Makalu

Dalilan da ka iya sawa a koma vegan diet

 • A ‘yan shekaru kadan da suka wuce, kafar yada labarai ta kasar Amurka mai suna USA Today ta ruwaito cewa kashi 50% na mutanen kasar Amurka suna ta kokarin su ga sun inganta lafiyarsu ta hanyar kokarin ganin sun rage yadda su ke cin nama da yawa a ciki abincinsu. A yayinda za ka tarar a duk inda ka sami dalibai biyar to daya da ga cikinsu ko dai shi vegan ne ko vegetarian ko dai yana ta kokarin rage yawan cin nama cikin abincinshi. Vegans sune wadda basa cin duk wani abinda ya fita daga dabba a matsayin abinci ko kuma yin wani amfani na daban da dabba. Sannan vegetarian kuma sune mutanen da basa cin nama sai kayan gayanyanki da kuma irin su nut da makamantasu. Wannan irin tsarin cin abincin ana kiranshi da plant-based diet ko vegan diet. Amma abin tambayar anan shi ne, wai mai ya sa ‘yan kasar Amurka da ma sauran sassan duniya da suka ci gaba suke ta faman kokarin rage cin nama cikin abincinsu ne? Yaya labarin ya ke a irin kasashenmu na Afirka?

  An jima ana muhawara da kuma sa-in-sa da cewar akwai ko babu illa cin nama ga lafiyar bil adama, yayinda masu ganin akwai illar suka fi alakanta laifin  ga harkokin kamfanonin sarrafa nama. A yanzu tafiyar da ake yi dai da yawa sun yadda lallai cin namar na da illa ga lafiya. Wannan dalili ya kara bawa masu tallata ra’ayin zamantowa vegan karin karfin guiwa da kuma basu karfin kara kaimi wajen campaign na su akan jama’a su bar cin nama. A ganin ‘yan vegan, idan dai har muna son dabbobi, to me zai sa mu ci namansu?

  Duk da mun san cewa a addinance, musamman addinin Musulunci, Allah Ya halattawa mutane cin naman dabbobi idan har sun bi ka’ida da addinin ya shinfida, to amma a wurin ‘yan vegan ba haka zancen ya ke ba. Akwai daliliai na lafiya da dama da idan aka duba to za a ga cewa bari ko rage cin nama na da kyau. Ga dalililan kamar haka:

  Rage hatsarin kamuwa da cututtukan da suka shafi zuciya da kuma ciwon sikari

  Bincike ya tabbatar da cewa abinci da ake samu a jikin dabbobi masu dauke da cholesterol mai yawa da kuma saturated fat suna gaba-gaba wajen haifar da cututtukan da suka shafi zuciya. Mutum na iya kare kansa da ga wannan hatsarin ta hanyar cin abinci irin su legumes, ganyayyaki da kuma su ‘ya’yan itatuwa. Su irin wadannan abincin masu lafiya suna bawa mutum high amount of potassium da kuma low fibre wadda hakan zai taimaka wajen rage hatsarin kamuwa da ciwon zuciya da kuma ciwon shan inna, wato stroke. Ciwon zuciya da stroke na daga cikin cuttuka da ke kashe mutane da yawa a yau.

  Wani likita a kasar Amurka mai suna, Dr Caldwell Esselstyne ya tabbar da cewa ya taimakawa marasa lafiya da dama, da ke jinya a wurinsa, ta hanyar saka su cin abinci vegan diet kawai. Kuma ya tabbatar da cewa wannan tsarin cin abinci ya taimaki mutane marasa lafiya daban-daban, wasu daga cikinsu har an yi nasarar warkar da cuta irinsu type 2 diabetes da ke damun su.

  Kariya daga cutar sankarau wato cancer da ma wasu cututtuka masu tsanani na zamani

  Cin abincin vegan diet na da matukar amfani ga lafiya, domin kuwa cikin ire-iren abincinsu akwai abubuwa masu kara lafiya da kuma kariya da cututtuka masu yawa. Suna da sinadaran da ake kira da suna antioxidants da kuma phytonutrients wadanda ke yaki da samuwar free radicals da ke haddasa lalacewar kwayoyin halitta na cell din dan adam da kuma haifar da inflammation. Cell deterioration da kuma inflammation kan haifar da cutuka irin su cancer da danginsu. Kuma bincike ya tabbatar da cewa idan mutum ya riki vegan diet zai rage hatsarin kamuwa daga hauhawar jini da ma dayawa da ga cututtuka irinsa.

  Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya, wato World Health Organization, ta tabbatar da cewa nama da ake sarrafawa, wato processed meat a Turance, is a proven carcinogen, ma’ana yana ingiza samuwar kansa. Sannan suka ce jar nama ma watakila na iya haifar da kansa din. Sannan kuma akawai da yawan bincike da aka gudanar a kafafen bincike na kasashen Turai da su China wadda ya alakanta ciwon kansa da cin abinci da suka fito a jikin dabbobi. Sannan kuma a ko da yaushe muka ziyarci likitocinmu sukan bamu shawaran rage cin nama, musamman idan shekaru sun ja. Saboda haka cin abinci da ya kunshi zallar tsirrai da ganyayaki ai ba laifi ba ne idan muka dubi ire-iren hatsarukan da ke tattare da cin nama.

