Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin kayyade iyali

Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin kayyade iyali

 • Mene ne kayyade iyali?

  Kayyade iyali ko tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wani mataki ne da ma'aurata kan dauka don hana mace daukan ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko ?ayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa ko dai ma don wasu dalilai na daban, kamar abin da ya shafi lafiyar uwa da makamantan su. Duk da cewa akwai ce-ce-ku-ce da yawa game da halacci ko rashin halaccin tsarin kayyade iyalin amma lamari ne da ya kamata duk ma’aurata su zamanto sun samu ilimi game da shi don wata?ila wata rana zai musu amfani.

  Amma babban abu mafi muhimmanci shine a duk lokacin da ma’aurata suka yi niyyar ?ayyade iyalinsu to su tafi wurin ?wararren likita don samun shawarwari ta yadda zai zama an yi dace.

  Ire-iren hanyoyin kayyade iyali

  Da farko yana da kyau ma’aurata su sani akwai hanyoyi guda biyu da ake bi domin ?ayyade iyali. Wa?annan hanyoyin kuwa su ne:

  1. Natural contraception
  2. Artificial contraception  

  Natural contraception

  Wadannan sune hanyoyi da ake bi ba tare da shan magani ko kuma saka wani abu a jikin mace ko na miji ba domin hana daukan ciki. Kafin mu yi bayani game da ko wani dayansu ya na da kyau mu fahimci abinda ke faruwa har ciki ya samu. Ga yadda lamarin ya ke kamar haka:

  Hoton mahaifa yayin da ba maniyyi kuma babu kwai

  Ha??in mallakar hoto: Babycenter

  Yadda ake daukan ciki

  A mahaifa ko uterus a Turance akwai wasu wurare guda biyu gefe da gefe da ake kira da suna ovaries (maikaratu na iya duba hoton da ke sama don fahimtar wannan bayani). Wadannan ovaries din sune mazaunar koyayen mace. Duk wata (month) kwai daya ko fiye za su fito da ga ovary (ovulation) su bi wani hanya da ake kira da suna fallopian tube, anan ne idan akwai maniyi sai su hadu. Wannan haduwa na kwai da maniyyi shi ake kira da suna fertilization. To wannan fertilized egg din sai ya gangaro gefen da ciki ke zama na mahaifa ya dasu wato implantation ke nan a Turance. Wannan shi ne mafarin cikin ke nan.

  To amma wannan kwan ko koyayyaki na rayuwa ne na tsawon awa 12 zuwa 24 (wasu sun ce ya kan kai har kwana uku) idan bai samu maniyyin namiji ba sai ya lalace. Sannan shi kuma maniyyi na iya zama a jikin mace har na tsawon kwana shida ne ko bakwai tsanani kafin ya lalace. Saboda haka idan mace ta sadu da na miji maniyyinsa na iya zama har na kwana shidda wadda hakan na nufi a wannan tsakanin idan kwanta ya fito to za ta iya yin ciki ke nan.

  Hoton mahaifa yayin da maniyyi da kwai suke haduwa

  Ha??in mallakar hoto: Mybaby’sheartbeatbear

  Ku kalli wannan bidiyon don ganin yadda mace ke daukan ciki

  Ire-iren natural contraception

  1. Withdrawal method

  Withdrawal wato abinda ake kira inzali da Hausa: Shi ne hanyar da namiji ke fitowa daga jikin mace a yayin saduwa kafin maniyyinsa ya fito. Wannan fitowa shi ne ake kira da outside ejaculation a Turance. Wannan hanya masana sun tabbatar da cewa saboda wahalarsa ya na amfani ne kawai kashi 75% zuwa 80% wajen hana daukan ciki domin wani lokacin maniyyin ?in na iya fitowa ka?an ba tare da sanin namiji ba.

  2. Barin saduwa a lokutan da mace za ta iya daukan ciki wato idan tana ovulating

  Ga yadda ake bin diddigin lukutan da mace za ta iya yin ciki. Mace ta fara ?irga kwanaki, tun daga ranar farko da ta fara al’ada har kwana sha hu?u. Bayan kwana sha hu?un nan sai a fara kirge, rana na sha biyar har zuwa sha takwas ko kuwa sha tara to wa?annan kwanaki su ne lokacin da mace za ta iya daukan ciki. Amma wasu lokutan ya danganta ne daga mace zuwa mace da sanin lokacin ovulation da kuma yanayi da mace ke ciki. Saboda haka yana da kyau a ziyarci likita domin samun cikakken bayanin yadda mace za ta bi diddigin ovulation na ta.

