Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Harshe da Adabi » Bita ta musamman akan rubutun gajerun labarai: Rana ta hudu

Bita ta musamman akan rubutun gajerun labarai: Rana ta hudu

 • Ku latsa nan don karanta darasin rana ta uku.

  DARASI NA 1

  Matakan rubutun gajeren labari

  A jiya mun yi bayani akan matakan da ake bi wajen tsara labari, yau kuma za mu bayani a takaice kan matakan da ake bi wajen rubuta ingantaccen labari. Waɗannan matakai ba tabbatattu ba ne, ma'ana ba wajibi ne sai marubuci ya bi su ɗaya bayan ɗaya ba. Sai dai manyan marubuta irin su Jerry Jekkins, Robert Edward sa Sydney Sheldon suna ganin cewa labarin da aka rubuta ta hanyar bin matakan nan ya fi armashi da jan hankalin mai karatu.

  Haka kuma su waɗannan matakai dai suna dangantaka ne da irin lokaci da damar da marubuci ya samu kafin ya fitar da labarin ga jama'a. Wasu marubutan na fitar da matakai da yawa kafin su saki rubutunsu, wasu kuma suna takaitawa. Ga wasu daga matakan da na rairayo daga manyan marubuta:

  1. Tunani akan labarin da ake so a rubuta
  2. Tsara labari akan sikelin Five Finger Pitch
  3. Samar da ɗangogin labari watau Outline ko Index ko Flash card
  4. Gudanar da bincike
  5. Rubutu na farko
  6. Karantawa da yin gyare-gyare
  7. Mikawa masana ko abokai su duba labarin
  8. Sake yin gyara tare da tabbatar da sunayen taurari da wurare da kuma sarrafa kalmomi.
  9. Samar da taken da ya dace da labarin

  Za mu kara bayani tare da misalai.

  DARASI NA 2

  Ga bayanin yadda matakan suke

  1. Tunani akan labarin da ake so a rubuta

  Mun fada a baya cewa marubuci na iya samun fikirar labari daga irin labaran da aka ba shi ko ya gani ko ya yi mafarki. Yawanci kuma kungiyoyin da suke saka gasa suna fadin irin abinda za a yi rubutu akai. Misali yanzu haka gasar Aminiya da ke gudana, ana so ne a yi rubutu akan abin da ya shafi Dimokradiyya da Siyasar Nijeriya.

  To amma a gefe daya kuma gasar BBC ba a fadi takaimaiman abu daya da za a yi rubutu akansa ba. Don haka ya rage ga marubuci yayi tunani ga labarin da yake ganin zai kayatar ya rubuta.

  Ana so marubuci ya zama mai yawan karance-karance, domin daga karatuttukan da yake yi ne zai karu da hikimomin marubuta wajen saka labari.

  Idan misali ka yi nufin za ka shiga gasar Aminiya, yana da kyau ka yi bincike akan labarai da aka bayar dangane da siyasa. Da haka za ka samu fikirar da kake bukata.

  2. Tsara labari akan sikelin Five Finger Pitch

  Mun riga mun yi cikakken bayani kan wannan a jiya. Kowanne irin gajeren labari ka yi tunani za ka iya dora shi a wannan sikeli. Daga abinda ka fitar ne masu gasa suke gane irin armashin da labarin zai yi. Kowacce gasa kamar BBC da Aminiya suna bukatar a rubuta takaitaccen bayani dangane da labarin. To nufinsu ka rubuta five finger pitch ne ba tare da ka rubuta shi gida-gida ba. Misalin da na bayar na uku shi ake bukata.

  3. Samar da ɗangogin labari watau Outline ko Index ko Flash card ko Blocking

  Wannan na da matukar muhimmanci a kowanne irin rubutun labari walau dogo ko gajere ko na fim. Yawanci ma marubutan fim na Hausa suna iya daukar fim daga irin Outline ko Blocking tun kafin a rubuta shi. Da son samu ne da za mu dauki lokaci muna bayani akan wannan abu.

  Outline ko Blocking ko Index ko Treatment duk yana nufin abu daya, yana nufin ka rubuta irin yadda labarin da kake son rubutawa daki-daki. Daga abu kaza sai abu kaza. Wannan zai sa duk nukudar da ka dauka idan ka kakare ka ajiye ta ka dauki wata. Daga baya sai ka dawo ka kulla can inda ka kakare.

  A misalan da muka bayar jiya, mun kawo misalin labarin wata bazawara wadda aka bar mata 'yaya da take fafutukar kula da tarbiyyar su. Bari mu yi Outline din labarinta domin sake fahimta sosai.

  A. Mutuwar Malam Ibrahim mijin Atika da irin damuwar da ta shiga

  B. Irin ɗawainiyar da take sha wajen neman taimakon yan'uwan mijinta amma sun juya mata baya.

  C. Ta soma aikin koyarwa a Firaibet amma shugaban makarantar na yi mata kyarkyara.

  D. Ta nemi agajin wani mai hali daga makwabta shi ma ya zo mata da zancen da bata yarda da shi ba.

  E. Ta samu labarin kokarin da yan'uwan mijinta ke yi na cefanar da wasu kadarorinsa na kauye. Ta tafi neman taimakon hukumomi da kungiyoyin agaji.

