Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake gashin tsokar kaza da kifi

Yadda ake gashin tsokar kaza da kifi

 • Wannan gashin tsokar kaza ko gashin tsokar kifi wato fish fillet, mun koyar ne a shirin girke-girkenmu na Ramadan wadda aka gabatar anan Bakandamiya a zauren, Free Ramadhan Classes with Umyuman.


  Abubuwan hadawa

  1. Tsokar naman kaza ko tsokar kifi
  2. Kayan kamshi (habbatussauda, busashshiyar na’a-na’a, garin thyme, da maggi)
  3. Mai

  Yadda ake hadawa

  1 Idan ki ka bi yadda muka koyar da gashin tsokan sa, za ki iya amfani da wannan tsarin domin gashin tsokar kaza, da kuma tsokar kifinki!

  2. Kaman yadda ki ka gani a hotunan na farko naman kirjin kaza ne, wato tsoka zalla. Za ki wanke ki shafe da kayan kamshi ki gasa shi a frying pan (abin tuyan kwai).

  Hoton gasashshen tsokar kaza zalla

  3. Hakanan hoto na biyu shi kuma zallar tsokar kifi ne, wanda turawa ke kira da fish fillet! Ana samunsa a manyan shagunan saida kayan abinci da namomi.

  Hoton gasashshen tsokar kifi (fish fillet)

  4. Idan ki ka sami fish fillet shima shafe shi za ki yi da kayan kamshi sannan a gasa yadda muka koyar a post dinmu na gashin tsokar sa!

  5. Illa kawai banbanci zai zama naman sa zai fi naman kaza jimawa a wuta haka naman kaza zai fi tsokar kifi jimawa a wuta!

  Misali:

  Mu ce namar sa 20mins
  Naman kaza 15mins
  Tsokar kifi 10mins

  Muna sa ran duk wacce ta gwada girkinmu za ta yi sharing hotunan girkin da mu, wannan shi zai bamu kwarin gwuiwar kawo muku girke-girke daban-daban a kullum. Muna godiya da kulawarku.

  Za ku iya duba daruruwan girke-girke da muka koyar a baya, kamar su, yadda ake appetizer salad da su yadda ake gashin kifi karfasa. Idan kuma kuna neman wannan girki ne daban to bincika ta hanyar butawa a search box namu.

  Rubutawa: Shaima Alhussainy

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Thu at 7:22 PM
  Posted by Bakandamiya
  Ku latsa nan don karanta babi na bakwai. Bata iya komawa bacci ba tunda ta tashi daga wannan mafarkin. Ta yi kuka har sai da idanunta suka fara yi mata zafi, gangar jikinta da zuciyarta suna yi mata rad'ad'in da ita kad'ai ta san yanda take ji. Ƙirar sallahr asuba yasa ta mik'e cikin hanzari, tana...
 • Mece ce cutar mantuwa (amnesia)? Idan aka ce mutum na fama da cutar amnesia dai to ana nufin cutar da ke sa mutum ya manta abubuwa kamar abubuwan da su ke zahiri, da kuma bayanai game da wani abu ko kuma manta abinda ya faru da su da makamanta ire-iren wannan mantuwa. Mutane da su ke dauke da wanna...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Saurin Fushi Na Kawo Da Na Sani. A wani ƙauye akwai wani mutum  ana kiran sa Abu Sabiru, ya kasance mai tsananin haƙuri da kawar da kai akan wasu al’amura. Dalilin da ya sa ma ake kiransa Abu Sabiru kenan. Yana zaune tare da matarsa kyakkyawar gaske ...
 • Ku latsa nan don karanta darasin rana ta uku. DARASI NA 1 Matakan rubutun gajeren labari A jiya mun yi bayani akan matakan da ake bi wajen tsara labari, yau kuma za mu bayani a takaice kan matakan da ake bi wajen rubuta ingantaccen labari. Waɗannan matakai ba tabbatattu ba ne, ma'ana ba wajibi ne...
 • Ku latsa nan don karanta babi na shida. Habeeb na kwance a kan doguwar kujera ya ji an murɗa handle ɗin ɗakinshi tare da turo ƙofar a hankali. A hankali ya buɗe idanunsa da suka yi nauyi sakamakon ciwon kan da yake fama da shi. "Fateemah" ya faɗa a ransa, lokacin da ya kai duba ga Jummai da ke ts...
 • Uwargida ba za ki yi dana sanin koyan yadda ake yoghurt in fruits ba. Domin kuwa kayan dadi ne sosai da sosai kuma cikin mituna kalilan za ki hada. Ba a ba yaro mai kiwiya!!! Wannan recipe yana daya daga cikin recipes da muka koyar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman a nan Bakandamiya. Abu...
View All