Makalu

Bayanai game da lalurar Autism spectrum disorder (galhanga)

 • Mene ne autism spectrum disorder (galhanga)?

  Autism spectrum disorder ko galhanga wata cuta ce ko ince lalura ce da ke haifar da developmental disorder wadda ke shafan hulda na yau da kullum, da sadarwa (communication) da kuma dabi’ar wadda ke kan wannan spectrum din. Kalmar “spectrum” da ake amfani da shi a autism spectrum disorder ya na nufi alamu daban-daban mabambanta da kuma yanayi tsanani ko rashin tsananin lalurar. Ana samu conditions kala daba-daban masu suna mabambanta da ake hada su a na kiransu da suna ‘autism spectrum disorder’. Za muga wadannan conditions din a gaba.

  Duk da cewar akan bincika a gano mutum na kan autism spectrum disorder a ko da yaushe cikin rayuwarsa amma alamomin wannan lalura suna bayyana ne tun daga shekaru biyu na farko rayuwa mutum.

  Masu wannan lalura suna fama da matsalar sadarwa (communication), da nanata dabi’a iri daya (repetitive behaviour), da restricted interest, sannan da matukar wahala wajen functioning wajen aiki ko makaranta ko ma sauran wurare hulda na rayuwa.

  Yaya alamominsa su ke?

  Social communication and interaction: Yaro ko ma babba da ke fama da lalurar autism spectrum disorder zai iya kasancewa yana samun matsala ko wahalar wajen yin hulda da jama’a da kuma communication (sadarwa). Wasu daga cikin matsalolin da za su iya fiskanta sun hada da:

  1. Su kan gagara amsa kiran sunansu ko kuma a ga alamun kamar ba su ji idan ana kiransu
  2. Yawanci ba su son a yi cuddling na su ko kuma a kama hannunsu. Yawanci sun fi son su yi wasansu su kadai
  3. Ba su iya hada ido da wasu ba sannan wayanci suna da poor facial expression
  4. Ba su magana ko kuma wahala wajen yin maganar
  5. Ba su iya fara magana da mutane ko kuma ba su iya dogon zance da mutane. Sun kanyi Magana ne kwai idan za su nemi wani abu haka.
  6. Su kanyi magana da wani irin murya da ba normal ba
  7. Su kan nanata kalma haka da baki amma basu san yadda za su yi amfani da Kalmar ba a zance
  8. Su kanyi wahala wajen gane tambaya mai sauki ko kuma kwatance
  9. Yawanci basa nuna wani emotion ko yadda suke ji sannan suna nuna alamun rashin fahimtar yadda wasu ke feeling
  10. Su kan nuna gazawa wajen fahimtar nonverbal cues kamar kwatance da makamantansu
  11. Su kanyi hulda da mutane ta hanyar ko dai ko-in-kula ko kuma aggressive ko kuma disruptive way

  DubiDalilan da ka iya sawa a koma vegan diet

  Pattern of behaviour: Wato yanayin dabi’a. Yaro ko mutum mai fama da lalurar autism spectrum disorder zai iya kasancewa da takaitaccen dabi’a da interest, ma’ana suna da wasu ‘yan dalibi’u da su kawai suke yi a ko wani irin hali. Sannan kuma abubuwan da su ke aikatawa kuma za su rika maimaita su.  Dabi’un za su iya kasancewa ko wanne daga cikin wadannan abubuwa masu zuwa:

