Rubutu

Blogs » Kiwon Lafiya » Coronavirus: Mece ce ita kuma ya ya za a kare kai daga kamuwa da ita?

Coronavirus: Mece ce ita kuma ya ya za a kare kai daga kamuwa da ita?

 • Sunar coronavirus dai a wannan lokaci da muke ciki wata suna ce da kusan kowa ya santa babba da yaro. To amma ba kamar yadda wasu suka dauka ba, ita wannan suna ta coronavirus suna ce ta wata dangi cututtuka da suka shafi numfashi wadda suka hada da MARS (Middle East Respiratory Syndrome), da kuma SARS (Severe Acute Respiratory Syndrome) da kuma sabuwar cikinsu, wato covid-19, wacce ita ce ta addabi duniya a wannan zamani da muke ciki.

  Tarihin covid-19

  A watan Junairun shekara ta 2020, gungiyar lafiya ta duniya wato World Health Organization (WHO), ta yi declaring cutar numfashi na covid-19 a matsayin cutar da ta zama matsalar lafiya ta duniya (global health emergency). Bincike ya nuna cewa wannan cutar dai ta samo asali ne daga kasar Sin, wato China, a wani yanki da ake kira Wuhan. An yi imanin cewa abun ya fara bulla ne a farkon watan Disamba ta shekarar 2019.

  A farkon lamari duk wadanda suka kamu da ita cutar an samu suna da alaka ne da tafiya zuwa kasar China. A yanzu haka kasashe ko yankuna na duniya sama da 200 ne ke fama da ballewar wannan cutar. Cutar ta zama wata annoba da kusan ba a taba irin ta ba a duniya, wadda a kusan duk duniya gwamnatoci sun saka dokan hana fita wa mutanensu domin kokarin shawo kanta.

  Mece ce covid-19?

  Cutar numfashi ta covid-19 - kamar sauran danginta na coronavirus kamar su MARS da SARS -  cuta ce da ta ke haddasa matsala irin kamar na mura. Alamunta sun hada da kamar wahalar numfashi da busashshen tari da zazzabi mai tsanani da sauransu. Wannan cutar na yaduwa ne daga mutum zuwa mutum ta hanyar iska don ‘yawu da ke fitowa daga baki yayin tari ko atishawa. Cutar na iya kama mutum har mutum ya warke a wani lokaci ba tare da wani jinya ba, sannan wani lokacin kuma cutar na iya yin tsanani har ya kai ga mutuwa.

  Mutane da suka fi kowa shiga hatsarin tsananin wannan coronavirus din su ne tsofaffi da mutane masu cutuka irinsu cutar kansa, ciwon zuciya da makamantansu.

  Cutar coronavirus cuta ce da ke yaduwa cikin saurin gaske saboda haka masana su ke cewa mutane lallai su rika yin nesa da juna musamman a wannan lokacin da ake fama da ita.

  A yanzu dai ba wani magani da aka tantance na wannan cutar. Masana sun bazama suna aiki akai da fatan nan ba da jimawa ba za a sami maganin wannan annoba!

  Babbar shawarar da ake bawa jama’a a yanzu ita ce su kansance sun ilmantu akan wannan cutar ta hanyar samun bayanai ta kafa sahihiya domin su ga yadda za su kare kawunansu.

  DubiCutar asma: Alamominsa, illolinsa, da kuma hanyoyin kariya daga cutar

  Ga wasu daga cikin hanyoyin kariya daga wannan cutar kamar yadda hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta wallafa a sashinta na Internet. Ga su kamar haka:

  1. Wanke hannu akai-akai

  A wanke hannu su wanku sosai da sabulu na gargajiya ko dai na ruwa ko kuma tsaftace hannun da sinadarin nan na alcohol-based hand rub ko hand sanitizer.

  Amfanin yin hakan: Wanke hannu da sabulu da ruwa na kashe kwayoyin cutar da ke hannun mutum walla’allah ko hannun na dauke da su.

  2. Rage cakuduwa cikin jama’a (social distancing)

  Idan ya zama lallai za a hadu da mutane, ya kasance a kalla a kwai rata na abinda bai kasa kafa uku tsakanin mutane ba. Saboda idan mutum na tari ko atishawa iskar ba zai kai ga wadda ke nesa ba.

  Amfanin yin haka: Idan mutum mai fama da tari ko atishawa ya yi tari akwai wasu ‘yan droplets da ke fita da ke iya daukan kwayoyin virus. Kuma mun san daya daga cikin alamun covid-19 su ne wannan tari ko atishawa din. Idan mutum na kusa zai iya shakar wannan virus din kuma ya kamu da cutar. Yin nesa na rage hatsarin kamuwa da cutar sosai.

  3. Kiyaye taba ido ko hanci ko baki

  A saboda hannun mutum na tabe-tabe na wajaje daban-daban, hanya mafi sauki na samun cutar shi ne ta hanyar yawan taba fuska da hannu. Idan hannu ya dauko virus sai mutum ya taba bakinsa, ko hancinsa ko idanuwarsa, sai virus din ya shige jikin mutum ta wannan kafar, shi ke nan virus ya samu gida!

  4. Bin ka’idar tsaftar numfashi (respirator hygiene)

  Mutum ya tabbar shi da mutanen da ke kusa da shi suna bin ka’idar tsaftar numfashi wato respiratory hygiene. Abinda respiratory hygiene ke nufi shi ne ya yin da ake tari ko atishawa mutum ya rufe bakinsa da hancinsa da gwiwar hannunsa ta ciki, wato bent elbow a Turance. Ko kuma ayi amfani da tissue paper wajen tare tarin ko atishawan sannan kuma a yar da tissue din a wurin da ya dace ya yin da aka gama amfani da shi cikin gaggawa.

