Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Abubuwan da ya kamata ku sani game da cutar mantuwa na amnesia

Abubuwan da ya kamata ku sani game da cutar mantuwa na amnesia

 • Mece ce cutar mantuwa (amnesia)?

  Idan aka ce mutum na fama da cutar amnesia dai to ana nufin cutar da ke sa mutum ya manta abubuwa kamar abubuwan da su ke zahiri, da kuma bayanai game da wani abu ko kuma manta abinda ya faru da su da makamanta ire-iren wannan mantuwa. Mutane da su ke dauke da wannan cuta yawanci sun san kansu wato ma’ana ba su manta ko su, su wane ne ba. Babban matsalarsu shi ne koyon wani abu sabo ko tuna wani abu sabo a rayuwarsu.

  Wannan cuta ta kan samu ne saboda wani illa da ka yi wa bangaren kwakwalwa da ke da hakkin tuna abubuwa (areas of the brain that are vital for memory processing). A fadin masana harkar kiwon lafiya, cutar amnesia na iya zama har abada a jikin mutum ba tare da ya warke ba sai dai idan amnesia ce ta wucin gadi wato abinda ake kira a Turance da suna transient global amnesia.

  A yanzu haka dai ba bu wani takamemmen magani da za a ce ga shi na wannan cuta ce, to amma akwai ‘yan dabaru da ake taimakawa marasa lafiya domin inganta tunaninsu (enhancing memory) da kuma psychological support  da ake basu da su da iyalansu domin samun sassaucin wannan lalura.

  Alamomin mutun na dauke da wannan cuta ta amnesia

  1. Wahalan koyon sabbin bayanai a lokacin da wannan cuta ta fara shigarsu. Ana kiran wannan irin alama na amnesia da suna anterograde amnesia.

  2.Wahalan tuna baya, wato tuna abubuwan da suka wuce har da abubuwan da su ka san su sosai, ana kiran wannan da Turanci retrograde amnesia.

  Yawancin mutane da ke dauke da cutar amnesia suna fama ne da matsalar short-term memory. Ba sa iya tuna sabbin bayanai ko abinda ya faru da su. Abubuwan da suka yi da bai jima ba sukan manta su amman idan anyi sa a sukan rike ko tuna abubuwan da suka sani da jimawa. Za ka tarar wani lokacin mutum zai iya tuna abinda ya faru da shi yana yaro amma kuma ba zai iya tuna abinda aka yi ba da jimawa ba kamar zai iya tuna sunan tsohon shugaban kasa amma sai ya manta sunan shugaba mai ci. Za su iya sanin a wani wata ake ciki da makamanci abu irin wannan.

  Wannan isolated memory loss din baya shafan basirar mutum, da kuma general knowledge, da dai abubuwa kamar wayewar mutum da kuma yananin hallayyansa (personality ko identity). Mutanen da ke da wannan cutar yawanci suna iya karatu da rubutu za su iya koyon skill kamar hawa keke da makamantansu. Za ma su iya gane suna da matsalar mantuwa din.

  Amma cutar amnesia ba daya ta ke da cutar dementia ba. Ita cutar dementia ta fi amnesia tsanani domin kuwa baicin mantuwa da mutum ke tsintar kansa a ciki har ma da matsalar rashin fahimta, wadda zai kai ga gagaran yin abubuwan rayuwa, kamar kula da kai da makamantansu.

  Ku dubi wannan: Bayanai game da lalurar autism spectrum disorder galhanga

  Wasu karin alamomin cutar amnesia

  Ya danganta da mene ne musabbabin wannan cutar, mai amnesia na iya fuskantar:

  1. Tuna wasu abubuwa da ba su faru ba sam akan cewa ai sun faru wato abinnan da ake kira da false memory a Turance.
  2. Rikicewa da kuma birkicewa

  Lokacin da ya kamata a ga likita

  Duk wanda ya ke fuskantar mantuwa mai tsanani da bai san dalilinsa be ko kuma ya ji ciwo a kansa, ko ya ke fama da rikicewa ko kidimewa to lallai ya kamata ya ga likita cikin gaggawa.

  Abu na gaba kuma shi ne mutumin da ke fama da cutar amnesia ka iya kasancewa cikin wani irin yana yi da ba zai ma san yadda zai yi ba don ya taimakawa kansa da kansa , to anan ne ya kamata ‘yanuwa da abokan arziki su kula su taimaka su kai shi asibiti domin ya samu kulawan likitoci.

