Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » Duhun Damina: Babi Na Takwas

Duhun Damina: Babi Na Takwas

 • Ku latsa nan don karanta babi na bakwai.

  Bata iya komawa bacci ba tunda ta tashi daga wannan mafarkin. Ta yi kuka har sai da idanunta suka fara yi mata zafi, gangar jikinta da zuciyarta suna yi mata rad'ad'in da ita kad'ai ta san yanda take ji.

  Ƙirar sallahr asuba yasa ta mik'e cikin hanzari, tana jin hajijiya na kwasanta amma ta dake.

  Bata iya ɗaura idonta akan madubin bayan-gidan ba, saboda gani take mafarkinta na iya zama gaskiya.

  A ranta, ta san laifinta, ta san isharar da wannan mafarkin yake nuna mata. Ya zata yi da duniyarta da ta yi anfani da hannunta da idanunta don ɓatawa? Ya zata gyara wannan laifukan da Rabbil izzati kad'ai ya san da su? Shin Allah zai gafarta mata? Shin zata iya rayuwa ba tare da ta aikata wannan abunda take samun biyan buk'atarta daga shi ba?

  Abu ɗaya ya dace da ita, kuma ta amince da shawarar da ta yanke. Zata ajje kunya da jin kai gefe guda, ta yi abunda ya dace da duniyarta.

  Cikakkiyar alwala ta yi, tana mai kula da dukkan wanke gab'ob'i gudun lam'a. Zata kyautata addininta, ta kyautata lahirarta dan samun rabo da rahamar mahaliccinta.

  Ta yi kuskure, ta sani, kuma ta ɗauki ɗamarar yak'i da zuciyarta, shaid'anin da ke mata rawa a kai har ma da sha'awar da take ajjewa gaba fiye da komai.

  Sallah ta yi na nafila, tana mai neman yafiyar mahaliccinta, tana mai zubar da hawaye da sauk'ad da kai. Ta ajje duk wani abu da take ji dasu, a gaban mahaliccinta take, bata da iko, bata da komai kuma garesa take neman biyan buk'atunta.

  Bayan ta idar, ta yi raka'atanil Fajr sannan ta sauk'e farali na asubahi. Bata rok'i duniya ba a yau, bata rok'i kud'i da sauran abubuwan jin dad'in rayuwa ba. Ta rok'i yafiyar Allah, ta nemi tsari da sharrin shaitan, da kuma samun ƙarfin ikon aikata aikin alhairi.

  Har ta kwanta ko zata iya samun bacci ta sauk'o, tana mai nemo Qur'aninta dan zuciyarta har a wannan lokaci yana cike da tsoro.

  'In ta mutu cikin wannan yanayi fa? In ta kasa tashi bayan kwanciyarta ta wuce inda kowa zai je bayan barinsa duniya? Me zata gabatar gaban mahaliccinta matsayin aikinta? Shin bata da kunya ne? Anya Allah zai karb'i tubanta?'

  A duk lokacin da tunani irin wannan ya fad'o mata, tana jin ina ma ba a halicceta ba, ina ma tana da yanda zata yi ya zama babu ranar ƙarshe, ita ta sani, aikinta bai isa ya shigar da ita rahamar Allah ba wato aljanna, Allah ba zai dubeta ba bare har ta samu kyakkyawar masauk'i a lahirarsa.

  Kuka ta yi sosai a yau, tana mai ci gaba da istigfari a duk lokacin da mafarkinta ya fad'o mata. Karatun Qur'ani ta yi har izu biyar sannan ta ajje ta fito cikin gida, ba dan komai ba sai don ta gyara gidan dan samun ladan da zai iya goge laifukanta.

  'Anya ma laifukanta zai gogu daga littafinta?'

  "Astagfirullah wa atubu ilaih!"

  Ta furta cikin tsoro had'e da runtse ido tana ci gaba da gyaran falon.

  Ƙarfe bak'wai da rabi ta ɗauki wayarta, bayan ta gama yanke shawarar abun yi, wanda ta tabbata shi ya dace da ita kuma shi ya dace da lalurarta.

  *****

  Tun jiya bayan ya dawo daga wurin mahaifinsa ya kwanta ko wayarsa bai duba ba, sanin cewa babu wanda zai nemesa a irin wannan lokaci.

  Toh dama Juwairiyya ce, kuma tana fushi ta ƙi ɗaga wayarsa bare yasa ran ganin ƙiranta.

  Duk da bai yi bacci da wuri ba, jin kalaman mahaifinsa ya sa shi farin ciki, ya jefa sa duniyar da shi kansa bai ɗauka akwai irinsa ba. 

  Sai dai wannan albishir bai zo lokacin da ya dace ba, bai zo lokacin da zai yi cikakken farin ciki ba.

  A yanzu da yake ta juyi akan gadonsa bayan ya dawo daga sallahr asuba, tunani ne ya cika kwanyarsa. Neman mafitar matsalarsa guda yake, tunda Allah ya amsa masa amincewar mahaifinsa.

