Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » Duhun Damina: Babi Na Tara

Duhun Damina: Babi Na Tara

 • Ku latsa nan don karanta babi na takwas.

  Ga ɗaurin Zahra Buhari. Ni dai ban iya ɗaurin ba. Yayata ke kafa min in zan je biki. In kuwa fita yawo ne ɗaurin 'yan Hausa na ke yi mai lankwasa a gaban nan.

  "Mama!" Ta furta cikin mamakin ganin ta.

  Bata saurareta ba bare ta amsa, cikin hanzari ta isa bakin gadon ta kwaye ƙaton bargon cikin zafin nama. Ta shiga kallonta daga sama har ƙafafunta.

  Riga ce daidai gwiwa a jikinta da wandonsa, babu alamar tana wani abu dan kayan ko alamar ɗaguwa bai yi ba.

  Yawo idonta yake yi a kan gadon, tana fad'a wa kanta ba komai, Juwairiyya ba abunda take yi.

  Mikewa Juwairiyya ta yi ta tsaya gefen mahaifiyarta, mamakin abunda take aikatawa bai bar fuskarta ba.

  "Mama lafiya? Me ya faru?" Ta tambaya tana mai son jin amsarta.

  Babu alamar zata amsata. Sai ma ganinta da ta yi ta ɗauko wayarta da ta kifesa tana kunnawa.

  Babu password, hakan ya bata daman budewa cikin sauki ya bayyana mata abunda Juwairiyya ke gani kafin shigowarta.

  "Mama...!"

  "Ki barni in gama abunda nake yi Juwairiyya."

  Sai da ta gama karance sakon tsaf sannan ta nuno mata wayar, ta na kallonta dan neman karin bayani.

  "Abdulwahab ne." Juwairiyya ta amsa, tana saukar da idanunta.

  "Uhum?"

  "Abunda ya ce kenan, yana son in fada muku zai turo. Abunda nake karantawa kenan kika shigo".

  Nannauyar numfashi mahaifiyarta ta sauke. Tana hamdala a ranta tare da fatan alhairi a al'amarin.

  "Shi ne duk kika tada min hankali? Tun safe kin sa na kasa sukuni? Haba Juwairiyya. Wannan abun ne kawai zaki kasa sanar da ni har ki takura kanki kina abu sumui-sumui. Auren ne zamu hanaki?” Ta ci gaba da cewa. “Zan sanar da mahaifinki a yau ɗin nan ba sai gobe ba. Duk yanda muka yi kya ji."

  Wayarta ta mika mata tana ƙakalo murmushi, ko ba komai ta wanke zargin da take yi wa 'yarta.

  Ficewa ta yi daga ɗakin, tana mai jin nutsuwa na shigarta.

  A yanzu abu ɗaya ya rage mata, maganar auren da ya zama dole a yi sa in ana neman zaman lafiya, dan a yanda take ganin Juwairiyya abun nata yayi ƙamari.

  Juwairiyya ta gane nufin mahaifiyarta, ta san abunda yake yawo akanta. Dad'inta daya, ta tuba, kuma tubanta yazo daidai lokacin da mahaifiyarta ke zarginta.

  Ba dan hakan ba, ta tabbata mahaifiyarta zata isketa cikin wannan aikin.

  "Alhamdulillah!"

  Idanunta na cikowa da hawaye, tana ci gaba da istigfari a zuciyarta.

  Wayarta ta ɗauko, tana mai lalubo layin Malam Mustapha. Kafin ta ci gaba da aiwatar da ra'ayinta ya kamata ta ƙirasa dan jin bayani gamsashshe game da halin da ta tsinci kanta.

  "Assalamu alaikum!"

  "Wa alaikis Salam Malama Juwairiyya, ya kike?"

  Muryarsa da kuma yanda ya kyautata zatonsa a kanta, bazata iya fitowa ƙarara ta sanar da shi damuwarta ba.

  Hakan ya sa ta ƙak'alo murmushi tare da saita sautin muryarta. Gaisuwa suka yi kamar yanda suka saba, malami yake a wurinta kafin ya bar garin Kaduna, kasancewarta ɗalibarsa mai hazak'a da kwanya yasa suke gaisawa har bayan barinsa Islamiyyarsu.