  Wasu hanyoyin natural contraception sun hada da:

  Duba temperature na jiki a kullu yaumin domin sanin lokacin ovulation. Domin a lokacin ovulation temperature jiki na tashi kadan kamar da degree 0.2. Sanin wannan zai taimaka wajen daukan matakin da ya dace don hana daukan ciki.

  Duba canji da ake samu na cervical mucus (wato farin ruwa mai yau?i-yau?i da ke fitowa a gaban mace). Idan mace na ovulating shi wannan ruwa na canzawa. Ya kamata idan mace ta na son gwada wannan hanyar ta ziyarci kwararru akan lamarin kiwon lafiya da ya shafi mata don a koya mata yadda za ta yi da kuma yadda za ta iya banbance wannan cervical mucus din.

  Dubi wannan makala don karanta cikakken bayani na hanyoyi daban-daban na natural contraception.

  Artificial contraception

  Artificial contraception su ne hanyoyi daban-daban da ake bi don ?ayyade iyali ta hanyar shan magani ko kuma ta hanyar saka wani abu. Hanyoyin suna da yawa, amma ga wasu daga cikinsu kamar haka:

  1.Intrauterine device (IUD)

  IUD wani ?an karamin roba ne mai shape na T da ake sakawa a mahaifar mace don ya hana maniiyin namiji haduwa da kwai ko kuma idan har ma sun hadu ba zai bawa kwan daman implanting a mahaifar ba. Wannan hanyar masana sun tabbatar idan an yi shi da kyau yana amfani wajen kashi 99% wajen hana daukan ciki. Ya kan iya zama har na tsawon shekara 5 zuwa10 a jikin mace. Sannan ana iya cire shi a kowani lokaci idan ana so. Kuma da zaran an cire shi za a iya daukan ciki nan take.

  An tabbatar da cewa wannan hanyar bai da hatsari sosai ga mace. Amma dai dan abinda ba za a rasa ba wani lokacin mace na iya samun infection, wato kwayoyin cuta, sannan ya kan iya kara yawan jinin al'ada da kuma tsawonsa musamman a watanni 6 na farkon sakawa. Idan mace na bukatan amfani da wannan hanyar ta tabbar ta samu ?wararriya ko ?wararren likita domin ta saka mata sannan ta tautauna da likitar don sanin abin yi da kuma yadda abin ke aiki.

  Ga hoton IUD

  Ha??in mallakar hoto: drugs.com

  2. Oral contraceptive pills ko combine pills

  Magani ne na kwaya da mace za ta rika sha mafi akasari har na kwana 21 a jere kuma a lokaci daya a kullum sannan ta tsaya na kwana bakwai ba shan maganin. Haka za ta ri?a yi duk wata. Wannan pills din na saka jiki ya rika releasing hormones ne da zai hana mace daukan ciki. Wannan hanyar tsarin ?ayyade iyalin wani lokacin yana da wuya domin dole mace ta tuna kullum ta sha kwayan yadda ya kamata. Idan kuma a ka manta yana iya rage kaifin aikin maganin. An ce shi wannan hanyar ya na aiki kamar kashi 99% shi ma idan aka bi shi yadda ya kamata

  Wani lokaci, shan pills din kan haifar da jin amai ko gudawa, da mood swings (canjin yanayi) da dai wasu yanayi na rashin jin dadi musammam a lokacin da aka fara amfani da pills din ba da jimawa ba.

  Ga hoton wasu daga cikin irin pills ?in

  3. Contraceptive implants

  Wannan wani hanya ne da ake dasa wani roba karami a hanun mace. Shi wannan roba zai rika fidda wani hormone da ake kira da suna progestogen a cikin jini ne da zai hana mace daukan ciki. Yana iya zama a jikin mace har na tsawon shekara 3. Amma ana iya cire shi duk lokacin da ake bukata a asibiti. An tabbatar shi ma wannan hanyar tsarin kayyade iyali na amfani wajen kashi 99% ko fiye wajen hana daukan ciki. Side effects na shi sun hada da mood swings, amai, wani lokacin ya kan hana mace al'ada kwata-kwata ko kuma al'adarta ta rikice da ma wasu side effect din na daban.

