Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Rayuwa da Zamantakewa » Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

 • A wannan Makala za muyi dubi ne zuwa ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani.

  Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a ne na kwarai ba, wasu daga cikin matasan namu sun mai da shi tamkar ado. Yayin da za ka ga matashi ko matashiya tana aikatawa tamkar bata san illar da ke cikin abin ba sabo da shaidan ya yi musu hudubar tsiya basa ganin aibun abin.

  Abin tsoron shi ne, ada wannan wata dabi’a ce da muke jinta a nesa ko kuma a tsakanin ‘yan daba, sai ka ji ana labarin abin ana kyamarshi sannan ana mamaki. To yau da kadan-kadan ga shi ya zo ya cimmana har gida. Yaro ko yarinya a gidan iyayensu suna shan wadannan miyagun kwayoyi. Wa iyazu billah!

  Dadin dadawa wannan dabi’a a da dabi’a ce da ake ganin maza ne kawai suke shigarta, abin takaici shi ne yanzu mata da yawa sun shiga kama daga ‘yan mata matasa har izuwa matan aure. Matan har suna neman su kere maza don ana ganin kashi sittin cikin dari na masu shaye-shaye a yanzu mata ne.

  Duba wannan Makala da ya yi nazari akan binciken masana game da shaye-shayen mata a arewacin Najeriya.

  Mata da ake tsammanin za su taimaka wajen gyara dabi’un yara kuma su ma sun bage da shiga wannan hali ai al’amarin ya baci. Duk sanda ake ce mace to ai ana mata kallon uwa ce, kuma ita ce fiye da kowa take da hakkin gyara al’umma. In har mace ta gyaru to ana sa ran al’umma zata gyaru.

  Illolin shaye-shayenan suna da yawa ainun, kama da ga yadda yake jirkita mu su kwakwalwa har zuwa yadda yake bata musu wasu daga cikin vital organs (kamar su huhu da hanta) na su, da kuma maye da ya ke haifar mu su ta inda za su rika aikata wasu abubuwa na ashsha ba’a cikin hayyacinsu ba.

  Kafin na kawo muku bayani game matsalolin da shaye-shaye ke kawo wa, bari na kawo muku sakamakon bincike da muka yi game da dalilan da mutane, musamman matasa mata, ke shiga shan kwayoyi.

  Dalilan dake jawo shaye-shaye

  Mun yi wani bincike da muke so mu gano dalilan dake sanya matan aure ke shiga shaye-shaye, kuma mun samo bayanai kamar haka:

  Rashin kasancewar mazaje kusa ga matansu

  Wata matan aure ta tabbatar mana da cewa ta shiga shaye-shaye ne sakamakon mijinta baya zama a gari. Tun lokacin da ya aureta yakan tafi wata jahar aiki ya barta a gida bawani abokin fira, sakamakon haka ke sata ta sayo maganin mura ta sha domin ta iya bacci, wannan shine sanadiya

  Matsalolin aure

  Wata kuma ta shaida mana cewa bakin ciki ne ya sanya ta shiga shaye-shaye. Mijinta ke muzguna mata, kuma koda ta kai karar sa a gida ba’a ganin laifinsa saboda tun farko an san bata son shi sai ake ganin tamkar sharri take mishi. Sanadiyar haka kawarta ta bata shawarar ta dinga shan kwayoyi in ta tsinci kanta a wannan matsayin.

  Mummunar kawance

  Yawan kawance da miyagun abokai ko kawaye kan kawo shiga shaye-shaye. Idan kai baka sha ko ba ki sha to baki waye ba ko ba lallai bane a yi kawance dake. Har’ila yau, samari na amfani da kwayoyi ga ‘yan mata don cimma wata manufa tasu sakamakon sun san basa samun dammar amfani da matan in bawai sun fita hayyacinsu ba.

  Shiga bangar siyasa

  Akwai matashin da ya shaida mana cewa ya shiga shaye-shaye ne saboda siyasa. Kasancewar s abaya iya daukar wasu hayaniya da matsaloli har sai ya hada da shan kwayoyi, kana ya tabbatar mana cewa wasu a cikin mutanensa duk hakan take faruwa saboda irin gwagwarmayar da suke shiga. Wa su manyan kuma sukan fara ne da shan magungunan kashe gajiya da ciwon jiki, daga nan kuma sai su saba.

  Sanin kowa ne duk wani maganin da za kasha batare da likita ya rubuta maka ba ko kuma baka sha shi a kan ka’idar likita ba to fa ana kiransa da drug abuse, don haka yana dakyau mu kiyaye sosai ko don zaman lafiyarmu, mutuncinmu, da kuma kare addininmu.

  Kuna iya karanta wannan makala da ta yi bayani akan shawarwari 8 don inganta tarbiyan yara.

  Yanzu kuma ga kadan daga cikin manyan matsalolin da shaye-shaye ke jawowa a yau.