  1. Za su rika motsi (movement) wadda zai kasance suna maimaita irinsa, kamar rocking, ko juyawa ko tafi da hannu
  2. Su kan aikata abubuwa da ka iya cutar da su kamar cizon kansu, ko buga kansu haka nan
  3. Su kan koyi wani routine su doru akansa sannan da zaran an samu canji, ko da kadanne, su kan shiga matsanancin hali.
  4. Akasari basu iya coordination sannan su kanyi tafiya a banbarakwai haka, kamar tafiya akan yatsunsu da makamancin haka
  5. Su kan saka hankalinsu with keen interest idan su ka ga wani abu na juyawa kamar tayan motar wasan yara amma ba su iya gane dalilin wannan juyawan
  6. Su kan tsargu da haske ko wani kara amma za su iya ko in kula da zafi (pain) ko kuma canjin yanayi (temperature)
  7. Ba sa irin wasa da yara su ke yi suna magana dinnan, wato make believe play
  8. Su na iya dora hankalinsu da ganinsu akan wani abu ko wani abu da ake yi da tsaninin dora hankali
  9. Su kan zama masu zaben abinci sosai. Kamar cin wasu kalan abinci kawai kadan ko su ki tsani abinci mai wani texture.

  Idan suna girma, wasunsu su kan koyi hulda da mutane sannan alamomin cutar da wahalhalunsa su kan ragu. Idan aka yi sa’a wadanda su ke da lalurar, amma ba mai tsanani ba, su kan koma su yi rayuwarsu kusan kamar normal mutane. Amma wasun kuma haka za su ta fama da wannan lalura. A lokacin shekaran balaga abu ya fi tsanani.

  Lalurai daban-daban da suke kan autism spectrum disorders?

  1. Asperger’s syndrome: Wannan ya fi ko wanne sauki a cikin wadannan jerin lulura na autism spectrum disorders. Mai wannan lalura kan iya kasancewa mai kaifin basira sai dai kuma su kan yi fama da wahalar hulda da mutane.
  2. Pervasive developmental disorder not otherwise specified (PDD-NOS): Ita wannan cutar tafi Asperger’s syndrome tsanani kadan amma kuma ba ta kai sauran ba.
  3. Autistic disorder: Autistic disorder ya fi su Asperger’s syndrome da PDD-NOS tsanani. Amma duk alamominsu iri daya ne.
  4. Childhood disintegrative disorder: Wannan ta fi duk cututtuka da muka lissafa a baya tsanani. Ita wannan cutar, za ka tarar yaro ya fara girma lafiya-lafiya kawai kwatsam sai yaro ya rasa duk dan abinda ya koya na magana ko hulda da kuma yadda kwakwalwansa ke aiki. Hakan na faruwa ne tsakanin wata shida na haihuwan yaro zuwa shekara biyu ko hudu.

  Domin karin bayani, ku duba wannan makala cikin harshen Turanci

  Yadda ake gano mutum na kan autism spectrum (diagnosis)

  Yawanci likitoci suna dogara ne da kula da dabi’unsu da kuma development na su domin hakikance lamarin. Yawanci wannan cuta ana iya gano shi ne akalla idan yaro ya shekra biyu.

  Yana da kyau duk wanda ya lura da yaronsa na nuna alamomin da aka ambato dinnan to ya yi maza ya je wajen likita domin a fara bincikawa. Bincike da ganon wannan lalura da wuri yana taimakawa kwarai ga rayuwan  yaro da na ma iyaye ko kuma ma su kula da yaro.

  Sannan bincike da gwajin babban mutum, don gano ko yana da wannan cutar, ya fi wuya fiye da yaro, saboda babba zai iya kasancewa yana da wasu mental health issues.

  Ana bin matakai da dama tare da likitoci da suka kware akan abubuwa daban-daban wajen gano ko yaro na kan autism spectrum disorder. Domin karanta cikakken bayanin hanyoyin da ake bi, dubi wannan makala da National Institute of Mental Health su ka rubuta.

