Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Harshe da Adabi » Bita ta musamman akan rubutun gajerun labarai: Rana ta farko

Bita ta musamman akan rubutun gajerun labarai: Rana ta farko

 • Bakandandamiya tare da hadin kan group din MARUBUTA ta shirya bita ta musamman akan rubutun gajerun labarai, wanda marubucin littafin TEKUN LABARAI, Danladi Z. Haruna, ya gabatar daga ranar 15 – 20 ga watan Yuni, 2020.

  Ku latsa nan don karanta cikakken bayani game da hadafi da kuma maudu'an bitar.

  Don ganin cewa mutane sun kara amfanuwa da wannan bita mai ilmantarwa, Bakandamiya ta hada bitar wuri guda a cikin makala kamar haka:

  RANA TA FARKO: DARASI NA 1 

  Gabatarwa

  Rubutun gajeren labari na bukatar kaifafa tunani tare da dunkule ma'ana ta hanya mai sauki da mai karatu zai fahimta. Kuma daga irin yadda ka aiwatar da gajeren labari ne ake tsammanin zai kayatar ko akasin haka ga labarin littafi. Don haka abu ne mai kyau kwarai ka nakalci yadda ake rubuta gajeren labari mai ma'ana.

  Idan aka ce gajeren labari, ana nufin duk wani labari da yake da farko tsakiya da karshe amma yawan adadin kalmominsa ba su kai ya zama littafi sukutum guda ba. Yawanci littafin labari na Hausa yana farawa daga shafuka 80 zuwa sama. Don haka za mu iya daukar duk labarin da tsawonsa bai kai shafi 80 ba, a matsayin gajeren labari.

  Sai dai gajerun labarun da ake bukata domin shiga gasa, an karkasa su zuwa rukuni kamar haka:

  A Gargajiyance (Traditional): kalmomi 1,500-5000
  Takaitaccen labari (Flash Fiction): Kalmomi 500-1,000 words
  Gajeriyar Tatsuniya (Micro Fiction): Kalmomi 50 - 500.

  Mafi yawa an fi saka gasa akan kalmomi 1000 zuwa 3000. Don haka wajibi ne marubuci ya tsara labarinsa daga farko har karshe ba tare da ya tsallake adadin kalmomin da ake bukata ba. Idan aka samu gazawa ko zarcewar haka, yana jawowa a cire labarin komai dadi ko ma'anar da yayi.

  DARASI NA 2

  Abin tambaya, shin ta yaya za mu iya gane labarinmu ya kai adadin kalmomin da ake bukata?

  Wannan tambaya ce mai muhimmanci, domin da irin rubutun da muke yi ne ake auna yawan kalmomin da muka rubuta. Na'urar kwamfuta da wayoyinmu na Android da Apples, suna da manhajar yin rubutu wadda ke kirga duk kalmar da muka rubuta. Hakan na yiwuwa ne wajen kirga adadin tazarar kalmomin da muka bayar watau space.

  A bisa wannan ma'auni, idan muka rubuta kalmar 'Abinda' ba daidai take da 'abin da' ba. Domin ta farko kalma daya ce a hade, ta biyu kuma kalmomi biyu ne a rarrabe.

  Kenan wajibi ne mu san dokokin rubutu musamman na hadewa da rabewa. Wannan ne zai ba mu adadin kalmomin da muke bukata ba tare da alkalai sun ci gyaranmu ba.

  Kaidojin rubutu suna da matukar muhimmanci wajen fayyace azancin labari. Don haka alkalai ke ware maki na musamman ga duk labarin da ya cika ka'idojin rubutu sosai.

  Sashen Hausa na BBC ya maida hankali sosai wajen cika ka'idojin rubutu. Kuma ba kasafai suke kula rubutun da bai cika ka'idoji sosai ba musamman rubutun da aka yi watsi da kalmomin hadewa da rabawa.

  Amfanin Kaidojin Rubutu

  Daya daga amfanin ka'idojin rubutun Hausa shi ne isar da sako kamar yadda kake buri a cikin ranka. Domin akwai kalmomi da haɗe su ko rabe su ke jawo wata fassarar ma'ana ta daban. Matukar ka nakalci yadda ake rubuta kalma, to wajibi ne kuma ka gane cewar raba ta zai ba da karuwar adadin kalmomi kuma hade ta zai kawo raguwar adadin kalmomi har ma da ma'ana.

  Za mu kawo misalin yadda hadewa da rabewar kalma ke sauya ma'anar jumla.

  DARASI NA 3

  Bari mu dauki misali.

  Malam Faruk Lawan Da'u ya kawo misalin wasu jumloli da yadda hadewa da rabewa ya jawo sauya ma'anarsu da kuma adadinsu.