  F. An samu masu tsaya mata wajen kwato hakkokin mijin da ke hannun yanuwansa. Kasancewar sa maaikacin gwamnati, akwai wasu hakkoki da suka kamata. Kungiyoyin sun shige mata gaba an danka komai a hannunta domin sunanta ne a jikin takardunta.

  G. Ta samu kudaden da suka ishe ta jari. Ta bude makarantar yara da koyar da sana'oi ga matan aure.

  DARASI NA 3

  Daga wadannan za ku ga abubuwan na tafiya daki-daki. Duk nukudar da ta kakare maka, sai kurum ka sake ta ka kama ta gaba. In ka so ma kana iya fara rubutunka daga nukudar karshe.

  4. Gudanar da bincike

  Bincike abu ne mai amfani sosai saboda zai sa ka rubuta abin da yake a zahiri haka yake. A littatafan Sidney Sheldon muna ganin yadda yake wassafa abu kamar dai iyakar kurewar masani ne a fannin. Ba komai ba ne illa bincike.

  Ga wani karamin misali na yadda marubucin wannan labari ya nuna irib harin da kada take illata mutum.

  •••••••
  Naji wani irin gurnani mai ban tsoro da kuma motsin ruwa mai karfu daga cikin, na dubi wajen a razane, ruwan ne ke wani irin bori a daidai inda Alhaji Sani yake, da kuma wani irin huci mai ban tsoron gaske. Da fari nayi tsammanin duk aikin ne yasa haka, amma dana kara dubawa sosai sai na sake tunani. Wani irin murgujejen kada ne ke juyi a wajen yana kada jelarsa wadda tasa ruwan ke wani irin bori. Ni dai ina rike da igiya bansan abinda ke faruwa ba, jira kawai nake naji an girgizata naja. A daidai lokacin Alhaji Sani ya sake dagowa sama, wannan karon yana mai kurma ihu da karajin neman taimako.

  Shehu ka ceci rayuwata, zan mutu! Kada ya cijeni a kafa zai kasheni ka taimake ni.Nan da nan naji hankalina ya tashi, tsorona ya karu fiye da da. Ba shiri na soma jan igiyar iyakar karfina. Wayyo Allah, rashin sani, ashe tuni kullin igiyar ya warware daga hannun nasa, ni dai bansan yadda haka ta faru ba. Saboda fisgar igiyar da nayi da karfi alhali babu komai a tare da ita nayi baya taga – taga, nayi karo da wani dutse na fadi da baya. Keyata bugu da dutse da karfi har sai da naji numfashina ya soma daukewa. Nayi ta maza na mike tsaye.

  Kadon nan ya tsare hanyar da Alhaji Sani zai fita yana wani irin huci mai firgitarwa. Alhaji Sani yayi ninkaya zuwa wani dan guntun dutse cikin tafkin ya kwanta. Lokaci – lokaci sai kadon ya waigo inda nake kamar yana son far mini, ni kuwa ganin haka sai na kara ja da baya, gaba daya makoshina ya bushe magana ma ta gagare ni. Cikin numfarfashi da alamun jin jiki Alhaji Sani yayi min magana, koda yake bana iya jin duk abinda yake fada, amma na fahimci yana jan kunnena da na yi hankali da wannan kadon. Kusan minti talatin babu wani mai katabus, yayin da Alhaji ke ta faman karajin ciwo ni kuwa na ma rasa abinda ya kamata nayi. Shin na tafi neman taimako ne, ko kuwa na kori kadon don ceto ran wannan bawan Allah? Kowanne zabi a ganina bani da mafita, don haka nayi ta adduoi iyakar wadanda nake iya tunowa cikin raina.

  ••••••
  Marubucin wannan labarin bai taba ganin kada a ruwa ba har zuwa lokacin rubutun, amma ta hanyar bincike da tambaya ya iya gane yadda take yi wa mutum..

  Don haka wajibi ne mai rubuta labari yayi tambaya da bincike musamman yanzu da muke da wuraren bincike a intanet.

  DARASI NA 4

  5. Rubutu na farko

  Bayan ka gama bincike, sai ka dauko Outline din da ka yi ka soma rubuta labari. Kana iya farawa daga kowanne Outline ka ga dama. Daga baya sai ka zo ka jera su.

  Anan rubutun kurum za ka yi ta yi kar ka damu da gyara ko duba adadin kalmomi. Kai dai kurum ka tabbata ka rubuta duk abin da ya zo zuciyarka. Wannan shi ake kira First Draft.
  Matsalar marubutanmu, yawanci daga wannan rubutun na farko ba sa kara waiwayensa, sai kurum su tura dab'i ko su watsawa duniya. Tilas kuwa a ga kuskure da tarin kwan gaba kwan baya.