  Dalilan da ke kawo cutar amnesia

  Kafin a ce mutum ya kasan ce yana cikin hayyacin tunaninsa tsaf, yana bukatan bangarori da dama a kwakwalwarsa suna aiki yadda ya kamata. To duk wata matsala da ta taba kwakwalwa, za ta iya shafan tunanin mutum.

  Cutar amnesia na iya samuwa idan structure na kwakwalwa ya samu damuwa. Cutar amnesia da ta samu asali a sabili da jin ciwo a kwakwalwa ana kiranta da suna neurological amnesia. Dalilan da ke kawo neurological amnesia sun hada da:

  1. Stroke (bugun jini)
  2. Kumburar ko rauni a kwakwalwa (brain inflammation)
  3. Rashin isashshen iskar oxygen
  4. Jimawa ana alaka da giya har ya haifar da wani matsala da ake kira da thiamin
  5. Tumor (kari) a wajajen da ke kula da tunani na cikin kwakwalwa
  6. Ire-iren cutukan kwakwalwa irin su Alzheimer disease da wasu ire-iren dementia
  7. Seizures
  8. Wasu magungunan sedatives (Magunguna ne da ke aiki da kwakwalwa sosai ainun)

  Jin ciwo a kai har ya haifar da concussion kamar a yayin hatsarin mota ko wajen wasanni su kan haifar da kidimewa da kuma matsala wajen tuna sabbin bayanai. Wannan yanayi na yawaita ne sosai a lokacin sabo-sabon samun wannan matsalar na concussion. Idan jin ciwon kan ba mai yawa ba ne, yawanci ko da mutum ya samu amnesia ba ya dorewa, yana warkewa bayan wani dan lokaci. Amma idan jin ciwon ya tsananta wannan kan iya haifar da amnesia na har abada.

  Akwai kuma wani irin amnesia da ake kira da suna dissociative ko psychogenic amnesia. Ita wannan amnesia ba ta faruwa da yawa kuma tana faruwa ne sakamakon wani irin firgita mai tsanani wato emotional shock or kuma trauma da mutum ya yi. Idan mutum ya kamu da wannan amnesia ya kan mance personal memories na shi da tarihin rayuwarsa na wani dan lokaci amma ya kan warke da ga baya yawa-yawan lokaci.

  Abuwan da idan mutun na yi ko kuma suka same shi zai iya kamuwa da cutar amnesia sun hada da

  1. Tiyatar kwakwalwa ko kuma jin ciwo a kai kuma trauma
  2. Stroke (bugawar jini)
  3. Wayan shan giya
  4. Seizures

  Irin matsalolin da cutar amnesia ke kawo wa mai dauke da ita

  Ire-iren cutar amnesia suna su ka tara, wasu suna da tsanani wasu kuma ba su da tsani. To ammam komi kankanta amnesia ta na baiwa mai dauke da ita wahala wajen gudanar da rayuwa na yau da kullum. Cutar kan haifar da matsala a wajen aiki, ko makaranta ko kuma cikin hulda da jama’a haka.

  Yana da wuya ace mutum zai iya recovering lost memories na shi gaba daya. Masu fama da wannan lalura suna bukatan kulawa na musammam, Saboda haka babban nauyi ga duk mai kula da su. Muna rokon Allah Ya basu da sauki, amin.

  Mai karatu na iya duba wadannan tambayoyi da amsoshi 10 game da cutar coronavirus

  Kariya daga kamuwa da cutar amnesia

  Yana da matukar muhimmanci mutum ya kula da kansa ta inda zai iya kokari wajen kare kansa daga jin ciwo da zai shafi kansa. Domin jin ciwo a kai, kamar yadda muka ambata a baya, na daga cikin ummul aba’isin wannan cutar. Ga wasu daga cikin hanyoyin kariyar:

  1. A kiyaye yawan shan giya
  2. A saka hula (helmet) idan ana tukin keke, sannan idan ana tukin mota ne a yi kokarin saka belt a ko da yaushe
  3. A yi kokarin jinyar duk wani kwayan cuta da ke damun mutum domin kada wani dalili ya kai shi ga kwakwalwa
  4. A nemi magani da wuri idan a ka ga wani alamu na stroke ko ciwon kai mai tsanani da makamantansu

  Kuma kada ku manta duk wani alamun ciwo ko rashin lafiya da mutum ya lura ya gani, to ayi maza a garzya domin ganin likita. Wannan Makala da makamantasu na kiwon lafiya muna rubutasu ne domin karuwan ilimi, amma ba da magani sai kwararren kuma likita mai lasi! Allah Ya kara mana lafiya da zaman lafiya, amin.

  Source: Mayo Clinic

Comments

0 comments