ki manta ma kin tura sannan zai maido mi ki da amsa. Idan kira ne ma sai ya ga dama ya amsa ma ki. Idan kika yi korafin hakan ya ji haushi ko ma ya fara mi ki fadan kin takura mi shi. 

  Da kin lura da hakan tabbas kin fara bankwana da masoyinki. 

  - Idan ya daina ba ki lokacin da a da yake ba ki 

  A da duk irin yanayin aikin ko karatunshi ya kan sama mu ku lokacin da za ku gana da juna ku yi hira tare da tattauna matsalolin rayuwa, sai ya zama a yanzu duk lokacin da kika nemi ki yi magana a kan rashin lokacin da yake ba ki, zai fada mi ki cewa aiki ya ma sa yawa, bai da lokacin yanzu. 

  A nan ina so ki tambayi kan ki, a lokuttan baya da yake samun damar ganawa da ke duk da yanayin aikinshi bai taba korafin hakan ba sai yanzu? 

  Idan namiji na sonki, duk irin yanayin rashin isashshen lokaci da yake da shi, sai ya samu lokacin da za ku zanta da shi. 

  Matukar ki ka tabbatar ba aiki ne ya mi shi yawa ba, babu wani kwakkwaran dalilin hakan na nuni da cewa soyayyar ku ta zo karshe. 

  - Ya daina lallashin ki a lokacin da kina cikin damuwa

  A lokacin da soyayyar ke ganiyar ta, baya son ya ga bacin ranki, zai ta tambayar ki damuwar ki, ko da kuwa ba zai iya share mi ki ita ba, zai ba ki dukkan kunnuwan sa wajen sauraren duk abinda kika zo da shi, ba zai yi fushi ba. Zai zamo yana tare da ke a kowane irin lokaci, yana ba ki kwarin gwuiwa. 

  Amma a yanzu sai ya zamo bai ma gane yanayin da kike ciki, koda kin fada ma sa damuwarki bai da ra'ayin taimaka mi ki, hakan ma sai ya zama kamar takura ne a wajen shi, ko kuma ya ga gazawar ki a lamuran rayuwa da har ba za ki iya magance su da kanki ba.

  Duba: Siffofi goma da mata ke so a wurin namiji

  - Ya daina kulawa da ke da duk wasu bukatun soyayyar ku 

  A lokuttan baya mutum ne shi mai taka tsan-tsan da duk wani abu da ya shafi soyayyar ku, yana ba ki kulawar da ta kamata. Ya san abinda soyayyar ku ke bukata da wanda ba ta bukata. 

  A kwana a tashi hakan ya sauya zani, babu wannan kulawar, komi ya canza. Kin yi duk wani kokari da za ki yi amma abin ya ci tura, babu wani ci gaba da aka samu. Hakan na nuna cewa ya janye a soyayyar. Duk yadda kika so a samu maslaha hakan ya kasa samuwa, dole ki yi hakuri ki kama gabanki duk da cewa abu ne mai matu?ar wuya, sai an daure. 

  - Ba ya cikin farin cikin idan yana tare da ke

  A lokuttan da su ka shude, kasancewar shi da ke na daga cikin ababen da ke samar mi shi da farin ciki. Dariyarki, murmushinki da kalamanki na sa ka shi farin ciki, hakanan ma ya ji cewa yana tare da ke kan kawo ma sa farin ciki. 

  Amma yanzu sam babu wannan walwalar a tattare da shi. Babu wani canji, kin kuma tabbatar ba canzawar yanayi ya samu ba, ke din ce dai baya farin ciki da kasantuwar ki a cikin rayuwar sa. Kin yi iya bakin kokarinki wajen ganin kin faranta ma sa amma abin ya ci tura. Duk wasu abubuwa da ki ka san a da yana saka shi farin ciki kin yi amma kuma abin ya ci tura, hakan na nuna cewa ya daina sonki. 

  - Ya daina cewa yana sonki

  Daga lokacin da ki ka fara tambayar kan ki "Shin har yanzu yana so na kuwa?", daga lokacin soyayyar ku ta shiga cikin wani yanayi na daban mara kyau. 

  Idan namiji na sonki zai ba ki duk wata soyayyar da ba za ki taba kokwanto ba, zai cike duk wani gurbi. Zai nuna yanda yake ji game da ke. 