  "Ƙawata ce ta zo min da wata tambaya malam, wanda ni alal hak'ik'a bani da amsar tambayarta, shine nace bari in ƙiraka ko zaka cire mu daga duhu".

  "Na'am, Allah ya sa na sani ina jinki."

  Tiryan-tiryan ta sanar dashi mafarkinta, tana mai iya k'ok'arinta dan daidaita sautin muryarta sakamakon tsoron da take samun kanta ciki.

  "Subhanallah!" Ya furta bayan ta kai aya a labarin nata.

  Ci gaba ta yi da cewa. "Malam a yanda tace, mafarkinta na da alaka da istimna'i da take yi, ko kuma kallon fina-finan da kowa ya san haramcinsa".

  "Eh toh, kai tsaye bazamu iya cewa hakan ba, amma shin, tana son sanin menene ma'anar mafarkinta?"

  Yawu mai tauri ta had'iye da ya furta wannan tambayar, bata tunanin zata so jin ma'anar mafarkinta, gwanda a barsa a rufe ko zata samu nutsuwar ruhinta.

  "A'a, ita dai tace tana son sanin abunda ya dace ta yi."

  "Hakan ya fi, saboda mafarki yana iya zuwa daga shaitan sannan kuma yana iya zuwa daga abunda mutum ya sa a ransa ko kuma isharar kamar yanda ta yi tunani."

  'Ya zo min saboda tunanin da na dade ina yi a kai a wannan ranar, abunda Abdulwahab ya yi min ya sa na yi tunanin ko aikina yasa ya zo gareni. Allah ka sa hakan ne." 

  Ta rok'a duk da wani sashe na zuciyarta na tabbatar mata ishara ce, sanin bayanan malam zasu wuceta yasa ta kawar da tunanin tana mai mik'a masa hankalinta kacokan.

  "Kin ga shi istimna'i, an samu sab'anin malamai. Wanda mafi yawan mutane basu tab'a damuwa da sanin cikakken bayani a kan wannan sab'ani ba.

  Imam Malik da Imam Shafi'i sun haramta kai tsaye, wanda hujjarsu shine. A cikin Al-Qur'ani mai girma, Suratul mu'uminun Allah yace "kuma waɗanda suke ga farjojinsu masu tsarewa ne.

  Face a kan matan aurensu, ko kuwa abin da hannayen damansu suka mallaka (Kuyangu) to lalle su ba waɗanda ake zargi ba ne.

  Wanda ya nemi biyan buƙata a abin da ke bayan wancan, to waɗancan su ne masu ƙetarewar haddi/masu take dokar Allah."

  Kin ga anan, haramcin istimna'i ya fito.

  Imam Abu Hanifa kuwa, ya tafi akan Halal ne amma da sharudd'a. Hujjarsa kuma ya tafi akan ƙiyasi, inda aka halalta cin dabba matacce dan rashin abun ci, ko kuma giya dan rashin abun sha.

  Misali:-

  Mutum ne yana cikin sahara, ya yi kwanaki bai ci komai ba, yunwa ya addabesa wanda zai iya mutuwa in bai samu abinci ba. Kwatsam ya samu kaza ta mutu a gabansa, an halalta masa ya ɗauki kazan nan ya babbaketa ya sarrafa ya ci.

  Haka ga wanda yake jin kishi ya rasa ruwan sha, kuma sai ya ga giya, rashin shan ruwan na iya illatasa, an halalta masa ya sha wannan giya.

  Sai Malam yace, to tunda an halalta irin wannan a lokacin da ake gabar azabtuwa, to ai shi maniyyi "sperm" in ya zauna a jiki a lokacin da ake cikin matsanancin sha'awa zai iya illatar da bawa, babu laifi ya yi istimna'i dan ya ciresa. Sab'anin hakan, haramun ne bai halalta ba a cewarsa.

  Amma shin hujjarsa ya goge ayar Allah?

  A'a, hakan yasa aka jingine bayaninsa a gefe, dan aya ta goge wannan hujja.

  Sai kuma Imam Ahmad ibn Hambal da ya tafi akan halal ne, hujjarsa kuwa ita ce akan mutum ya fada babban, wato zina, gara ya fada ƙarama.

