Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Mene ne ku ka sani game da cutar mantuwa na Alzheimer’s?

Mene ne ku ka sani game da cutar mantuwa na Alzheimer’s?

 • Cutar mantuwa na Alzheimers dai cuta ce da ita ce gaba-gaba wajen janyo cutar nan na dementia kuma ita ce ta fi yawa a cikin ire-iren cutar neurodegenerative disorders. Cututtukan neurodegenerative disorders wasu cututtuka ne da suka shafi rashin yin aiki ko matsala na wani bangare na kwakwalwa. A kasar Amurka an kiyasta misalin mutane miliyan biyar ne ke fama da wannan cuta ta Alzheimer’s. Duk da cewa, yawanci, akan gano wannan cuta ne a jikin mutane a lokacin da suke shekaru sittin da biyar zuwa sama, amma akwai kadan daga cikin masu fama da ita da aka gano suna da wannan cuta a shekaru kasa da sittin. Kuma an kiyasta wannan cuta ita ce a lamba ta shidda daga cikin cututtuka da ke sanadiyan mutuwa a kasar Amurka.

  Cuta ce da ake danganta ta da mantuwa wadda mantuwa ke kara tsanani (progressive memory loss) idan shekaru na tafiya. Sannan kuma masu cutar na fiskanatar canjin yanayi na mood da kuma personality. Idan cutar ta jima mai fama da ita na iya komawa baya iya yin komai wa kansa sai dai abinda aka yi da shi. Saboda da tsanani da kuma wahalar wannan cuta, jinyar ta tana da tsada sosai. Masu dauke da wannan lalura sunfi  saurin mutuwa idan aka kwatanta da takwakwarorinsu wadanda basu da ita.

  Sannan mai karatu na iya duba wani kalan cutar mantuwa da ake kiran amnesia anan

  Kaman sauran cututtukan da suka shafi kwakwalwa, alamun cutar Alzheimer’s sun hada da:

  1. Ci gaba da mutuwar kwayin halittan kwakwalwa da kuma ci gaban rasa hankali (Pogressive of death of brain cells and loss of mental abilities)
  2. Cutar na samuwa ne saboda misfolding na wasu proteins wadda hakan ke haifar da abinda ake kira da oxidative stress da kuma mutuwan kwayin halitta (cell death).
  3. Taimako da ake bayarwa na therapy da kuma magunguna ana yin su ne kawai domin ba da kwarin guiwa ne ga majinyatan. A kashin gaskiya ba bu wani maganin zamani da ke iya tsayar da ci gaban wannan cutar sai dai ya rage saurin ta kawai.

  Babban kalubalen da ke tare da cutar Alzheimer’s shi ne rashin gano ta da wuri. Yawa yawan lokaci, yayin da aka gano mutum na fama da wannan cutar, an rigaya an bata lokaci mai muhimmanci sosai na farkon shigan wannan cutar. Domin cuta na shiga jiki ne a sannu a hankali har ya dauki shekaru kafin ma a ce an yi gwaji an gano cutar shekaru sun tafi. Amma idan za a yi sa’a a gano cutar da wuri to hakan zai taimaka sosai wajen ganin an karyar lagon saurin yaduwantan ta.

  Ga wasu alamu na fara shigar cutar (early signs)

  1. Wahala wajen tuna abu (remembering), da natsuwa (concentrating) da kuma warware matsala. Amma yawanci ana cakuda wadannan alamu da alamun tsufa wadda su daman can suna zuwa da tsufa.

  2. Kidimewa na rashin gane wuri da lokaci

  3. Wahala wajen yin ayyuka da ba masu wahala ba a gida. Ayyukan da ba su bukatar wani tunani ko karfi.

  4. Wahala yin karatu ko fahimtar kwatance wato visual clues

  5. Wahala wajen yin magana ko kuma wahalan zance da jama’a

  6. Rasa abubuwa masu muhimmanci

  7. Rashin sanin abinyi ko abinda ya kamata a yi wato lack of proper judgement

  8. Cire kai ga hulda da mutane

  9. Canjin yanayi da kuma personality (mood and personality changes)

  Wadannan su ne alamu da suka fi yawa a farkon kamuwa da wannan cuta, amma yana da matukar muhimmanci kar a cakuda su da alamun tsufa. Domin a bangaren cutar Alzheimer’s, wadanan alamu za ka ga suna nuna alamun karuwa da ci gaba a kullum.

  Duk da cewa babu maganin warkar da cutar Alzheimer’s, akwai wasu hanyoyi marasa hatsari da ake bi domin a rage saurin cutar sosai. Wasu daga cikin wadan nan dabaru na rage saurin wanan cutar suna taimakawa wajen karawa mutum tsawon kwana da kuma iya rayuwa ba tare da dogaro da taimakon mutane ba wato independent na tsawon lokaci.

