Makalu

Blogs » Addini da Tarbiyya » Bayani kan hukuncin haduwar Idi da Jumma'a a rana daya

Bayani kan hukuncin haduwar Idi da Jumma'a a rana daya

 • Bismillahi rahmanir Rahim

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya.

  Lalle haduwar Idi da Jumma’a wani abu ne da ya saba faruwa lokaci zuwa lokaci. Hakan ya taba faruwa a zamanin Manzon Allah (S.A.W) da zamanin shabbai da tabi'ai.

  Babu sabani tsakanin malamai kan cewa duk wanda Jumma'a take wajaba akansa idan bai samu yin sallar Idi ba, to wajibi ya halarci sallar Jumma'a. Haka nan babu sabani kan halaccin yin sallar jumma'a ga wanda ya halarci sallar Idi.

  Mafi yawa cikin malaman mazhabobi guda hudu sun tafi akan cewa wajibi ne liman ya halarci sallar juma'a. Amma malamai sun yi sabani kan idan Idi da Jumma'a suka hadu rana daya, shin Jumma'a ta wajaba akan wanda ya halarcin sallar Idi?

  KAULI NA FARKO

  Sallar Jumma'a tana faduwa idan mutum ya haraci sallar Idi, sai ga liman kadai; ya wajaba ga liman ya halarci sallar Jumma'a, saboda ya jagoranci wadanda suka zo sallah. Wannan shine kaulin Hanabila.

  Dalilin wannan kaulin

  Sun kafa hujja da dalilai masu yawa:

  1. Daga Zaid Bn Arqam (R.A) Lalle Mu'awuya Bn Abi Sufyan ya tambaye shi: Shin ka riski Idi biyu da suka hadu rana daya tare da Manzon Allah (S.A.W)? Sai ya ce: Eh. Sai Mu'awuya yace: Toh ya ya aikata? Sai Zaidu ya ce: Ya yi Sallar Idi, sannan ya rangwanta halartar Jumma'a, kuma ya ce: "Duk wanda ya so, ya sallace ta (wato Jumma'a)". Imam Ahmad da Nasa'i da Ibn Majah da Darimi da Hakim ne suka rawaito wannan hadisi.

  2. Daga Abu Huraira (R.A), daga Manzon Allah (S.A.W) yace: "Hakika a wannan yinin naku Idi biyu sun hadu a cikinsa, wanda ya so (Idin farko) ya isar masa halartar sallar Jummu'a. Amma mu zamu yi Jumma'a". Hakim da Abu Dawud da Ibn Majah ne suka rawaito shi. Kuma Hakim da Albani sun inganta shi.

  3. Daga Abdullahi bin Umar (R.A) yace: "Idi biyu sun hadu a zamanin Manzon Allah (S.A.W), sai yayi sallah da mutane, sannan yace: "Wanda ya ga dama ya halarci sallar Jumma'a, to ya halarta, wanda kuma ya ga daman kin zuwa, to kada ya halarta". Ibn Majah ne ya rawaito shi.

  Imam Tabarani ya rawaito wannan hadisin da wani lafazi, daga Ibn Umar (R.A) ya ce: "Idi biyu sun hadu a zamanin Manzon Allah (S.A.W) a ranar karamar sallah, da kuma Jumma'a, sai Manzon Allah (S.A.W) ya yi sallar Idi tare da mutane, sannan ya fuskanto su yace: "Ya ku mutane! Lallai ne kun sami alheri da kuma lada, kuma lallai ne mu zamu yi Jumma'a, wanda ya so zai yi jumma'a tare da mu to ya yi, wanda kuma yake ganin zai koma ga iyalansa,  to ya koma".

  KAULI NA BIYU

  Sallar Jumma'a bata faduwa ga wanda ya yi sallar Idi daga mutanen birni, amma tana faduwa ga mutane kauye. Wannan shine kaulin Shafi'iyya.

  Dalilinsu na wannan kauli

  Sun kafa hujja ne da hadisin da Abu Ubaid (R.A) ya rawaito, ya ce: "Na halarci Idi tare da Usman bin Affan (R.A), inda ya kasance ranar Jumma'a ne, sai ya yi sallah kafin khuduba, sannan ya yi khuduba, sai ya ce: "Ya ku mutane! Lallai wannan yini ne da aka hada muku Idi biyu acikinsa, duk wanda ya so ya jira Jummu'a daga cikin mutanen Awali (kauyen Madinah), to ya jira, duk wanda kuma yake son ya koma; to na bashi izini". Bukhari ne ya rawaito wannan hadisi.

  Suka ce: Izini da Usman (R.A) ya baiwa mutanen kauye na kar su halarci sallar Jumma'a in sun so, dalili ne da yake nuna bai yiwa mutanen birni izini ba, saboda haka wajibi mutanen birni su halarci sallar Jumma'a.

  KAULI NA UKU

  Sallar Jumma'a bata faduwa ga wanda ya halarci sallar Idi ga duk mutanen birni da na kauye. Ma'ana wajibi ne halartar sallar Jumma'a ga duk wanda Jumma'a take wajaba akan sa, ko da kuwa ya halarci sallar Idi. Wannan shine kaulin Hanafiyya da Malikiyya.