  Shima hujjarsa an jingine gefe guda, babu inda ake ɗaukan ƙiyasi a inda aya ko hadithi ingantacce ya bada bayani a kai. (Duba tafsir na suratul mu'uminun aya ta biyar, shida da kuma bakwai).

  Ina fata kin fahimta?"

  Kada kanta ta yi, tana mai amsa shi da cewa, "Eh ina fahimta."

  "Abun da ya dace da wannan ƙawar taki, tunda ta gane tana kuskure, ta ci gaba da istigfari, ta nesanta kanta daga dukkan abunda zai iya jefata wannan hali.

  Kama daga hotuna, rubutu, faifan video, hatta ita kanta, ta nesanta kanta da ganin al'auranta, ko da wanka ta je, ta ƙokarta ta hana kanta dadewa ciki kuma ta kiyaye ganinta.

  Ta daina zama ita ɗaya, ta yawaita shiga cikin mutane. In zata kwanta, ta tabbatar ta sanya kayan da zai yi mata wahalar cirewa ko da tunanin hakan ya zo mata. Ba dan komai ba, sai don duk lokacin da hakan ya bijiro mata kafin ta kai ga aiwatarwa zata iya daidaita nutsuwarta.

  Ta sa a ranta tana aikata sabo, tana tunatar da kanta inda wannan aiki zai iya kaita, wato wuta.

  Daga ƙarshe ta nemi miji ta yi aure."

  Sosai ta ji dadin bayanansa. Godiya ta yi masa bayan ta tabbatar masa zata sanar da ƙawarta duk bayanansa sannan suka yi sallama.

  Kwanciya ta gyara akan gadonta, tana yi wa kanta fadan halayenta, daga bisani ta shiga tunanin farkon musabbabin fadawarta aikata istimna'i.

  Mafarin komai

  "Ga shi ki ajiye min, Juwairiyya, banda tabe-tabe, yanda na baki haka zaki bani abuna."

  Wayar ta karba, bayan ta kada kanta alamar ta ji bayaninsa, kuma zata yi yanda yace.

  Sai dai zuciyarta da tunaninta yana jaddada mata bude wayar da zaran ya tafi, tana son ta ga abunda Ayman yake ɓoyewa, ba za ta iya hana kanta ba.

  Ficewa ya yi bayan ya ɗauki kayan ƙwallonsa, ya bi sauran abokansa da zasu buga wasa da malamansu a yau.

  Bata fita ba Juwairiyya, bata kasance mai son wasan ball ba, hakan ya sa ta zauna cikin ajinsu (SS1) ita ɗaya bayan ta tabbata babu wanda zai dawo bayan tafiya filin kwallo.

  A hankali ta shiga binciken wayarsa ƙirar Nokia C3, sabuwar fita ne wanda mahaifinsa ya sayo masa satanni biyu da suka wuce.

  Hotuna ta fara kallo, wanda mafi yawa na 'yan mata ne cikin shigar rashin mutunci. Kallo take yi, tana rayawa a ranta abunda yake ɓoyewa kenan.

  Bata ji komai a ranta ba, shekarunta goma-sha-biyar a lokacin. Ganin hotunan ba masu ƙarewa bane ya sa ta fada wurin ajiyar bidiyo.

  Ta ci karo da abun dariya masu yawa, tana ta kyakyatawa ita kadai, a hankali ta sauko kan faifan da har a yau, ta sani, shi ne silar canjawar rayuwarta, shi ne silar shiganta wannan hali.

  Da ta sani, da ta hana kanta bude ajiyar da aka bata, da ta sani da ta fice kallon ball ɗin nan ko da kuwa bata ra'ayi.

  A lokacin da ta ɗaura idanunta a kan faifan bayan ta danna "Play", ta ji zuciyarta ya tsinke.

  Da farko ta ji abun ya bata ƙyama, ya kuma bata tsoro, hakan yasa bata iya kallo da yawa ba ta kashe, tana mai aiyanawa a ranta, Ayman ɗan iska ne.

  *****

  Tun ranar da hakan ya faru, daidai da rana guda bata taba yi ba tare da ta tuno ba. A duk lokacin da wannan abu ya fado ranta, ta kan ji tsoro ya shigeta, amma wani sashe na zuciyarta na kwadaitar da ita sake kallo.