  Motsa jiki kamar mild to moderate aerobic suna taimakawa sosai wajen kariya da kuma rage yaduwan cuta da sauri. An kiyasta cewar motsa jiki na misalin mituna 150 a sati yana rage hatsarin kamuwa da cutar Alzheimer’s da kusan rabi. Hanyar da ta fi dacewa shi ne mutum ya motsa jiki matsakaici wato moderate exercise na kaman tsawon minti 30 sau biyar a sati. Wannan moderate exercise yana da kyau ga zuciya da kuma metabolic diseases. Sannan motsa jiki da ke kara karfi kamar su Tai Chi or Yoga su ma suna taimakawa sosai.

  Sannan kula da abinci da ake ci, wannan ma wata hanya ce mai matukar muhimmancin gaske wajen bada kariya ga kamuwa da wannan cuta ko kuma rage saurin yaduwanta idan an rigaya an kamu da ita. Wasu da ga cikin hanyoyin da za a bi domin samun abinci masu lafiya sune rage cin abinci mai trans fats da saturated fat (duk wadannan, trans and saturated fats, ana samun su a man abinci da muke saya na kanti). Cin abinci na Mediterranean diet wato abinci da ke dauke da kifi maimakon nama da kuma abinci mai yawan ganyeyyeki da dai sauran abinci masu kyau ga jiki.

  Sannan yana da muhimmanci a rika yawan exercise na kwakwalwa ta hanayar yawan karatu da yin irin su puzzle games da kuma shiga cikin social groups ana hulda da mutane da sauran abubuwa da za su rika bawa kwakwalwa exercise.  

  A karshe kamar yadda muka fada da farko, motsa jiki da kuma exercise na kwakwalwa tare da tsari mai kyau na physical activity sune hanyoyi wadanda suka fi inganci wajen kariya ga cutar Alzheimer’s ko kuma rage illarta ga mai dauke da ita. Sannan kuma bai cin wadannan mutum kan iya amfani da supplements da sauran dabaru da likitoci ke taimakawa da su.

  Cutar Alzheimer’s na daya daga cikin cututtukan da mutane da yawa ba su fahimce su ba, amma abinda masana kiwon lafiya suke cewa tsananin da alamun wannan cuta ya bambanta daga mutum zuwa mutum. Saboda haka idan wani ko wasu dabaru na jinya bai yi wa wasu amfani ba, wannan baya nufin kai ba zai yi maka aiki ba. In ji malam Bahaushe, sai an gwada akan san na kwarai! Allah Ya bamu lafiy a da zaman lafiya  

  Kuma kada ku manta duk wani alamun ciwo ko rashin lafiya da mutum ya lura ya gani, to ayi maza a garzaya domin ganin likita. Wannan Makala da makamantasu na kiwon lafiya muna rubutasu ne domin karuwan ilimi, amma ba da magani sai kwararren kuma likita mai lasi!

  Source: Penprofile

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Mene ne zazzabin cizon sauro? Zazzabin cizon sauro wato malaria cuta ce da ta ke damun mutanen duniya, musamman mutanen Afrika, kuma wannan cuta tana daya daga cikin cututtukan da suke damun mutanen Nigeria. Tana iya shafar yara, manya, tsofaffi, maza da kuma mata. Ma'anar maleriya Maleriya cuta ...
 • Maza da mata jinsi ne guda biyu mabanbanta da ke da bambancin halaye. Maza da mata suna da yanayi daban-daban, amma da fatan wannan makalar za ta taimaka wajen fayyace abubuwa da samar da kyakkyawar fahimta game da irin wadannan bambance-bambancen.  Ya kamata maza da mata su yaba wa wadannan ba...
 • Ciwon sanyin mata wata babbar matsala ce da ke addabar mata. Akasarin mata na fama da wannan cutar, daga kauye zuwa birni, matan aure da yan mata. Kafin nayi wannan rubutun sai dana tattauna da mata da yawa akan wace cuta ce tafi damun mata a yanzu? Amsar dana samu kuma ita ce 'ciwon sanyi'. Mene n...
 • Mece ce cutar sikila (sickle cell disease)? Jini wanda ake gani a zahiri idan mutum ya ji ciwo ko kuma ya yanke jikinsa yana dauke da abubuwa iri daban – daban, kamar su plasma, Red Blood Cells (RBC), White Blood Cells (WBCs), Platelets da sauransu. Cutar sickler ko amosanin jini tana faruwa ...
 • Brain tumor wani tudun tsiro ne na abnormal cells (wato wasu kwayin halitta) da ke samuwa a kwakwalwan dan adam.  Akwai kala daba-daban na wannan brain tumor din. Wasunsu basa kaiwa ga kansa (benign) sanna wasunsu kuma sukan kai ga zama kansa (malignant). Brain tumor kan fara ne daga kwakwalwa ...
 • Matashiya Zazzaɓin Typhoid (taifod) cuta ce mai saurin yaɗuwa a jiki wacce wata bacteria ce mai suna Salmonella enterica serotype typhi ke haifarwa. Zazzaɓin taifod yana da alamomi wadanda suka shafi cutar kuma suke nunawa. Manya-manyan alamominta sun haɗa da zazzaɓi, da ciwon gaɓoɓin jiki, da yaw...
View All