  6. Karantawa da yin gyare-gyare

  A wannan mataki, marubuci zai zauna a tsanake ya karanta labarinsa. Zai dauki matsayin makaranci ne watau ya karanta labarin tamkar ba shi ya rubuta ba. Yana yi yana duba kuskure yana gyarawa. Anan ana so marubuci ya rika lura da sunayen mutane da wuraren da ya zaba kada a samu sabani.

  Duk gyaran da ya kama sai a yi. Tunda yanzu muna rubutu ne da naurori kamar a da da ake rubutu da biro da takarda ba, gyara ba shi da wahala sosai.

  Kana iya kwafin tsohon labarin daban kafin ka shiga yin gyararraki gudun ta ɓaci.

  Kana iya karanta labarin fiye da sau daya domin yin gyararraki.

  Labarina mai taken 'Da Sandar Hannunka Kake Jifa.' na karanta shi sau 15 ina yi ina gyarawa. A karshe na ci nasara, domin kuwa ya zo na uku a gasar Pleasant Library.

  7. Mikawa masana ko abokai su duba labarin

  Sau tari ko da marubuci ya karanta labarinsa ba ya iya gano wani kuskure da ke ciki. Don haka ake so ka samu wani ka ba shi ya karanta domin ya yi maka gyararraki ko shawara.

  Sai dai da yake yawanci manyan mu ba su da lokacin duba mana rubutu saboda tulin ayyuka, kana iya samun abokanka da ka amince da su ka aika musu labarin cikin sirri su duba maka. Kun san labarin gasa ba a so a fitar da shi kafin a aikawa masu gasa. Don haka yana da kyau ka zabi amintattunka da ba za su sake shi a gari ba.

  Duk labarin da na rubuta sai na zabi wadanda zan ba wa su duba min. Hatta surukaina ma ina kai musu rubutu su duba min kuma na ji raayinsu kan ma'ana ko dadin labarin.

  8. Sake yin gyara tare da tabbatar da sunayen taurari da wurare da kuma sarrafa kalmomi

  Bayan masu dubawa sun gama kuma sun ba da shawara. Za ka sake zama ka yi nazarin shawarwarin daya bayan daya ka dauki wadanda suka dace ka yi aiki da su.

  Har ila yau a wannan mataki ne za ka bi a hankali ka rage kalmomin da suka yi tsayi ka daidaita rubutunka zuwa adadin kalmomin da ake bukata. Kana iya cire wasu kalmomin ka sa wasu.

  Misali

  Ta yi tsalle a fusace = kalmomi 5
  Zuwa
  Ta hau sababi = kalmomi 3

  9. Samar da taken da ya dace da labarin

  A wannan gabar ne ya dace ka zabi taken da ya dace da labarin, domin duk lakabin da ka ba wa labari shi zai bi shi. Akwai hanyoyi da dama na samarwa labari suna, amma mafi shahara ita ce ka rada masa sunan da ma'anar abin zai fito daga cikin labarin.

  Mu kwana nan. 

  Ku latsa nan don karanta darasin rana ta karshe, rana ta biyar.

  Danladi Z. Haruna

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta labarin Afuwa ƙwaya Ce, Ka Shuka Ɗaya Ka Girbi Goma. An yi wani attajiri da ke da dukiya mai yawan gaske, ana kiransa Abu Tammamu. Saboda yawan dukiyarsa, bai san iyakacin abin da ya mallaka na daga gidaje da gonaki da dabbobi da bayi da sauran kadarori ba. B...
 • Ku latsa nan don karanta shafi na 12 da 13. SHAFI NA 14 Tana isowa ta dubi Mama tare da mika mata wayar "Ga mamansu Sumayya za kuyi magana." Mama ta amshi wayar ta saka akunne ta na fadin salamu alaikum jin shiru yasa ta dubi fuskar wayar tare da fadin "La kinga ta katse." Fati ta amshi wayar ta...
 • Zamantakewar aure, zamantakewa ce mai wahala, matuƙar wahala kuwa. Sai dai da zarar ka fahimci tana da wahalar, sai ta zama mai sauƙi a gare ka. Domin fahimtar tana da wahalar shi zai ba ka damar neman iliminta. Shi kuma iliminta sai ya ba ka damar samun sauƙin ta. A shirinshi da ya saba gabatarwa ...
 • An haifi Olufela Olusegun Oludotun Ransome-Kuti a ranar Asabar 15-10-1938, a Abekuta ta jihar Ogun. Iyayensa manyan mutane ne domin Mahaifiyarsa Fummilayo Ransome-Kuti, 'yar gwagwarmaya ce, mai fafutukar kwato 'yancin mata. Mahaifinsa Isra'el Olodotun Ransome-Kuti, babban limamin coci ne, shugaban ...
 • Idan aka ce Hepatitis, to ana nufin ciwon hanta kenan a Hausance. Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta na...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Dogaro Ga Allah Jari. Cikin ƙasashen Mongol an yi wani babban Sarki mai yawan jarumai ana kiran sa Bihikatu. Shi wannan Sarki jarumi ne amma mugu ne na ƙin ƙarawa. Tun da yake bai taɓa yin afuwa ga wanda ya saɓa masa ba. Ba a taɓa ganin dariyarsa ba s...
View All