Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

 • Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kuma tare da sanin hanyar da zamu bi mu ga mun cimma nasara akan wannan kuduri abu ne mai muhimmanci.

  Sanin kaloris nawa muke bukata, da yawan abinci mai kyau da inganci da jikinmu ke bukata, da kuma yadda ya kamata mu rinka motsa jikkunanmu ilimi ne da kowani dan adam ya kamata ya same su tun da dai abu ne da ya shafi kowa da kowa - babba da yaro. Yayin da a kullum idan mun ziyarci likita ko kuma wani wajen harkar kiwon lafiya na daban, za ka ga bayanai birjik ko ta ina game da wannan maudu’in ta yadda mutum zai zaci idan an mai da hankali wannan ilimi ba wai ilimi ne boyayye ba – yana nan ko ta ina.

  To amma, wai shin mene ne nutrition?

  Nutrition na nufin samarwa ko tabbatarwa samun wadatacciyar abinci mai kyau da jikinmu  ke bukata don kasancewa cikn koshin lafiya da kuma kuzari kamar yadda ake bukata. Kasantuwar mun iya mun samarwa jikinmu lafiyayye kuma wadatacciyar abinci, da adadin vitamins, da kuma su minerals isashshe domin samun daman gudanar da harkokinmu na yau da kullum shi ne abinda nutrition ko kuma nutritional need ya kunsa.

  Sani mene ne ma’anar nutrition wani bangare ne daban, sannan kuma sanin diet din da muke bukata shima wani bangarenne can na daban. Saboda haka yanzu ya ya zamu iya sanin yawan adadin abinci mai kyau da inganci da jikinmu ke bukata? Amsar tambayar shi ne, ta hanyar ilmantar da kawunan mu akan Health and nutrition, sanin mene ne na ke bukata na abinci, me iyalai na ke bukata kuma a dauki wannan ilimi ayi amfani da shi wajen sayan abinci  da girka shi da mu da iyalanmu. 

  Sannan kuma yadda muke gudanar da rayuwanmu ma, wato lifestyle a Turance,  ya na nuni da irin nutrition da muke bawa jikinmu – lifestyle na gaba wajen nuni da irin abinci da sauran nutrient da muke bawa jikinmu.

  Kamar yadda muka ce nutrition ya na da alaka da lifestyle din mutum saboda yana nuni da irin nutrient da muke sakawa jikinmu domin kasancewa cikin koshin lafiya. Maudu’i da ya shafi cin abinci isasshe kuma mai inganci maudu’i ne da ake ta faman magana akansa tuntuni, tun daga kungiyoyi masu zaman kansu har izuwa na gwamnati. Misali, a majalisan dinkin duniya, wato United Nations, akwai kungiyoyi daban-daban kamar Food Drug Admiistration (FDA) sannan kuma anan kasashenmu misali a Najeriya muna da National Agency for Food and Drug Administration and Control (NAFDAC).  Wadannan kungiyoyi ba wai kawai kula suke da irin abinci da jama’a suke ci a kasashensu ba, har ma yadda mutane ke alaka da kwayoyi na magani da na maye. Suna kula da masu yin magunguna da masu sayarwa domin su tabbatar jama’a basu fada cikin hatsari ba, sannan suna samun abinci da ya kamata da kuma inganci. Kusan ko wacce kasa a wannan duniyar ta mu ta na da kungiya ko kungiyoyi masu alhakin kula da wannan lamari.

  Mene ne nutritional need na mu, wato abubuwa da abinci da muke bukata domin samun lafiya da kuzarin jikinmu?

  Amma duk maganganu da muke ta yi akan nutrition, shin mun ma san asali yawan adadin abinda muke bukata na nutrient domin samun lafiyayyen jiki? Mun san yadda ko hanyar da za mubi domin biyan wannan bukatar ta mu? Ta ya ya za mu ci abinci don samun asali irin value da muke nema na nutrient? Ba na zaton akan wannan lamari mutane sun samu ishashen ilimi da zai amsa duk wadannan tambayoyi duk da irin matakai da kuma maganganu da ake yi akan nutrition a kullu yaumin. Kullum za ka ji ana maganar fortified cereal ko fortified milk, ana maganar vitamins kaza da kaza a jikin gwangwanayen da ledojin abinci, to amma shin mun san asali adadin wadannan abubuwa da muke bukata ne, kuma asalin nawa muke samu daga wadannan abincin? Bana zaton mutane da yawa za su iya amsa wannan tambayar.

