Rubutu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake hadin shinkafa ta musamman

Yadda ake hadin shinkafa ta musamman

 • Kowa ya san ana dafa shinkafa ta hanya daba-daban, kamar su fried rice, da su jollof rice, da su rice and stew ga sunan dai barkatai, amma wannan dafuwar shinkafar ta musamman ce wadda duk wanda ya saka ta a baki zai manta inda ya ke. Uwargida da amarya kar ku bari a baku labari!  Sai angwada akan san na kwarai!

  Wannan hadin shinkafa ta musammam an koyar da ita ne lokacin shirin girke-girkenmu na Ramadan a cikin zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman.

  Abubuwan hadawa

  1. Shinkafa
  2. Kayan kamshi
  3. kwai
  4. Albasa mai lawashi
  5. Koriyar tattasai
  6. Peas
  7. Karas
  8. Albasa
  9. Bay leaves
  10. Maggi da gishiri
  11. Man gyada
  12. Nikakkiyar nama
  13. Curry

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki fara dafa shinkafarki da curry ki ajiye a gefe.

  Hoton dafaffen shinkafan

  2. Ki kada kwai ki soya ki dagargaza ki ajiye a gefe.

   

  Hoton dafaffen kwai

  3. Sai ki daura mai ki kawo albasa mai lawashi ki zuba da koriyar tattasai da nikakkiyar nama da maggi da kayan kamshi ki soye duka ki sa kayan lambunki duka.

  Hoton dakakkiyar nama da sauran kayan lambu da kayan kamshi ina soyawa

  4. Sannan sai ki dauko dafaffiyar shinkafa ki sa a ciki ki cakude ko ina yaji sai ki kawo kwan ki zuba ki rufe ki bari ya turara

   

  Komai ya hadu anan, sai ci!

  Mai karatu na iya duba girke-girkenmu na baya kamar su Yadda ake gashin tsokar kaza da kifi da Yadda ake hadin lemun kankana da abarba da makamantansu duk anan cikin Bakandamiya

  Rubutawa: Shaima Alhussainy

Comments

0 comments