  Amfanin yin haka: Idan ba ku manta ba mun ce ya yin tari ko atishawa, virus na bazuwa ta hanyar droplets (dan iska da digon ruwa-ruwa da ke watsuwa) da  ke fita, to idan aka tare, an tare hanyar bazuwan virus din ke nan ta wannan hanyar. Idan mutum ya bi wannan shawara zai kare na kusa da shi daga kamuwa da cutar numfashi irin su covid-19.

  5. Idan mutum na jin zazzabi, ko yin numfashi da kyar da kuma tari, to a nemi taimakon kwararru da wuri

  Idan mutum na jin zazzabi, ko yana yin numfashi da kyar da kuma tari, to ya nemi taimakon kwararru da wuri ta hanyar zuwa asibiti ko dai ta duk hanyar da ake bi don samun taimakon likita cikin gaggawa a inda a ke da zama.

  Amfanin yin haka: Neman taimakon kwararru cikin gaggawa na ba su dama su gano asalin abinda ke damun mutum, sannan kuma su ke da duk wasu bayanan gaskiya da kwarewa game da lamarin wannan cuta, saboda haka su suka fi cancanta a tunkara da wuri.

  6. Ilmantar da kai da kuma bibiyan duk wani sabon lamari game da wannan cuta

  Ya kasance mutum na bibiya kuma yana ilmantar da kansa da duk wani sabon abu game da cutar covid-19. Yin hakan shi ne zai kawo sanin abin yi idan an ji alamun cutar ko kuma wani na kusa da mutum ya ji.

  Hanyoyi masu sauki na jin labaru sune sauraren gidajen rediyo da talabijin da kuma taskokin yanar gizo. Sannu a lura kwarai, akwai kafofi da dama, musamman a yanar gizo dake yada karerayi game da cutar.

  Mai karatu na iya dubaCiwon kan migraine: Dalilai da alamun kamuwa da shi da kuma hanyoyin maganceshi

  7. Saka surgical mask

  Ga mara lafiya: Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutum na iya saka mask ne idan yana tari ko kuma yana numfashi da kyar ko kuma yana da zazzabi mai tsanani. A nan za a saka ne don kare jama’a da ke kusa don kar su sami kwayar cutar a wurin mai dauke da ita.

  Ga mai jinyar wani: Idan kana tare ne da mutumin da ke da wannan cuta, hukumar WHO ta ce kasa mask duk lokacin da ka ke daki daya da mara lafiyan. Yin hakan na bada kariya.

  Ga mai lafiya: A fadin hukumar, mutum mai lafiya baya bukatar saka mask domin babu wani shaida da aka ginata ta hanyar ilimi da ta ke nuni da cewa mask na iya kare mutum daga daukan coronavirus. Sannan WHO ta ce idan har za ka sa to ka bi duk doka da ake bi na kariya, kamar wankin hannu akai-akai, tare tari da cikin gwuiwar hannunka da dai sauran hanyoyin kariya da masana lafiya suka ba da shawaran a bi.

  Wata sabuwa game da mask

  Da shike wannan coronavirus din sabuwar cuta ce da masana ke ta aikin gano yadda ta ke, hukumar Center for Disease Control and Prevention (CDC) da ke kasar Amurka ta ce mutane su rika saka wannan mask din ko da suna da lafiya, domin sabon bincike da ya fito na kwana-kwanan nan ya yi nuni da cewa cutar na bazuwa ta iska. Hukumar ta kara da cewa saka mask na iya rage hatsarin kamuwa da cutar.

  Amma dai sunce ba wai yana hana daukar cutar kwata-kwata ba ne sai dai sun yi imani yana ba da dan kariya, kuma malam Bahaushe cewa ya yi, 'sanadi ba ta kadan'.

  Yadda ake saka mask daga hukumar WHO

  1. A wanke hannu da sabulu da ruwa ko a tsaftace hannun da alcohol-based hand sanitizer.
  2. A dauki mask bayan an busar da hannun, sai a duba, a tabbar yana da kyau ba wani matsala a tare da shi.
  3. A yi la’akari da cikinsa (wato wajen da za a kifa a fuska) da kuma samansa (wurin dorawa a hanci). Cikinsa shine farin kala, sannan samansa kuma akwai wani dan karfe ta ciki.
  4. Sai a saka ta hanyar kama robobi guda biyu da ke gefe da gefen mask din sannan a rataye su a kunnuwa. Saman mask din kuma a dora a hanci sannan a matsa don ya kama hancin. A jawo kasan kuma har zuwa gemu.
  5. Idan za a cire, a kamo wadannan robobin da ke rataye a kunnuwa, ba tare da an taba fuska ba, sai a yar a kwandon shara da kyau inda wani ba zai taba ba.

  Wannan shi ne kadan daga abinda zamu iya kawo mu ku daga cutar coronavirus. Muna fatan Allah ya kare mu da duk jama’a na duniya baki daya. Allah Ya bawa marasa lafiya sauki.

  A karshe muna kira ga jama’a da don Allah mu maida hankali wajen bin doka da kuma ka’idoji da likitoci suke gindayawa game da wannan cutar. 'Taya Allah kiwo ya fi Allah na nan!'

  Kuna iya dubaDalilan da ka iya sawa a koma vegan diet

Comments

0 comments