Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Cutar asma: Alamominsa, illolinsa da kuma hanyoyin kariya daga cutar

Cutar asma: Alamominsa, illolinsa da kuma hanyoyin kariya daga cutar

 • Cutar asthma ko asma da Hausa wata cuta ce da ke kumbura hanyar iska da ke huhun dan adam. Hanyar iskar kan kumbura kuma ya tsuke wadda zai kara yawan majina (mucus). Wannan lamari ya kan saka wahala wajen yin numfashi wadda hakan sai ya haifar da tari da numfashi sama-sama (wheezing) da kuma daukewar numfashi.

  A wajen wasu mutane, cutar asma baya takura su sosai amma idan ka duba wasu mutanen da dama cutar wani babban kalubale ne a rayuwarsu da kan iya shigar da su hatsari na mutuwa.

  Abin da yakamata a sani shi ne, cutar asma dai ba ta warkewa. Amma kuma ana iya kiyaye alamomin kamuwa da shi (its symptoms can be controlled). Saboda cutar asma na canzawa, yana da kyau mara lafiya, tare da hadin guiwar likitansa, ya kula da alamominsa don sanin irin canji da za a yi na jinya duk lokaci da bukatar hakan ta taso.

  Alamun cutar asma (symptoms)

  Alamun cutar asma ya danganta ne daga mutum zuwa mutum. Mara lafiya na iya shiga asma attack ko da yaushe ko kuma abun na jimawa kafin ya dame shi. Koma ya ya abun ya ke, ga alamominsa kamar haka:

   1. Daukewar numfashi
   2. Jin takura a girji ko kuma zafi (chest tightness)
   3. Wahala wajen bacci saboda daukewar numfashi, tari ko numfashi sama-sama
   4. Fidda sauti na whistling wato sauti mai nuni da wahalan numfashi (yawanci yara masu fama da cutar asma sun fi fama da wannan)
   5. Tari ko kuma numfashi sama-sama da ke kara ta’azzara saboda virus na mura da makamantarsu

  Alamu da ke nuni da cewa watakila cutar asma ta yi tsanani

  1. Idan alamomin asman suka cika faruwa ga mara lafiya akai-akai
  2. Karuwan wahalan numfashi
  3. Yawan bukatar amfani da quick-relief inhaler akai-akai

  Wajen wasu mutane, alamun asama na ta’azzara ne saboda wani yanayi da suka shiga. Wasu daga cikin wadannan yanayai sun hada da:

  1. Exercise-induced asthma, ma’ana asmar ya ta shi ne saboda atisayi. Hakan kuma ya kan iya fin karfi idan iska na da busawa sosai kuma da sanyi.
  2. Occupational asthma, wato irin asma da kan ta’azzara saboda wajen aiki. Hakan na faruwa ne watakila saboda wani wari ko kamshi na wani chemical, ko gas ko kuma kura da ake amfani da shi a wurin.
  3. Allergy-induced asthma, wato irin wannan asman na tsananta ne domin irin wani abu da jikin mutum baya so. Wannan kan samu saboda wani airborne substance, irin su mold spores (burbudin fusa), da dattin kyankyaso da makamantansu.  

  Mai karatu na iya duba: Amfanin man zaitun ga dan adam

  Lokacin da ya kamata a ga likita

  Matsanancin asma attack na iya halaka mutum. Mara lafiya ya tabbar ya san ab inyi idan alamun asman shi ya tsananta. Wannan kuma abin yin likitan shi ne zai gaya masa. Alamun emergency asthma sun hada da:

  1. Yawan faruwan daukewar numfashi ko kuma yawan faruwar numfashi sama-sama
  2. Rashin samun sauki ko da an yi amfani da quick-relief inhaler irin su albuterol
  3. Daukewar numfashi idan an danyi aiki da ba mai yawa ba

  Je ka maza ka ga likita:

  Idan kana zaton ka kamu da cutar asma: Idan kana yawan tari da numfashi sama-sama da kan dauki lokaci mai tsayi ko kuma wani alamu na cutar asma na daban, to yi kokari ka ga likita cikin gaggawa. Fara jinyar asma da wuri na iya kare mutum da shiga hatsarin kamuwa da matsanancin matsalar huhu sannan kuma zai iya kare mutum daga ta’azzarar cutar.

  Don kula da yanayin jikinka bayan an same ka da cutar: Idan ka san kana da cutar asma to ya kamata ka zamanto kana bibiyar likitanka don ya taimaka maka ku kula da yanayin cutar. Shi wannan kula na yau da kullum idan ya zama jiki ga mai cutar asma na taimakawa wajen kariya daga fadawar asthma attack mai hatsari nan gaba.

  Idan alamomin cutar asmarka suna tsananta: Maza-maza tuntubi likitanka idan alamomin tsananta cutar sun nuna, misali kamar kana shan magani amma abun baya sauki ko kuma bukatan amfani da quick-relief inhaler ya na yawa a gare ka. Kar ya kansance ka ce za ka yi manejin lamarin da yawan shan magani a gida. Idan mara lafiya ya yawaita amfani da maganin asma ya na iya haifar da wani matsalar kuma na daban ko kuma ya kara ta’azzara cutar.