  Ranar Jumma'a, kamar ko yaushe sun fito tara (break) tana tare da ƙawayenta. Ayman ya iso wurinsu yana ta washe baki.

  Duk da ta daina kulasa sosai kamar da, bai hana lokacin da ya ce yana son magana da ita ta iso garesa ba. A nan ya ciro wayarsa, ya mika mata yana magana a hankali.

  "Na zo da waya wasu suka gani, wai za su kai ƙara. Dan Allah ki ɓoye min na san babu wanda zai yi tunanin yana wurinki, in an tashi zan zo in karba. Yana silent kar ki damu".

  Hannu ta sa tana karba, zuciyarta na bugawa. "Ayman in aka kama fa?"

  "Kar ki damu, ba abunda zai faru, Daddy sai ya saya min wani".

  Murmushi ya sakar mata dan ƙara bata ƙarfin gwiwa. 

  Wayar ta sa cikin ƙaramin hijabinta ta koma cikin ƙawayenta. A zaman nata ta san yanda ta yi ta cusa tsakanin cikinta, hantsen wandonta ya rike tamau, duk da rashin sabo yasa tana rikewa lokacin da ta tashi zata koma aji.

  Har aka tashi ta sanya wayar a jakanta ta fito bata ga Ayman ba. Da ta shiga nemo ƙannenta kuwa, shaf ta mance da batun waya har direba ya zo ta shige mota ta koma gida.

  *****

  Bayan sun iso gida, ɗakinta ta wuce kai tsaye bata hadu da mahaifiyarta ba. Hakan ya bata damar shiryawa cikin sauki, ta yi wanka ta sanya kayanta sannan ta fice neman abinci.

  A ɗakin mahaifiyarta ta gabatar da sallolinta, ta zauna da 'yan kannenta suka sha hira. Sai ƙarfe tara ta yi sallama da kowa ta wuce ɗakinta.

  Wurin jakarta ta nufa kai tsaye dan ɗauko littafanta. Ta saba duba takaddunta a kullum kafin ta kwanta bacci, hakan ta yi niyyan yi a yau.

  Sai dai bata kai ga ɗauko littafin ba ta ci karo da wayar Ayman. Sosai ta ji zuciyarta ya buga, tabbas in mahaifiyarta ta ga wannan waya nata ya ƙare. Hakan ya sa ta zaro wayar dan ta kashe amma sai ta ci karo da missed calls da sakonni.

  Sai da ta duba wadanda suka ƙira sannan ta yi niyyar kashewa, sai dai lokaci guda ɓangare na zuciyarta ya bijiro mata da faifan videon wayar.

  Kai tsaye ta shiga folder ɗin da ta gani kwanaki. Sabbin faifai ta gani mara kyaun gani, bata iya zaban ko ɗaya ba, sai da ta gama artabu da zuciyarta game da budewan.

  Daga ƙarshe ta danna ɗaya daga ciki, tana mai mikewa a ƙafafunta bayan ta zaro earpiece na wayar.

  Idanunta akan wayar har ta isa kan gadonta. Makunnin wutan da ke gefen gadon ta danna ta kashe, ta shige cikin bargo tana jin sassan jikinta na amsar sakon da faifan ke aika mata.

  Mintuna ƙadan ta ji sha'awar da tun haihuwarta bata taba ji ba, duk da kasancewarta mai halitta irin wannan, bata taba samun kanta cikin irin wannan yanayi ba.

  Bata iya aiwata komai ba, saboda bata san me ya dace ta yi ba, bata san komai game da abunda take ji ba bare wani tunani ya zo mata.

  Ƙarewar faifan yasa ta fadawa cikin wani faifan, wanda ya ƙara ɗaurata kan sabon mizanin sha'awarta.

  Bata san ya aka yi ba, ita kanta bata san me take aikatawa ba, ta dai san ta ji zuciyarta na kwadaitar da ita samun wannan jin dadin, wanda kwakwalwarta ya hasasho mata hannunta kamar yanda ɗaya daga cikin wadanda ke cikin faifan take amfani dashi.

  Tabbas ta ji zafi a wannan ɓangaren a farko saboda rashin sabo, sai dai bai hanata ci gaba da aiwatar da aikinta ba, a yanda take jin gangar jikinta, ba za ta iya sarrafa kanta ba, ba za ta iya hana kanta ba.