  'Ta ya zan samu amincewarta bayan abunda na yi mata? Ta ya zan tunkareta da maganar mahaifina yana son ya yi magana da nata mahaifin akan aurenmu? Anya Juwairiyya zata sake amincewa da ni?'

  A zuciyarsa yake wannan tambayoyi, yana mai juyi akan gadonsa.

  A jiya da mahaifinsa ya sanar dashi dalilin ƙiransa, zai iya cewa babu mahaluk'in da ya kai sa farin ciki. Sai dai a yanzu da yake kwance a kan makeken gadonsa, komai ya cunkushe masa, ga samu ga rashi. 

  Idanunsa ya runtse, yana mai jin ɓacin rai da haushin aikinsa. Bai kyauta wa kansa ba, bai ɗauka hankalinsa zai iya gushewa a wurin Juwairiyya ba. Ko da yake, turarenta ya ƙara lular dashi, ita ma da nata laifin.

  "Ya Rabb!" 

  Ya furta yana fitar da iska mai zafi ta bakinsa. Ba maganar laifinta bane yanzu, maganar mafita yake, neman yardarta da amincewarta.

  Zai ci gaba da binta har sai ta hak'ura da fushin da ta yi dashi. Ina zai iya rayuwa ba tare da Juwairiyyarsa ba?

  Wayarsa ya janyo dan duba lokaci, da alamu bacci bazai iya d'aukansa yana cikin wannan yanayi ba.

  Sak'on Juwairiyya ya shigo a daidai lokacin da ya kunna hasken wayar. Bakinsa bud'e ya tsaya kallo, dan bai yi tsammanin ganin sak'onta a wannan lokaci ba. Ƙarfe 7 da mintuna arba'in ne, ya tabbata a irin wannan lokaci bacci take yi.

  Sai da ya had'iye yawu mai tauri sannan ya danna wayar ya shiga cikin sak'on. Ba doguwar wasik'a ba ce, haka zalika ba abunda zuciyarsa ya raya masa bane.

  "Let's get married! (Mu yi aure!)"

  Ya karanta a fili, yana jin damuwarsa na raguwa farin cikinsa na ninkuwa. Sai dai mamaki bai barsa ba.

  Juwairiyya ta gama yi masa komai a rayuwa. Ta hak'ura kuma ta ga dacewar aurensu saboda gudun maimaituwar abun da ya yi mata.

  Da hanzari ya ƙira layinta, amma har ya gama ƙara bata ɗauka ba.

  "Juwairiyya alkhairi ce gareni, ina alfahari da ke da kaifin tunaninki. Ina sonki da dukkan zuciyata, ina kuma son kasancewa tare da ke har abada".

  Murmushi yake sakarwa kansa, yana nuna tsantsar farin cikinsa. Addu'a ya ke yi mata can cikin zuciyarsa, na Allah ya yi mata albarka ya kuma saka mata da alkhairi dan fahimtarsa da ta yi.

  *****

  11:00am

  Tun bayan da ta aika masa sak'on ta sa wayar a 'silent' tare da ɓoyewa a ƙark'ashin filonta, ta san dole ya ƙirata, ita kuwa bata tunanin zata iya amsa wayarsa bare har ta yi masa magana. 

  Laifinsa bai kai nata ba, a tunaninta. Me laifi dan ta goge nasa ta janyosa dan su samu cikar rabin addininsu? 

  Tana tsoron jin amsarsa, tana tsoron yanda zai ɗauki maganar. Sai dai ya zata yi? Hakan take so, kuma hakan shine shawarar da ta yanke.

  Ta rubuta wannan sak'o yafi sau goma tana gogewa, saboda a ganinta shi ya dace ya fara yi mata maganar.

  Sai da ta kai zuciyarta nesa sannan ta aika masa sak'on, tana rok'on Jallal-Allah yasa bata yi kuskure ba.

  A yau Juwairiyya bata iya cin abincin kirki ba lokacin da mahaifiyarta ta ƙirata dan cin abinci. Haka zalika ta kasa sakewa ta yi hira da kowa a gidan.

  Mahaifiyarta ta lura da hakan, sai dai ta bar wa kanta abunda take tunani game da Juwairiyyar. 

  Bata kasance uwa da take barin abu ya wuce ba tare da ta bi diddigi ba, kuma bata kasance uwa mai nuna wa 'ya'yanta sun yi kuskure ba tare da tana da tabbaci ba.

  Tun ranar da suka yi maganar infection da Juwairiyya take lura da ita, take kuma lura da yanayinta. Ba wai yanayi na lokaci guda ba, a'a, tana lura da yanayinta a duk lokacin da aka nuno wani abu mai kama da miji da mata a talabijin.

  Tun da, ta san irin ɗiyarta, ta san yanayinta, sai dai bata tab'a ɗaura mata abunda take gani daga gareta a yanzu ba.

  Lumshe idanunta a duk lokacin da suke kallon film na India aka hasko miji da mata, lashe leb'b'a har ma da gyara zama ko kwanciya. 