  Domin a duba irin ci gaba da ake samu akan jinyar da ake yi: Cutar asma cuta ce da kan canza, wato ma’ana it changes over time. Saboda haka yi kokarin ganin likita a kai-kai don ku rika tattauna irin yanayin da ka ke ji don likitan yasan matsayin cutar a jikinka kuma ya taimaka maka ta inda ya dace.

  Wai shin me ke kawo ciwon asma ne?

  Babu wani takamammen dalili da za a ce ga shi, shi ke sa wasu su kamu da cutar asma sannan wasu kuma basu kamuwa da shi, amma dai ana zaton dalilai da kan kawo shi sune dalilan muhalli (environnment) da kuma gado.

  Abubuwan da ke haddasa asma (asthma triggers)

  Exposure ga irritants da kuma wasu substance daba-daban na jawo abubuwan da kan haddasa asma. Abubuwa da kan haddasa asma ya danganta ne daga mutum zuwa mutum. Ga wasu da cikinsu:

  1. Airborne substance irin su pollen (irin burbudi ko gari da ke fitowa daga flower), da irin ‘yan kwarin nan da ke cikin kura wadda ido baya ganinsu, ana kiransu da Turanci dust mites, da burbudin fusa (mold spore), da dattin kyankyasu da sauransu.
  2. Matsalar numfashi ko respiratory infection kamar su mura
  3. Motsa jiki ko ta atisayi ko kuma don wani ayyuka na daban (exercise-induced asthma
  4. Iska mai sanyi
  5. Abubuwa masu gurbata iska (air pollutants and irritants)
  6. Wasu magunguna, kamar su beta blockers, da su aspirin, da irin su ibuprofen (Advil, Motrin IB, da sauransu), da naproxen (Aleve)
  7. Yanayi mai girgiza hankali (strong emotions) da kuma gajiya (stress)
  8. Abubuwan da ake sakawa a abinci irinsu sulfites da su preservatives wadda ake sakawa a irin su beverages, da su shrimps, da busassun ‘ya’yan itace, da su dankalin da ake sarrafawa a inji , da giya da wine da sauransu
  9. Gastroesophageal reflux disease (GERD), irin cutar da kansa acids na cikin mutum su taru a makogwaro

  Dalilai da ka iya sa mutum ya kamu da cutar asma (risk factors)

  1. Idan wani daga cikin dankin mutum ya na da ciwon
  2. Allergic condition kamar su atopic dermatitis
  3. Kiba fiye da kima
  4. Shekan hayakin taba ko da mutum ba mashayin taban ba ne
  5. Hayakin da ke fitowa daga salansar mota ko makamancin haka
  6. Exposure to occupational triggers kamar irin chemical da ake amfani da su wajen noma da masana’antu

  Matsalolin da cutar ke haifarwa (complications)

  1. Matsalolin da ke hana bacci ko aiki ko kuma wani recreational activities
  2. Hana mutun sukuni wajen aikin yau da kullum - kullum sai rashin lafiya
  3. Tsukewar bronchial tubes wadda shi ne ke ba da damar numfashi da kyau
  4. Yawan zuwa emergency room ko kuma kama mutum a gadon asibita saboda severe asthma attack
  5. Sides effect na amfani da wani maganin asma din na lokaci mai tsayi

  Yana da kyau a sani samun jinyar da ya dace na bada gudumawa sosai wajen rage irin complication da cutar asma kan haifar.

  Za a iya duba: Yadda za a rage suga a cikin jinni ba tare da shan magani ba

  Kariya daga cutar

  Duk da cewa ba wani abin da zai warkar da cutar asma amma mara lafiya na iya rage shiga hatsarin samun severe asthma attack ta hanyar aiki tare da likitansa wajen samo tsari da za a bi daki-daki na rayuwa da cutar ba tare da an shiga hatsari ba. Ga wasu abubuwan da mara lafiya ya kamata ya bi don kariya daga shiga hatsarin complications na asma:

  1. Kokarin bin asthma action plan
  2. Tabbatarwa an samu rigakafin mura da kuma na pneumonia
  3. Sani da kuma kokarin kariya daga asthma triggers
  4. Kula da numfashi
  5. Sani da kuma magance duk wani attack na asthma din cikin gaggawa
  6. Shan magani kamar yadda likita ya bayar da umarni
  7. Mai da hankali idan yawaitar bukatan quick-relief inhaler ya yi yawa

  Kamar yadda muke fada a kullum, duk wani matsala na rashin lafiya kar ayi wasa da shi. A yi kokarin ganin likita da zarar bukatar hakan ta taso. Allah Ya bamu lafiya. Ga mai son karanta wannan makala da harshen Turanci, ya na iya latsa nan.

Comments

0 comments