  Karanta: Hanyoyi guda biyar na rage kiba ba tare da an shiga hatsari ba

  Abinci n da ke samuwa ta jikin dabobbi (animal products) suna dauke da chemicals masu yawan gaske

  Kungiyar nan da ke ikirarin kare hakkin dabbobi wato, PETA ta tabbatar da cewa animal product kamar su kwai, da nama ko kuma abubuwan da suka shafi madara wato dairy product na dauke da antibiotics, da sinadarai masu guba, da kuma hormones, da kwayoyin cuta na bacteria da dai sauran sinadarai masu guba daban-daban. Wadannan abubuwa kuwa ka iya jawowa dan adam matsalolin lafiya masu tsananin gaske. Kuma sannan, USDA sun tabatar da cewa kashi saba’in na food poisoning na samuwa ne a sanadiyar cin nama dabobi da basu da inganci.

  A sabili da yadda ake bukatar nama da sauran abinci da ke samuwa ta wajen dabbobi ya sa manoman dabbobin suna amfani d hormone da su antibiotics domin saka dabobbin girma da wuri. Wannan hanyar na haifar da antibiotic-resistant bacteria ga su dabbobin da kansu wadda hakan na iya haifar da carcinogenic substance (sinadari mai haddasa kansa) kuma a karshe duk wannan matsalar zai kare ne a jikin dan adam.

  Tsarin cin abinci na vegan yana taimakon muhalli (environmentally-friendly)

  Bincike ya tabbatar da cewa kamfanoni masu samar da nama sun dauki kamar kashi 18 zuwa 51 daga cikin kamfanoni masu gurbata muhalli, wato human-made pollution. Gungiyar Earthsave sun tabbatar da cewa kafin a sarrafa pound daya na namar hamburger sai an amayar da 75kg na iska mai guba na CO2. Saboda haka idan aka duba kenan irin barna da kamfanoni da ke sarrafa nama ke yi wa muhalli ya ma fi kamfanonin sufuri (transportation company) da kuma sauran masana’antun kere-kere.

  Cin abinci na tsarin vegan zalla na karawa mutum walwala

  Bincike ya nuna cewa mutane da ke bin tsarin vegan diet sun fi kasancewa cikin walwala da koshin lafiya, wato a healthier mood state. Wannan na nuni da cewa suna da kariya mai yawa kenan daga bakin ciki da damuwa, da kuma yawan fushi, da kuma fatigue da makamantansu. Abin mamakin shi ne shi cin abinci da ake kira da plant-based food yana karawa mutum walwalar ne sabodo da suna dauke da antioxidants masu yawan gaske.

  Mai karatu na iya duba makamancin wannan makala da ta yi bincike akan amfanin man zaitun ga lafiyar bil adam.

  Yana sa mutum ya kasance cikin kuruciya 

  Abinci na tsarin vegan na karawa mutum yaranta domin suna gyarawa mutum fatansa da kuma gashi saboda yawan minerals da kuma vitamins da antioxidant da ke cike cikin ire-iren abincin. Ka ga kenan a maimakon kashe makudan kudi wajen gyaran jiki da sayan mayukan kanti wadda yawanci ma ba wani inganci ne da su ba, mai zai sa ba za a koma cin shi wannan plant-based food din ba? Sun fi araha, kuma ba su da wani hatsari ko kadan ga lafiya.

  A karshe, zan iya cewa tabbas cin abinci na tsarin vegan yana da matukar amfani da ba su kidayuwa. Abubuwa kamar yadda zai kare muhalli daga fidda iska mai guba da kamfanonin sarrafa nama ke yi har izuwa yadda ya ke kare mutane daga samun cututtuka irin su kansa, sannan kuma zai taimaka wajen karawa mutum kuruciya. Malam bahaushe yace, hanyar lafiya a bita da sannu!

  Kuna iya latsa nan don karanta wannan makalar cikin harshen Turanci.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Hudu

  Posted Fri at 4:38 PM

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. Yana fitowa daga wankan kai tsaye gaban mudubi ya nufa, tun kafin ya kai ga ƙara sawa idanuwansa suka tsinkayo masa  ƙananan kaya ya she akan gado riga da wando,  da dukkan alamu Sakinah ce ta ajiye masa su, sai faman wan...

 • Yadda ake hada spring chin-chin

  Posted Thu at 10:16 AM

  Assalamu Alaikum. Barkan mu da warhaka. Ayau na sake zuwa mana da sabuwar makala ta girke-girke wacce ciki za mu koyi yadda ake soya spring chin-chin. Abubuwan hadawa Flour (4 cups) Baking powder (1 teaspoon) Butter (125grms) Mangyada Gishiri (1 teaspoon) Ya...

 • Yadda ake hada KFC chicken

  Posted Thu at 10:11 AM

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girken Bakandamiya tare da ni mai gabatar muku da shirin. A yau in sha Allah zan nuna mana yadda ake hada KFC chicken. Abubuwan hadawa Kaza Flour Man gyada Bread crumbs ko cornflakes Kwai Maggi ...

 • Yadda ake hada egg masala

  Posted Thu at 9:57 AM

  Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo mana da yadda za a hada egg masala a saukake. Abubuwan hadawa Dankalin turawa Albasa Carrots Maggi Mangyada Kwai Yadda ake hadawa Farko za ki wanke dankal...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

View All