  Dalilan da ke kawo autism spectrum disorder

  Duk da cewa masana sun kasa cewa lallai ga takamammen abinda ke kawo autism spectrum disorder, amma bincike na nuni da gado da kuma wuri wato environment akan suna taka muhimmayar rawa wajen taimakawa ga samuwar wannan lalaurar. Alal hakika har yanzu masana sun gagara su gano dalilan da ke sa wasu su ke kamuwa da wannan lalura sannan wasu kuma ba su kamuwa da shi. Amma sun yi Imani wadannan dalililai, da zamu ambato a kasa, suna daga cikin risk factors, ga dalilan kamar haka:

  1. Idan mutum na da dan uwa (sibling) mai dauke da wannan lalura
  2. Iyaye tsofaffi
  3. Idan mutun na da wasu genetic condition (yanayin gado). Yanayi kamar su down syndrome, da fragile X syndrome, da Rett syndrome suna jefa mutum high risk na autism spectrum disorder
  4. Yaro da aka haifa dan mitsitsi mara nauyi (very low birth weight)

  Ko akwai hanyoyin kariya daga haihuwan yaro mai autism spectrum disorder?

  Kamar yadda muka fada a baya, likitoci ba su da hakikanin sani lalle-lalle ga dalilian da ke kawo lalurar autism, amma dai sun yi imani da cewa gado na taka muhimmayar rawa sosai da sosai.

  Sannan likitocin sun ce, wani lokaci idan uwa ta zama exposed to wasu chemicals lokacin tana dauke da ciki, ana iya haihuwar yaro da mushkila, amma hakan ba ya faruwa sosai sam. Amma kuma likitoci ba sa iya sanin cewa uwa zata haifi da mai autism a lokacin da ta ke da ciki.

  Duk da shike uwa ba za ta iya hana Kanta haihuwan da mai autism ba, amma za ta iya kokarin ganin ta haifi da lafiyayye. Ga hanyoyin da za ta bi domin haihuwan lafiyayen da:

  Ku karanta: Hanyoyi biyar da za a bi don rage damuwa anxiety

  Rayuwan koshin lafiya (Live healthy): Ta hanya cin abinci mai balanced diet, da motsa jiki, da kuma zuwa wajen likita akai-akai domin duba lafiyarta da na danta.

  Kar ta sha wani magani da ba likita ne ya rubuta mata ba: Duk wani maganin da mace za ta sha idan tana da ciki ya kansance ya zo ne daga kwararen likita, musamman maganin anti-seizure. 

  Barin shan giya kwata-kwata: Idan mace na da ciki, likitoci sun yi gargadi da babban murya a kan lalle mace ta kiyayi shan giya ko da kuwa ba mai yawa ba ne.

  Neman magani idan uwa tana da existing health condition: Idan uwa na da wani rashin lafiya ta yi kokarin maganinsa domin kare danta. Idan uwa na da cutuka kamar su celiac disease  ko PKU ta tababatar ta na bin dokan likita domin kula da cuta yadda ya kamata.

  Yin rigakafi da su ka kamata, kamar su German measles (rubella) da sauransu

  Shawarwari ga iyaye na yadda za su tafiya da yaro da ke kan autism spectrum disorder

  Sanin kowa ne cutar autism cuta ne mai wuyan sha’ani ga mai fama da ita harma ga iyaye da su ke kula da yaron. Sannan iyaye suna taka rawa a nasarar ko rashin nasarar rayuwan ‘yan’yansu, to haka abin ya ke ga iyaye masu fama da mai lalurar autism. Ga shawarwarin, kamar haka:

  A mai da hankali akan positive things: Sabo da wahalhalu da ke tare da jinya da kula da mai autism, ba wuya uwa ko uba su shiga kunci, kuma wannan kunci ba zai taimaki kowa ba. Kasancewar iyaye cikin farin ciki zai sa su yi hakuri wajen taimakawa irin wadannan yara. Kuma su masu autism spectrum disorder sun fi koyo ko cimma abinda ake so su cimma idan ana cikin yanayi mai kyau, wato positive environment.