  A wasu lokuttan ba sai ya fada da baki ne zai nuna cewa yana sonki ba, ko ta hanyar sakonni, a'a ke karan kanki za ki yi amanna da cewa yana matu?ar kaunar ki, saboda ya bi duk wasu hanyoyi da zasu nuna hakan, kuma za su hana ki wasiwasi a kan soyayyar ku. 

  Daga zaran ya daina nuna cewa yana sonki, ya daina fadi, ya daina duk wasu abubuwa da za su tabbatar mi ki da kasantuwar ki a zuciyarsa. 

  Tabbas ya daina son na ki ne, saboda a halittar namiji ba shi da boye-boye dangane da abinda yake so. 

  Kadan kenan daga cikin alamomin dake nuna ba sonki yake ba.

  Har yanzu kima iya duba wadannan karin alamomi guda goma dake nuni da cewa soyayya ta kare tsakanin ki da shi.

  Idan har a baya burinki ne ki ga kin kawo gyara a soyayyar ku, na san abu ne mai ciwo ki tabbatar da wadannan alamomi a tattare da mutumin da kike so. Sai ma idan ya kasance ya nuna sama da alamomi biyu da na zayyana. 

  Karbar gaskiya a irin wannan yanayi shi ne mataki na farko da ya kamata ki yi, na cewa wanda kike so kike burin gina rayuwarki da shi baya sonki yanzu. 

  Ba za ki taba gane barin wannan soyayyar ita ce mafi girman kyautar da kika taba yi ma kanki ba sai a gaba. 

  Sannan dan namiji ya nuna baya sonki ba shi ne shaidar cewa ke din ba a bar so ba ce ko kuma ba ki da wannan darajar ta a so ki, kawai yana nufin bai da ra'ayin kasancewa da ke ne. 

  Ina fatan bayan kin karanta wannan makala za ki fahimci ina soyayyarku ta dosa, kafin yanke hukuncin mataki na gaba da za ki bi. 

  Wacce ta rubuta: Ayeesh Chuchu, daga Gusau, Nigeria

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake gashin kifi karfasa

  Posted Jul 12

  Gasashshen kifi karfasa ko grilled fish ko kuma grilled tilapia abinci ne da mutane da yawa suke so kuma suke sha’awar koyon yadda ake sarrafawa. Saboda haka Umyuman ta koyar da yadda ake gashin kifi a cikin recipes da ta koyar a lokacin Ramadan a cikin zaurenta n...

 • Bita ta musamman akan rubutun gajerun labarai: Rana ta biyu

  Posted Jul 12

  Ku latsa nan don karanta darasin ranar farko. DARASI NA 1 Abubuwan lura a rubutun gajeren labari A jiya mun bayyana siffar gajeren labari ta fuskar adadin kalmomi. Mun riga mun san cewar shi Rubutu baiwa ne. Ba kowa ke da baiwar rubutu ba. Duk da haka akwai hanyoyin ...

 • Ko Ruwa Na Gama Ba Ki: Babi na Biyar

  Posted Jul 12

  Ku latsa nan don karanta babi na hudu. Gabaɗaya Asabe da Malam Amadu sun kasa kunne suna jiran Jummai da ke zaune a gabansu, ta faɗa musu wanda ya yi mata ciki, sakamakon tsawon lokacin da ta ɗauka tana ɓoye musu. Kan Jummai na ƙasa ta ce, "Habeeb ne". kusan duk ba s...

 • Physics: Darasi game da energy da kuma work 

  Posted Jul 8

  A wannan makala zamu yi bayani ne akan ENERGY da kuma WORK. Game da wannan darasi abubuwan da ake so dalibai su lura da su sune, energy, work, types of energy, sources of energy, classification of sources of energy, law of conservation of energy da mathematical problems...

 • Tekun Labarai: Idan Farauta ta Ki Ka

  Posted Jul 8

  Ku latsa nan don karanta farkon labarin. Ka sani ya kai Sarkin zamani, an yi wani bafatake mai nasibi a harkar saye da sayarwa, duk abin da ya kama sai ya yi daraja. Akwai lokacin da dirhami ɗaya ke jawo masa ribar dirhami hamsin. A kwana a tashi sai kasuwancin ya juya...

View All