  Ya kawo mata dadin da bata taba sani ba, ta yi mamakin yanda aka yi ta iya aikata hakan, kuma tabbas ta yi mamakin yanda aka yi wurin ya iya daukar hannunta.

  Bata daina ba, har sai da ta gamsar da kanta, tana jin duniyarta yana canjawa. Idanunta a lumshe bayan ta danna wayar ta kashe.

  Mintuna talatin da afkuwar hakan, ta mike a ƙafafunta tana mai gyara zaman skirt nata. Ta mayar da wayar cikin jakarta, ta shige ban ɗaki tana mai sakar wa kanta ruwan zafi.

  *****

  A kwanakin weekend ɗin nan, aikin Juwairiyya kenan kullum da dare in ta zo bacci, a lokacin bata san me sunan aika-aikar ba, bata san hukuncinsa ba, bata san illarsa ba bare ta yi ƙokarin hana kanta.

  A ranar da ta mayar masa da wayarsa, tunanin abubuwan da take kallo kadai ta yi amfani da, wurin aiwatar da wannan aiki nata.

  Daga ranar ta samu aikin yi, ta fara kadaicewa ita kadai a ɗakinta. Duk da mahaifiyarta ta lura da hakan har ta yi mata maganar, amma bai hanata ci gaba da aikinta ba.

  Tana aji biyar a sakandare mahaifinta ya saya mata dankarareriyar waya ta fara WhatsApp.

  A nan ta samu ci gaba da samun labaran batsa, wanda yake ƙara mata ƙaimi da aiwatar da istimna'i.

  Kwanaki kadan ta ji son kallon faifai irin na Ayman na bijiro mata, hakan yasa ta shiga laluben yanar gizo, har sai da ta gano inda zata iya kallo a saukake.

  A ranar da ta fara jin haramcin masturbation a Islamiyyarsu, ta yi kuka har ta gode Allah.

  Ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, ta sha yin alwashin daina wannan aikin, amma duk lokacin da ta ci karo da labaran Hausa ko na Turanci na batsa bata iya hana kanta, shaidani na tasiri akanta sosai, duk da ya hadu da rashin bin ƙa'idan daina istimna'i.

  Ta daina kasancewa da ƙawayenta, saboda wannan aiki. Wani lokaci bata sanin tana yin abu, maganar mahaifiyarta da ƙorafinta ke fargar da ita abunda take aikatawa.

  Saurayi bai dameta ba, ta yi irin soyayyar nan na sakandare, sai kuma irin wanda baza a rasa ba dan kada a ce bata da samari.

  Soyayya ta gaskiya Abdulwahab kadai ya samu daga wurinta, bayan shi babu kowa, kuma tana fatan ya zame mata miji ya kuma tayata tallafar rayuwarta.

  Monday

  Cikin shigarsa ta suit royal blue ya fito rike da brief case nasa, fuskarsa na haske murmushi mamaye da lebbansa.

  Ɗakin mahaifiyarsa ya shiga bayan ya kwank'wasa ƙofar. Ya sameta zaune kamar yanda ya yi tsammani tunda ita ta nemi ganinsa kafin ya tafi office.

  Bata amsa gaisuwarsa ba, bata kalli inda ya ke zaune ba, bare ya sa ran zata yi masa kyakkyawar tarba kamar yanda ta saba a kullum.

  "Dole sai da ka sa Daddy ya amince da auren nan naka ko? Ban isa in gaya maka magana ka ji ba?"

  A dake ta yi masa maganar ba tare da ta dubesa ba, tana maganar ne cike da jin ɗaci a ranta.

  "Mommy ki yi hak'uri, ina so ki fahimceni. Kin sani, nima na sani cewa babu mai bin ra'ayinki na ƙin yin aure da wuri irina a gidan nan. A ganina tunda kika ga na ajiye makamaina na kawo kaina da maganar auren nan a duba a yi min uzuri…."

  "Ba za a yi uzurin ba." Ta furta a fusace tana dubansa.

  "Na ɗauka ka girma kana da hankali ashe baka da wayo Abdul? Aure? A ina zaka ajiye yarinyar? Waye zai mata makaranta tunda kace bata ma gama makaranta ba yanzu take aji biyu. 