  A samu wani abu da aka dora su akai kuma a jajirce akan bin yadda aka tsara (Stay consistent and on schedule): Su masu wannan lalura sun fi yin aiki da suka saba da shi kuma akanyi a lokaci guda a kullum misali idan ana karatu karfe tara ne a kullum to sun fi son kullum a rika yin shi da karfe taran ba canji. Nv ,00

  A saka wasa a cikin ayyukansu na kullum. Ya kasance a kullum an ware musu lokacin wasa wadda ba karatu ne ba.

  Kar ya zamana an karaya. Saboda irin wahala da renon irin wannan yara su ke da shi, sai ka tarar   wani lokaci iyaye sun gaji da gwada wani dabara kula da su da za a gaya musu. Iyaye su daure ba a san dabaran da zai yi aiki ba.

  Za ku iya karanta: Tambayoyi da amsoshi 10 game da cutar coronavirus

  A rika fita da su. Kar a ce za a rika barinsu a gida a kokarin kare su domin wani lokacin za ka tarar iyaye ba su son fita da su ne, saboda yanayin jikinsu sukan shiga halin da ba mai dadi ba a cikin mutane. Idan za a je dan sayayya haka ko dan wani waje da ba dadewa za a yi ba a rika kokarin fita da su wannan zai taimaka musu su saba da yanayin mutane.

  References

  National Institute of Mental Health (March 2018). Autism Spectrum Disorder. Retrieved from

  https://www.nimh.nih.gov/health/topics/autism-spectrum-disorders-asd/index.shtml

  Mayo Clinic (n.d). Autism Spectrum Disorder https://www.mayoclinic.org/diseases-conditions/autism-spectrum-disorder/symptoms-causes/syc-20352928

  WebMD (n.d) What Are the Types of Autism Spectrum Disorders?

  https://www.webmd.com/brain/autism/autism-spectrum-disorders

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake gashin kifi karfasa

  Posted Jul 12

  Gasashshen kifi karfasa ko grilled fish ko kuma grilled tilapia abinci ne da mutane da yawa suke so kuma suke sha’awar koyon yadda ake sarrafawa. Saboda haka Umyuman ta koyar da yadda ake gashin kifi a cikin recipes da ta koyar a lokacin Ramadan a cikin zaurenta n...

 • Bita ta musamman akan rubutun gajerun labarai: Rana ta biyu

  Posted Jul 12

  Ku latsa nan don karanta darasin ranar farko. DARASI NA 1 Abubuwan lura a rubutun gajeren labari A jiya mun bayyana siffar gajeren labari ta fuskar adadin kalmomi. Mun riga mun san cewar shi Rubutu baiwa ne. Ba kowa ke da baiwar rubutu ba. Duk da haka akwai hanyoyin ...

 • Ko Ruwa Na Gama Ba Ki: Babi na Biyar

  Posted Jul 12

  Ku latsa nan don karanta babi na hudu. Gabaɗaya Asabe da Malam Amadu sun kasa kunne suna jiran Jummai da ke zaune a gabansu, ta faɗa musu wanda ya yi mata ciki, sakamakon tsawon lokacin da ta ɗauka tana ɓoye musu. Kan Jummai na ƙasa ta ce, "Habeeb ne". kusan duk ba s...

 • Physics: Darasi game da energy da kuma work 

  Posted Jul 8

  A wannan makala zamu yi bayani ne akan ENERGY da kuma WORK. Game da wannan darasi abubuwan da ake so dalibai su lura da su sune, energy, work, types of energy, sources of energy, classification of sources of energy, law of conservation of energy da mathematical problems...

 • Tekun Labarai: Idan Farauta ta Ki Ka

  Posted Jul 8

  Ku latsa nan don karanta farkon labarin. Ka sani ya kai Sarkin zamani, an yi wani bafatake mai nasibi a harkar saye da sayarwa, duk abin da ya kama sai ya yi daraja. Akwai lokacin da dirhami ɗaya ke jawo masa ribar dirhami hamsin. A kwana a tashi sai kasuwancin ya juya...

View All