  Dalilinsu

  Sun kafa hujja da dalilai kamar haka:

  1. Fadin Allah madaukakin sarki: “Ya ku wadanda suka yi imani! Idan an yi kira zuwa ga sallah a ranar Jumma'a, sai ku tafi zuwa ga ambaton Allah (wato sallar Jumma'a)". Suratul Jumu'ah, aya ta 9. Suka ce wannan umurni ne a bayyane ga duk wanda Jumma'a ta wajaba akan sa.

  2. Suka ce: Sallar Idi sunnah ce a wurin mafi yawan maluma, ita kuma sallar Jumma'a wajiba ce. Don haka a ka'ida: wajibi baya faduwa don an yi sunnah. Saboda haka sallar Jumma'a bata faduwa don an yi sallar Idi.

  3. Suka ce: kamar yadda sallar azahar bata faduwa idan Idi ya dace da sauran ranakun mako, to haka ma in Idi ya dace da ranar Jumma'a, ba zai sa Jumma'a ta fadi ba.

  KAULI NA HUDU

  Idi idan ya dace da ranar Jumma'a, to Jumma'a ta fadi ga wanda ya halarci sallar Idi, haka ma sallar azahar na wannan ranar. Sai ya zama sallar la'asar kawai za'a yi. Wannan kaulin Ada'u bn Abi Rabah.

  Dalilin wannan kauli

  Dalilin wannan kauli shi ne abinda Ada'u bn Abi Rabah ya rawaito, ya ce: "Abdullahi bin Zubair ya yi mana sallar Idi ranan Jmumu'a da hantsi, sai muka zo yin sallar Jummu'a, sai ya ki fitowa, sai muka yi sallar mu mukadai. A lokacin Abdullahi bin Abbas (R.A) ya na Ta'if, da ya dawo sai muka bashi wannan labarin hakan. Sai ya ce: "Lallai (Abdullahi bin Zubair) ya dace da Sunnah". Abu Dawud da Ibn Majah ne suka rawaito wannan hadisi.

  A wani lafazin: Ada'u bn Abi Rabah ya ce: "Ranar Jumma'a ta hadu da ranar Idin karamar sallah a zamanin Ibn Zubair, sai ya ce: "Idi biyu sun hadu a rana daya". Sai ya hada su gaba daya, ya sallace su raka'a biyu da hantsi, bai kara akan su ba har sai ya yi La'asar".

  MAGANA MAFI RINJAYE

  Idan ranar Idi ta dace da ranar Jumma'a, to an yi rangwamen halartar sallar Jumma'a ga wanda ya halarci sallar Idi. Sai dai kuma halarta Jumma'a ga wanda ya halarci sallar Idi shi ne ya fi. Saboda Manzon Allah (tsira da aminci Allah su tabbata gare shi) ya yi rangwame, amma shi ya fita sallar Jumma'a. Idan kuma mutum ya yi aiki da rangwamen da aka yi na rashin halartar Jumma'a, to dole ya yi sallar Azahar a kan lokacin ta. Cewa sallar Azahar ta fadi, magana ce mai raunin gaske.

  Ibn Abdul-Barr yace: "Amma cewa sallar Jumma'a tana faduwa saboda Idi, kuma ba za a yi sallar Azahar ko Jumma'a ba, wannan batacciyar magana ce a fili, kuma kuskure ne karara, Magana ce abin yasarwa mai ita kayansa, sannan kuma zance ne abin kauracewa, ba a karkata gare shi…." Duba littafin At-Tamhid (10/401).

  Sheikh Ibn Bazz (Allah ya masa rahamah yace: "Idan Idi ya dace da ranar Jumma'a, ya halatta ga wanda ya halarci sallar Idi ya yi sallar Jumma'a, kuma (ya halatta) ya yi sallar Azahar, saboda abinda ya tabbata daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam akan wannan.

  Hakika ya tabbata daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam lalle ya yi rangwame ga wanda ya halarci Idi, yace: "Idi biyu sun hadu a wannan rana ta ku, duk wanda ya halarci Idi, to babu Jumma'a akansa". Sai dai ba zai bar sallar Azahar ba, abinda ya fi shi ne ya yi sallar Jumma'a tare da mutane, idan bai samu yin sallar Jumma'a ba, to sai ya yi sallar Azahar. Amma liman shi (dole ne ya halarta), zai yi sallar da wadanda suka halarci Jumma'a in sun kasance mutum uku zuwa sama, liman tare da su, idan babu wanda ya zo sai mutum daya, sai su yi sallar Azahar".

  A takaice dai duk wanda ya halarcin sallar Idi, to yana da zabi, ko ya haranci Jumma'a, ko kar ya halarta, saboda rangwamen da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi ga wanda ya halarci sallar Idi. Amma halartar Jumma'a shi ya fi rashin halarta. In kuma bai halarta ba, to dole ya yi sallar Azahar raka hudu. Wanda kuma bai halarci Idi ba dole ne ya halarci Jumma'a. Sannan kuma wajibi ne ga limamin Jumma'a ya halarci sallar Jumma'a, saboda ya jagoranci sallar ga wadanda basu samu zuwa Idi ba, da kuma wadanda suka je Jumma'a cikin wadanda suka halarci Idi.

  Kuna iya duba wannan makala da ta yi bayani akan hukunce-hukuncen layya.

  Muna rokon Allah ya nuna mana gaskiya, ya bamu ikon bi. Allah kuma ya karba mana ayyukan mu.

  Dr Kabiru Adamu Lamido Gora

Comments

0 comments