  Bata fatan abunda take tunani ya hau kan ɗiyarta. Ya zama dole ta sanar da mahaifinta dan a bata dama ta kawo mijin aure. 

  Bata son hasashenta ya kasance gaskiya, duk da ta kasa ganin tabbacin hakan daga gareta, ba za ta so 'yarta ta fad'a halaka tana sane ba.

  A yau, tun fitowarta da safe ta kula da yanda Juwairiyya ke abubuwa kamar ba jini a jikinta. Ga idanunta ya sauya ba irin yanda ta saba ganinsu ba.

  Idanunta bai ɗauke daga kanta ba, hatta kitchen in ta shiga tana binta a wayo dan ta ga me zata aikata. Duk da bata ga komai ba, amma hankalinta bai kwanta ba har shigewar Juwairiyya ɗaki.

  Mintuna goma ta bawa kanta, sannan ta mik'e tana addu'ar Allah ya sa kada ta ci karo da zarginta. Tana tsoro, ta sani tana tsoron mugun gani, amma ya zata yi da Allah ya ƙaddaro mata tarbiyyar ɗiya mace? Macen ma mai irin halittar Juwairiyya?

  Isowarta ƙofar ya ƙara tsananta bugun zuciyarta, sai dai bata saduda ba, sai ma ƙarfin gwiwa da take bawa kanta, na sanin abunda yake damun 'yarta da kuma abunda take aikatawa.

  Hannunta ta ɗaura a mabud'in ƙofar, ta had'iye yawu mai tauri had'e da lumshe idanunta.

  Ƙofar ta bud'e ba tare da sallama ba, ta sa kai tana mai ɗaura idanunta akan Juwairiyya da ke kwance kane-kane akan gadonta, jibgegen bargonta rufe a jikinta ruf ga wayarta a hannunta, wanda ganin mahaifiyarta yasa ta yi hanzarin kifarwa tare da tasowa kad'an daga kwanciyarta.

  *****

  Me Juwairiyya take yi?

  Shin me matsalarta?

  Me labarinta?

  Me take ɓoyewa?

  Tambayoyi akanta da yawa.

  Shin kun shirya dan jin komai daga gareta?

  Kun shirya ku karbi labarin rayuwarta da babu wanda ya sani sai ita da mahaliccinta?

  Daga babi na gaba inshaAllah, komai zai fito ku ga komai.

  Ku biyo ni a sannu dan mu warware labarin Juwairiyya. 

  Mu fada rayuwar aurenta har ma mu ga da me Hamrah ta shigo babin rayuwarsu.

  Thank you for reading, Jazakumullah

  Ku latsa nan don ci gaba da karanta babi na tara.

  Alkalamin Maryamerh Abdul

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • A karkashin ilimin kimiyyar lissafi wato (physics), yau zamu yi karatu ne akan wata maudu’i mai matukar mahimmanci. Wannan maudu’in kuma ba wata ba ce face heat. Idan muka tuna a makalar da ta gabata mai suna energy mun ce heat nau’i ne daga cikin nau’ukan energy. A yau zamu ...
 • A wannan makala dalibai za su ga yadda za a yi bayani game da work da kuma power dama yadda ake solving mathematical problems. Workdone ko work a physics yana nufin a yi multiplying na force da displacement. Sa’annan aikin yana gudana ne a direction na force. Idan har W ya kasance work, F kum...
 • Vanilla cupcake kalar cupcake ne da yara kar harma manya su ke so sosai. Na san muta ne da dama suna sha'awar koyon yadda za a sarrafa shi. Saboda haka a yau muka kawo muku yadda ake yinsa domin mai sha'awar koyo. Wannan recipe idan kin bi shi yadda ya ke, za ki samu cupcakes guda 20 ne dai dai. Ab...
 • Ku latsa nan don karanta babi na takwas. Ga ɗaurin Zahra Buhari. Ni dai ban iya ɗaurin ba. Yayata ke kafa min in zan je biki. In kuwa fita yawo ne ɗaurin 'yan Hausa na ke yi mai lankwasa a gaban nan. "Mama!" Ta furta cikin mamakin ganin ta. Bata saurareta ba bare ta amsa, cikin hanzari ta isa bak...
 • A kwanakin baya na ga wani tattaunawa a social media game da zuwa aiki ga mata, musammam matan aure da kuma mata masu yara. Abinda na lura shi ne yawanci mazaje ba su fiya son matansu na zuwa aiki ba duk da cewa yawancin mazan na so a ce matansu sun yi karatu sosai kuma sun waye da sanin abubuwan ra...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Mai Haƙuri Ya Kan Dafa Dutse. A ƙasashen ƙetare an yi wani ɗan Sarki ana kiran sa Bihizadu. Ya kasance kyakkyawa ne, kuma yana da kirki domin kuwa yana zama tare da talakawa da fatake da attajirai. Mutane suna son sa, sai dai yana da saurin ƙagauta a al'amuran ...
View All