  Lokacin da mahaifinka ya zo gareni da neman aurena ina Masters dina a Turkey. 

  Ka san me na sanar dashi? Nace sai na gama, ni mace ma kenan, i was 26years old (ina shekaru ashirin da shida), He was 37 (yana shekaru talatin da bakwai).

  Ya gama makaranta ya yi shekaru almost 10 yana aikinsa. Amma na dakatar da shi saboda bana son in ɗaura masa liability.

  Ban san me yake kanka ba, yaro da kai dan kana ganin ka fara samun pocket money shikenan ka dami kanka sai ka yi aure? Anya Abdul?"

  Kansa a ƙasa, baya tunanin mahaifiyarsa zata gane matsalarsa. Ana maganar jiki da jini wa yake maganar kud'i kuma?

  Shi ya gani yace yana so, me laifi a cikin abunda ya ga zai iya ba tare da taimakon kowa ba?

  "Mommy!" Ya ƙira sunan jin ta gama maganarta.

  "Ki ƙara hak'uri da ni, saboda ina son auren nan wallahi. Zamani ne ya kawo mu, ki karb'i buk'atata ki sa min albarka dan Allah."

  Cikin sauk'ar da kai ya yi mata maganar, hakan ya sa ta tsaya kallonsa tana mamakinsa. Bata iya furta komai ba na 'yan dakiku.

  Daga ƙarshe ta yi ƙarfin halin cewa, "Allah ya kiyaye hanya, ka tafi aikinka kada ka makara." Sannan ta mike a ƙafafunta tana mai basa daman barin ɗakin ba tare da ya furta komai ba.

  *****

  Office

  Ƙarfe takwas ya isa harabar kanfanin, ya ajje motarsa wurin ajiyar motoci. Ya rik'o jakarsa yana jin kwanciyar hankali na mamaye dukkan zuciyarsa.

  A yau da ya kusa samun cikar burinsa, yana jin babu wanda ya kai sa dace da farin ciki a duniya. Komai cikin nutsuwa yake aiwatarwa.

  "Barka da isowa ranka ya dade!"

  Amon muryarta yasa shi waigowa yana kallon fuskarta.

  Bai iya furta komai ba, yanayin shigarta ta doguwar riga da kalar kayan wato blue ya tafi daidai da ra'ayinsa. 

  Daga sama har k'asa ya kalleta, daga k'arshe ya ajje dubansa jikin tag na sunanta da ke mak'ale gefe kad'an da ƙirjinta.

  "Barka dai Hamrah"

  Ya furta bayan ya karance sunanta, yana mai kawar da kansa daga dubanta ya wuce ofishinsa.

  Takalminta da ya kasance flat ta shiga taku a kai, hankalinta na tafiya kan addu'ar da take yi cikin zuciyarta na samun nasara da kuma alhairi cikin sabon aikin da zata fara a yau.

  Baza ta tab'a wasa da wannan dama da Allah ya bata ba, zata ajiye komai gefe guda ta dubi mahaifiyarta da ita kad'ai take samun kwanciyar hankali daga gareta, sai kuma ƙannenta, wad'an da a kullum burinsu su kyautata mata kamar yanda ita ma take kyautata musu.

  Ta yi alwashi zata yi yak'i da duk wanda ya kawo mata cikas cikin abunda ta sa gaba, ba dangin mahaifinta ba bare mahaifiyarta da take da yak'inin baza su takurata ba.

  Zata tabbatar da cewa rayuwar ƙannenta ya tafi yanda kowacce ɗiya take so rayuwarta ya zama, zata zame musu uba, ta basu gata daidai da yanda mahaifinsu ya yi ƙok'arin basu ko ma fiye, idan Allah ya bata iko.

  Da zuciya d'aya ta shiga kanfanin, zata bada lokacinta da iliminta dan bunk'asa kamfanin. Wannan dama da Abdulwahab ya bata, ba zai tab'a da-na-sani ba, saboda ta nemi wannan dama a wurare da dama amma suka rufe ido suka hanata cikar burinta.