  A wani bangaren kuma, za ku iya duba wannan makalar: Cutar asma alamominsa illolinsa da kuma hanyoyin kariya daga cutar

  Yawa yawancin lokaci zaka tarar bukata da muke da shi na minerals da vitamins sun fi bukata kaloris da muke da shi a jikinmu. A irin wannan lamari sai kaga mutane sun koma shan magunguna da ke dauke da vitamins da kuma minerals domin cike gurbin, yawanci saboda umarnin likita. Wani ayar tamabayar kuma anan shi ne, shin wadannan vitamin and mineral supplements din suna ko biyan bukata, ko a’a? Amsar tambar dai shi ne, akwai babban ayar tambaya akan alfanun supplements domin kuwa akwai ce-ce-ku-ce masu yawa game da shan food supplements.

  A gaskiya ilimin nutrition ilimi ne mai matukar sarkakiyar gaske. Domin akwai bangarori daban-daban na wannan ilimi, kuma kowa da irin abinda ya kamata ya sani saboda da bukatu da suka sha bam-bam na jikinsa, ko shekaransu ko kuma jinsinsa. Misali mutumi da ke fama da ciwon zuciya bukatarsa ta nutrition ba daya ya ke da na lafiyyayen mutum ba. Haka zalika bukatun mata ya sha bam-bam da na maza. Nutritional need na mata tsuffi ba daya ya ke da na mata matasa ba, da dai sauran dalilai daban-daban. A sabili da haka, sanin abinda mutum ke bukata na nutrient a cikin abinci na bukatan mutum ya kasance yana sane da condition na shi tare da neman ilimin akai-akai game da nutrition da ma sauran bangarori na lafiyan jikinsa.

  Ganin irin wannan sarkakiya da ke tattatre da harkar ilimin nutrition, abu mafi a’ala shi ne ya kasance kowa as individual ya san yanayinsa da yanayin jikinsa. Sanin hakan zai sa mutum ya iya sanin mene ne asalilin nutritional need na sa da kuma hanyar da zai bi domin samun isashen nutrient da iyalinsa.

  A karshe abinda na yi concluding shi ne, neman ilimi shi ne amsa! Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya, amin.

  Mai karantu na iya duba: Dalilan da ka iya sawa a koma vegan diet

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Mece ce cutar mantuwa (amnesia)? Idan aka ce mutum na fama da cutar amnesia dai to ana nufin cutar da ke sa mutum ya manta abubuwa kamar abubuwan da su ke zahiri, da kuma bayanai game da wani abu ko kuma manta abinda ya faru da su da makamanta ire-iren wannan mantuwa. Mutane da su ke dauke da wanna...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Saurin Fushi Na Kawo Da Na Sani. A wani ƙauye akwai wani mutum  ana kiran sa Abu Sabiru, ya kasance mai tsananin haƙuri da kawar da kai akan wasu al’amura. Dalilin da ya sa ma ake kiransa Abu Sabiru kenan. Yana zaune tare da matarsa kyakkyawar gaske ...
 • Ku latsa nan don karanta darasin rana ta uku. DARASI NA 1 Matakan rubutun gajeren labari A jiya mun yi bayani akan matakan da ake bi wajen tsara labari, yau kuma za mu bayani a takaice kan matakan da ake bi wajen rubuta ingantaccen labari. Waɗannan matakai ba tabbatattu ba ne, ma'ana ba wajibi ne...
 • Ku latsa nan don karanta babi na shida. Habeeb na kwance a kan doguwar kujera ya ji an murɗa handle ɗin ɗakinshi tare da turo ƙofar a hankali. A hankali ya buɗe idanunsa da suka yi nauyi sakamakon ciwon kan da yake fama da shi. "Fateemah" ya faɗa a ransa, lokacin da ya kai duba ga Jummai da ke ts...
 • Uwargida ba za ki yi dana sanin koyan yadda ake yoghurt in fruits ba. Domin kuwa kayan dadi ne sosai da sosai kuma cikin mituna kalilan za ki hada. Ba a ba yaro mai kiwiya!!! Wannan recipe yana daya daga cikin recipes da muka koyar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman a nan Bakandamiya. Abu...
 • Hadin special salad nawa na musamman ne! Ga sauki ga dadi, uwargida sai kin gwada za ki bani labari! Wannan ma yana daya daga cikin recipes da muka koyar a Ramadan a shirin girke-girkenmu wadda aka gabatar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin ko kin tuna gashin tsokar kaza da muka koya...
View All