  Yi nazarin wadannan jumloli a tsanake ka fada mana abin da kowacce jumla ke nufi da kuma abin da ya bambanta ta da sauran:

  1. Ta je fadama
  2. Ta jefa dama
  3. Taje fa dama
  4. Ta je fa da ma
  5. Tajefa dama
  6. Ta je fada ma
  7. Taje fadama
  8. Taje fada ma
  9. Ta jefada ma
  10. Tajefa da ma

  Ina so dalibai a yi nazarin wadannan jumloli a fayyace mana abubuwa kamar haka:

  a. Wadanne ne jumloli masu ma'ana. Wadanne ne marasa ma'ana?

  b. A cikin jumloli masu ma'ana da aka kawo a sama, me kowacce ke nufi?

  c. Kalmomi nawa ne a cikin kowacce jumla mai ma'ana?

  A RUBUTA AMSAR A KASA CIKIN MINTI 10

  DARASI NA 4 - KAMMALAWA

  Idan aka yi kuskuren rubuta kalmar da ba ita ba ce, mai karatu zai yi maka fahimta baibai, kuma zai sauya ma'anar labarinka.

  Haka kuma a wajen dangantaka, yawancin kalmomin mallaka ana hade su ne domin nuna alaka tsakanin mamallaki da abin mallaka. Misali, idan ka rubuta 'Takalminka', za mu fahimci takalmin mallakin tauraron da ake magana da shi ne. Amma idan ka rubuta, 'Takalmin ka' sai mu yi tsammanin cewar takalmin ne ya aikata wani abu wanda gaba daya ya sauya ma'anar zancen da ake yi.

  Kafin mu yi sallama bari mu bayar da aikin gida.

  Kowanne daga mahalarta wannan bita ya rubuto mana gajeren labari mai dauke da kalmomi 150 - 250.

  Labarin ya kasance an lura da kaidojin rubutu musamman hadewa da rabewa. Sannan a ya zamana yana da mafari... Kada a damu koda bai kai karshe ba. Domin mafarin labari shi ne babban abin da ke rike makaranci har zuwa karshe.

  Kenan labarin da za a turo zai iya kasancewa tsakure ne daga wani labarin. Duk wanda zai aiko sai ya wallafa a wannan zaure. Wanda ya aiko da nasa zai samu maki, wanda da shi za a yi amfani waje bada satifiket.

  Idan akwai tambaya sai a yi karkashin kowanne post din da tambayar ta taso.

  Zan saka audio na wannan bita ta yau domin a sauke a ji idan ana bukata

  Wasallamu Alaikum 

  Danladi Z. Haruna

  Ku latsa nan don cigaba da karanta darsin rana ta biyu. Sannan za ku iya ziyartar zauren MARUBUTA dake taskar Bakandamiya don bibiyar bitar baki daya.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta shafi na 12 da 13. SHAFI NA 14 Tana isowa ta dubi Mama tare da mika mata wayar "Ga mamansu Sumayya za kuyi magana." Mama ta amshi wayar ta saka akunne ta na fadin salamu alaikum jin shiru yasa ta dubi fuskar wayar tare da fadin "La kinga ta katse." Fati ta amshi wayar ta...
 • Zamantakewar aure, zamantakewa ce mai wahala, matuƙar wahala kuwa. Sai dai da zarar ka fahimci tana da wahalar, sai ta zama mai sauƙi a gare ka. Domin fahimtar tana da wahalar shi zai ba ka damar neman iliminta. Shi kuma iliminta sai ya ba ka damar samun sauƙin ta. A shirinshi da ya saba gabatarwa ...
 • Wed at 1:17 AM
  Posted by Bakandamiya
  An haifi Olufela Olusegun Oludotun Ransome-Kuti a ranar Asabar 15-10-1938, a Abekuta ta jihar Ogun. Iyayensa manyan mutane ne domin Mahaifiyarsa Fummilayo Ransome-Kuti, 'yar gwagwarmaya ce, mai fafutukar kwato 'yancin mata. Mahaifinsa Isra'el Olodotun Ransome-Kuti, babban limamin coci ne, shugaban ...
 • Idan aka ce Hepatitis, to ana nufin ciwon hanta kenan a Hausance. Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta na...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Dogaro Ga Allah Jari. Cikin ƙasashen Mongol an yi wani babban Sarki mai yawan jarumai ana kiran sa Bihikatu. Shi wannan Sarki jarumi ne amma mugu ne na ƙin ƙarawa. Tun da yake bai taɓa yin afuwa ga wanda ya saɓa masa ba. Ba a taɓa ganin dariyarsa ba s...
 • Da sunan sarki rabbana mai duniya Al-kaliƙu wanda ya yo duniya Ya yi ƙorama har da teku na maliya Al-maliku kai ke mulkin duka duniya Sunanka ne farkon faɗi kowace safiya Kuma kai nake kira da yamma sakaliya. Na yi yabo gurin Annabi Muhammadu Da ya fi kowa bauta Annabi Hamidu Ma'aikin Allah Sahibin...
View All