  Go hoton contraceptive implants.

  Ha??in mallakar hoto: Healthdirect

  4. Diaphragm or cap

  Wani roba ne mai kama da hula da mace kan sa lokacin saduwa don hana maniyi shiga mahaifarta. Ana amfani da shi ne tare da wani gel da ake kira da suna spermicide. Amfani da diaphragm na kare mace da daukan ciki da kashi 92% ko fiye idan anyi yadda ya kamata.

  Ga hoton diaphragm

  Ha??in mallakar hoto: daveasprey

  5. Contraceptive injection

  Allura ne da akan yiwa mace don hana ta daukan ciki. Yawanci allurar na aiki na tsawan sati 8 zuwa sati 13. Shi wannnan hanyar ko da an bar yin allurar ya na iya kaiwa shekara kafin mace ta iya sake daukan ciki. Sannan ya kan iya kawo matsalar al'ada ko ma tsaida shi gaba daya. Side effects na shi sun hada da, saka ciwon kai, mood swings, kara kiba da sauransu.

  Wasu hanyoyin sun hada da amfani da kwaroron roba wato condom na maza da na mata yayin saduwa, da contraceptive sponges da dai sauransu. Za ku iya karanta wannan makala cikin harshen Turanci don samun cikakken bayani game da hanyoyin daban daban na tsarin iyali

  Wannan shi ne dan abin da za mu iya kawo muku game da wannan maudu’i na tsarin ?ayyade iyali. Da fatan za a amfana kuma idan akwai wani kuskure da ku ka gani, kunnenmu a bude suke don sauraro kuma insha Allah za mu gyara duk wani kuskure da aka nuna mana. Ka da ku manta wannan makala an rubuta ta ne don karuwar ilimi ba don a yi substituting da zuwa wajen likita ba. Cikakken likita ne kawai zai iya rubuta magani ya kuma gaya maka/ki yadda za ka/ki yi amfani da maganin. Allah Ya kara mana lafiya, amin.

  Kuna iya karanta wata makalar da ta yi bayani akan hanyoyin kayyade iyali da kuma illolinsu.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta labarin Afuwa ƙwaya Ce, Ka Shuka Ɗaya Ka Girbi Goma. An yi wani attajiri da ke da dukiya mai yawan gaske, ana kiransa Abu Tammamu. Saboda yawan dukiyarsa, bai san iyakacin abin da ya mallaka na daga gidaje da gonaki da dabbobi da bayi da sauran kadarori ba. B...
 • Ku latsa nan don karanta shafi na 12 da 13. SHAFI NA 14 Tana isowa ta dubi Mama tare da mika mata wayar "Ga mamansu Sumayya za kuyi magana." Mama ta amshi wayar ta saka akunne ta na fadin salamu alaikum jin shiru yasa ta dubi fuskar wayar tare da fadin "La kinga ta katse." Fati ta amshi wayar ta...
 • Zamantakewar aure, zamantakewa ce mai wahala, matuƙar wahala kuwa. Sai dai da zarar ka fahimci tana da wahalar, sai ta zama mai sauƙi a gare ka. Domin fahimtar tana da wahalar shi zai ba ka damar neman iliminta. Shi kuma iliminta sai ya ba ka damar samun sauƙin ta. A shirinshi da ya saba gabatarwa ...
 • An haifi Olufela Olusegun Oludotun Ransome-Kuti a ranar Asabar 15-10-1938, a Abekuta ta jihar Ogun. Iyayensa manyan mutane ne domin Mahaifiyarsa Fummilayo Ransome-Kuti, 'yar gwagwarmaya ce, mai fafutukar kwato 'yancin mata. Mahaifinsa Isra'el Olodotun Ransome-Kuti, babban limamin coci ne, shugaban ...
 • Idan aka ce Hepatitis, to ana nufin ciwon hanta kenan a Hausance. Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta na...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Dogaro Ga Allah Jari. Cikin ƙasashen Mongol an yi wani babban Sarki mai yawan jarumai ana kiran sa Bihikatu. Shi wannan Sarki jarumi ne amma mugu ne na ƙin ƙarawa. Tun da yake bai taɓa yin afuwa ga wanda ya saɓa masa ba. Ba a taɓa ganin dariyarsa ba s...
View All