Makalu

Yadda ake gasa tsokar naman sa mai armashi

 • Mutane da dama suna tambayanmu game da yadda ake gasa nama, to alhamdulillahi a yau mun kawo muku daya daga cikin girke-girkenmu da muka koyar a free Ramadhan cooking classes a nan Bakandamiya tare da Umyuman. 

  Assalamu Alaikum warahmatullahi ‘yan uwana barkanmu da warhaka. A yau zamu koyi yadda ake gashin tsokar sa ne, wadda aka fi sani da grilled beef steak a Turance. Uwargida za ki iya amfani da wannan grilled beef steak din a cikin girke-girke daba-daban. Idan kin shirya, mu je zuwa

  Albishir: Wani abin dadin ba dole sai da oven ba ko abin gashin gargajiya za ki yi gashin naman da shi ba. Abin da ki ke bukata kawai frying pan ne!

  Abubuwan hadawa

  1. Tsokan nama sa zalla
  2. Kayan kamshi (habbatussauda, busashshiyar na’a-na’a, garin thyme, da maggi)
  3. Mai

  Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko namanki tsoka zalla ki yanka fala fala kaman fefa. Kamar yadda za ku gani a hoton da ke zuwa a kasa.

  Kun ganni a hoton yadda na ke yankawa.

  2. Abu na gaba shi ne, ki kawo kayan kamshi da muka lissafa a samannan sai ki hade su a waje guda sannan ki sa mai ki cakuda.

  3. Sai ki bi ki shafe wannan nama da ki ka ajiye a gefe da wannan hadin kayan kamshin. Ki tabbatar kin shafe nama sosai da kayan kamashinnan.

   

  Lokacin da na shafe naman da kayan gamshi

  4. A daura abin tuyan kwainki a wuta wato frying pan sai ki sa mai kadan sannan ki dora naman a kai. Idan gefe daya ya yi sai ki juya dayan gefen.

  5. Da namanki ya yi sai ki yanyanka shi a tsaye Kamar yatsu. Ga hoton yadda na yi nawa ku duba a kasa.

  Ga gasashshen naman yayin da na yayyanka shi 

  Karin bayani:

  Wannan gashin tsokan sa ina amfani da shi a girke-girke daban-daban. Kin ga ni in na yi kalan gashin nan, nakan sa shi cikin salad, ko in sa cikin shinkafa, da taliya da sauransu! Abin ba a cewa komi, sai angwada!

  Ga wasu daga cikin hotunan yadda na ke serving gasashshen tsokan sa nawa a kasa.

  Ga gasashshen naman sa namu a salad din latas

  Ga namanmu a cikin jollof na shinkafa

  Ga shi kuma a wani irin samfurin salad na daban

  Zan so in ji yadda ku ke gashin naman sa ku na ku a kasa. Shin kun gwada wannan yadda ake gashin naman sa din na, ina son in ji daga gare ku a comment section.

  Rubutawa: Shaima Alhussainy

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake gashin kifi karfasa

  Posted Jul 12

  Gasashshen kifi karfasa ko grilled fish ko kuma grilled tilapia abinci ne da mutane da yawa suke so kuma suke sha’awar koyon yadda ake sarrafawa. Saboda haka Umyuman ta koyar da yadda ake gashin kifi a cikin recipes da ta koyar a lokacin Ramadan a cikin zaurenta n...

 • Bita ta musamman akan rubutun gajerun labarai: Rana ta biyu

  Posted Jul 12

  Ku latsa nan don karanta darasin ranar farko. DARASI NA 1 Abubuwan lura a rubutun gajeren labari A jiya mun bayyana siffar gajeren labari ta fuskar adadin kalmomi. Mun riga mun san cewar shi Rubutu baiwa ne. Ba kowa ke da baiwar rubutu ba. Duk da haka akwai hanyoyin ...

 • Ko Ruwa Na Gama Ba Ki: Babi na Biyar

  Posted Jul 12

  Ku latsa nan don karanta babi na hudu. Gabaɗaya Asabe da Malam Amadu sun kasa kunne suna jiran Jummai da ke zaune a gabansu, ta faɗa musu wanda ya yi mata ciki, sakamakon tsawon lokacin da ta ɗauka tana ɓoye musu. Kan Jummai na ƙasa ta ce, "Habeeb ne". kusan duk ba s...

 • Physics: Darasi game da energy da kuma work 

  Posted Jul 8

  A wannan makala zamu yi bayani ne akan ENERGY da kuma WORK. Game da wannan darasi abubuwan da ake so dalibai su lura da su sune, energy, work, types of energy, sources of energy, classification of sources of energy, law of conservation of energy da mathematical problems...

 • Tekun Labarai: Idan Farauta ta Ki Ka

  Posted Jul 8

  Ku latsa nan don karanta farkon labarin. Ka sani ya kai Sarkin zamani, an yi wani bafatake mai nasibi a harkar saye da sayarwa, duk abin da ya kama sai ya yi daraja. Akwai lokacin da dirhami ɗaya ke jawo masa ribar dirhami hamsin. A kwana a tashi sai kasuwancin ya juya...

View All