Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake red velvet cake

Yadda ake red velvet cake

 • Red velvet cake, cake ne da mutane da dama suke so kuma kuma suke son ci. Saboda haka, akwai hanyoyi daban-daban na yin red velvet cake, ga yadda na ke nawa cake din na kawo muku.

  Wannan yana daya daga cikin recipes da muka koyar lokacin Ramadan anan Bakandimya. Domin ganin duk jerin recipes din da a koyar a wannan zauren, ku ziyarci zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman.


  Abubuwan hadawa

  1. Flour 2cups
  2. Madara ta gari kofi 1 sai a dama da ruwa kofi 1 sannan a matsa lemon tsami rabi a ciki.
  3. A narkar da butter rabin kofi
  4. Sugar rabin kofi
  5. Baking powder cokali biyu
  6. Kwai guda biyu
  7. Coco powder (poda ce baqa me kalan bonbita) rabin kofi
  8. Jan kala (zaki yi ta zubawa har sai kin ga yayi jazur)

  Hoton abubuwan hadin cake din

  Yadda ake hadawa

  1. Za ki hade duka abubuwan da na lissafa a sama ki cakude su wuri guda ki tabbatar sun hade sossai kaman yadda za ki gani a hotonnan!

  Hodon hadin cake din

  2. Yana hadewa za ki samu abin gashin cake ki shafe sa tas da butter sannan sai ki zo ki zuba kwabin red velvet cake dinki a ciki ki saka a oven ki gasa na kimanin minti shabiyar a wuta madaidaici!

  Hoton kullun cake din

  3. Ki rika dubawa har sai  ya yi, ta yadda za ki gane ya yi shine ki sami tsinken tsokaci (tooth pick) ki tsikara a ciki ki ciro, inkinga ya fito tsaf ba tare da qullin cake a jikinsa ba to cake dinki ya yi!

  4. Abu na gaba shine za ki sami garin whipping cream (ana saidawa a kasuwa)
  Ki dibi kofi daya sai ki zuba masa madara mai sanyi kalau rabin kofi, in kina da mixer ki yi ta bugawa da shi in babu ki yi ta bugawa da hannunki za ki ga ya yi kauri ya yi fari tas, bayan cake dinki ya huce sai ki bi ki shafe shi tas da whipping cream dinki da ki ka kada ya yi kauri!

  5. Za ki iya yiwa cake dinki kwalliya ta diban burbudin cake din na ki ki watsa a samanshi!
  Zai bada armashi matuka, bai da wahalar yi!

  Zaku iya duba girke-girkenmu na baya da muka koyar kamar su, Yadda ake gashin hakarkari awazun rago da  yadda ake gashin tsokar kaza da kifi

  Rubutawa: Shaima Alhussainy

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta labarin Afuwa ƙwaya Ce, Ka Shuka Ɗaya Ka Girbi Goma. An yi wani attajiri da ke da dukiya mai yawan gaske, ana kiransa Abu Tammamu. Saboda yawan dukiyarsa, bai san iyakacin abin da ya mallaka na daga gidaje da gonaki da dabbobi da bayi da sauran kadarori ba. B...
 • Ku latsa nan don karanta shafi na 12 da 13. SHAFI NA 14 Tana isowa ta dubi Mama tare da mika mata wayar "Ga mamansu Sumayya za kuyi magana." Mama ta amshi wayar ta saka akunne ta na fadin salamu alaikum jin shiru yasa ta dubi fuskar wayar tare da fadin "La kinga ta katse." Fati ta amshi wayar ta...
 • Zamantakewar aure, zamantakewa ce mai wahala, matuƙar wahala kuwa. Sai dai da zarar ka fahimci tana da wahalar, sai ta zama mai sauƙi a gare ka. Domin fahimtar tana da wahalar shi zai ba ka damar neman iliminta. Shi kuma iliminta sai ya ba ka damar samun sauƙin ta. A shirinshi da ya saba gabatarwa ...
 • An haifi Olufela Olusegun Oludotun Ransome-Kuti a ranar Asabar 15-10-1938, a Abekuta ta jihar Ogun. Iyayensa manyan mutane ne domin Mahaifiyarsa Fummilayo Ransome-Kuti, 'yar gwagwarmaya ce, mai fafutukar kwato 'yancin mata. Mahaifinsa Isra'el Olodotun Ransome-Kuti, babban limamin coci ne, shugaban ...
 • Idan aka ce Hepatitis, to ana nufin ciwon hanta kenan a Hausance. Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta na...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Dogaro Ga Allah Jari. Cikin ƙasashen Mongol an yi wani babban Sarki mai yawan jarumai ana kiran sa Bihikatu. Shi wannan Sarki jarumi ne amma mugu ne na ƙin ƙarawa. Tun da yake bai taɓa yin afuwa ga wanda ya saɓa masa ba. Ba a taɓa ganin dariyarsa ba s...
View All