  1. Jirkita kwakwalwar mai sha

  A yayin da mutum ya dauki mummunar dabi’a ta shan miyagun kwayoyi, a wannan lokacin tunaninsa zai banbanta da na masu hankali wanda sanadiyyar haka yana haifar da ciwon hauka sannan kuma ya illata wasu sassa na jiki da kwakwalwa. Ya kan koma baya jin kunyar kowa baya kuma jin tsoron kowa.

  2. Matsalolin rashin lafiya

  Mai shaye-shaye kan gamu da cututtuka daban-daban wadanda sun hada da kwakwalwa, ciwon kirji, ciwon koda, ciwon hanta harma ga mata yakan lalata musu mahaifa.

  Kuna iya karanta wannan makala da ta yi karin bayani game da illolin shaye-shaye ga lafiyar jiki, ko kuwa wannan dake bayani akan rushe tarbiya ta duniyar yanar gizo.

  3. Aikata munanan abubuwa na ashsha

  Tabbas akwai abubuwan da mutum mai hankali ba zai iya aikata su ba sai dole ta hanyar fita hayyacinsa wanda hakan zai sa ya koma amfani da wani tunani na daban kuma ya iya aikata abubuwan ashha ba tare da tausayi ko sanin dai-dai ba. Daga cikin irin abubuwan da mashayi zai aikata sun hada da: aikata kisan kai, fyade, bangar siyasa da sauransu.

  Kuna iya duba wannan makala da ta yi sharhi bisa dalilan dake kawo yawan fyade a yanzu. Shaye-shaye na daga cikin su.

  4. Rasa mutunci da darajar kai

  A yayin da mutum ya dauki shaye-shaye a matsayin abin yi koda yaushe yakan rasa duk wata daraja da kuma mutuncinsa a idon jama’a. Hakan kan jawo ma sa kaskanci da wulakanci a rayuwa.

  5. Shaye-shaye kan nisanta mutum daga ibada

  Sakamakon gushewar tunani da shagalta cikin aikin ashsha sai ka ga lokuta ibada na kubucewa mutum ba tare da mutum ya sani ba. Wannan irin yanayi na kara cusa mutum cikin halin da sai dai a ce Allah Ya gyara.

  Kuma ba zai dace ace mutum ya tsinci kansa a wannan yanayi na shaye-shaye ana kyamatar sa ba ko kuma ana kokarin sa ba wai a nema masa magani ko mafita akan hakan ba. Yana da kyau kuma ya zama dole a gaggauta kai mutum wajen likitoci sannan kuma yakasance an sama abin yi ta yadda ba zai sake fadawa irin wannan hadari ba.

  Muna rokon Allah da ya shiryar mana matasanmu a kan tafarki madaidaiciya. Sannan iyaye da gwammanti ya kamata kowa ya yi iya kokarinsa a matsayinsa wajen rage ko kuma kawar da wannan dabi’a gaba daya a cikin al’umma.

  Wacce ta rubuta: Hadiza Balarabe, daga Kaduna, Nigeria

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Mon at 1:39 PM
  Posted by Bakandamiya
  Uwargida ba za ki yi dana sanin koyan yadda ake yoghurt in fruits ba. Domin kuwa kayan dadi ne sosai da sosai kuma cikin mituna kalilan za ki hada. Ba a ba yaro mai kiwiya!!! Wannan recipe yana daya daga cikin recipes da muka koyar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman a nan Bakandamiya. Abu...
 • Hadin special salad nawa na musamman ne! Ga sauki ga dadi, uwargida sai kin gwada za ki bani labari! Wannan ma yana daya daga cikin recipes da muka koyar a Ramadan a shirin girke-girkenmu wadda aka gabatar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin ko kin tuna gashin tsokar kaza da muka koya...
 • Red velvet cake, cake ne da mutane da dama suke so kuma kuma suke son ci. Saboda haka, akwai hanyoyi daban-daban na yin red velvet cake, ga yadda na ke nawa cake din na kawo muku. Wannan yana daya daga cikin recipes da muka koyar lokacin Ramadan anan Bakandimya. Domin ganin duk jerin recipes din da...
 • Bismillahi rahmanir Rahim Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lalle haduwar Idi da Jumma’a wani abu ne da ya saba faruwa lokaci zuwa lokaci. Hakan ya taba faruwa a zamanin Manzon Allah (S.A.W...
 • Lemun zaki ko orange juice lemu ne mai dadi da kuma tarin amfani a jiki. Ga yadda na ke lemun zaki na a gida. Da farko wannan recipe mun koyar da shi ne a shirinmu na Ramadan cikin zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin yaya ki ke yin lemon zakinki? Ga yadda na ke nawa, ki gwada wannan!&nbs...
 • Bismillahi rahmanir Rahim Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai girma da daukaka. Salati da sallama su kara tabbata ga Manzon Allah, da iyalansa da Sahabansa. Mece ce layya? Layya ita ce: Abinda ake yankawa na dabbobin ni'ima (rakumi da shanu da rago da akuya) ranar idin babbar sallah, d...
View All