  Zamanta a cikin ofishinta, cikin lausashshen kujerar da aka tanada domin ta, ya ƙara bata ƙarfin gwiwa, ya karya mata zuciya da tsantsar farin cikinta.

  Taruwar hawaye a kwarmin idanunta ya sa ta kawar da dukkan tunaninta, tana ajje dubanta akan ƙaramar komfutar da ke gabanta.

  "Hamrah, ki jajirce ki kawar da damuwarki, komai ya zo ƙarshe da izinin Rabbi, zaki iya aiwatar da komai da yardar mahaliccinki."

  Ta furta a fili, ta furzar da iska daga bakinta, tana jin damuwarta, da wannan ƙullutun da ya tokare mata wuya na komawa mazauninsa. 

  Ta danna makunnin na'urar, tana mai bada dukkan hankalinta a kai.

  Wasa-wasa maganar auren Juwairiyya da Abdulwahab ya kankama, mahaifinsa da ƙaninsa suka yi tattaki aka tsayar da magana guda.

  Watanni biyu kacal aka sa, duba da cewa lokacin Juwairiyya na farkon komawa makaranta, shagalin biki ba zai shafi karatunta ba.

  Bayan an sa ranan aurenta sakamakon jarabawarta ya fito, kamar yanda ta yi tsammanin ganin sakamakon hakan ya kasance ko ma ince ya ɗara tunaninta.

  Wacce take samun 4 points a CGPA nata, tayi ƙasa warwas zuwa 2points, ta tabbata ba dan kasancewarta hazika ba, bazata samu 2 ɗin ba ma.

  Bata iya sanar da mahaifiyarta ba, gudun fada da kuma sabon zargi.

  Sai dai hakan bai yu ba, yanda mahaifiyarta take tambayanta dole ta sanar da ita, hakan ya jawo mata sabon kula da sa ido daga mahaifiyarta.

  Tun ranar da ta yi mafarkin nan mai rikitarwa, ta hana kanta komawa ga aikinta, ba dan komai ba sai don tsoro da kuma fargaban abun da zata iska nan gaba.

  Shawarwarin malaminta ta yi ƙok'arin bi, duk da mafi yawan lokaci tana cin karo da littafan batsa a yanar gizo, ba ƙaramin artabu take yi da kanta ba kafin ta iya wucewa, wani lokacin ma wayar take ajjewa gefe guda ta koma wurin mahaifiyarta, sai wannan tunani ya bar kanta sannan ta ɗauko wayar.

  Ƙawayen da take hana kanta zama da su a da, yanzu su ne mutane na uku ko ma dai tace na biyu cikin wad'an da ke ɗauke mata kewa da kuma hanata tunanin da zai iya kaita wannan aiki.

  Karatun Qur'ani da littafai masu anfani kuwa, sun zame mata abokan hira da dare har bacci ya ɗauketa.

  A ɓangaren rashin lafiyarta, ta ga sauyi mai yawa, duk da gashinta bai dawo yanda yake a baya ba, amma bai ci gaba da karyewa ba kamar yanda ya fara.

  Ƙurajen fuskarta tuni suka daina fitowa, ruwan da ke yawan fitowa gabanta ya ragu, wanda a da, ta kan rasa gane wani irin ruwa ne, shin na wanka ne ko kuwa na tsarki ne kawai? Kowanne da kalarsa.

  Hakan sosai yake rikita mata ibadarta, ita kanta bata iya gane shin tana kan daidai ko kuwa.

  Infection nata kuwa, ta gama shanye magungunanta, ta dukufa haikan wurin yin "Kegel exercise", wanda a ganinta zai daidaita mata tsukewar da ta san istimna'i ya bude.

  Sai dai hakan zai yu kuwa? Ita kanta tana tambayar kanta, amma bata saduda ba, ko ba komai Allah ma ji rok'on bayinsa ne, zai gafarta mata kuma ya inganta rayuwarta tunda ta dawo daga rakiyar shaitan da kuma zuciyarta.

  A ɓangaren Abdulwahab kuwa, barin wannan aiki nasa yana matuk'ar yi masa wahala, ba dan komai ba sai don kasa gane inda matsalarsa yake.

  Yanda Juwairiyya ta samu cikakken bayani da kuma yanda zata yi ta daina, shi bai samu hakan ba, hasali ma, bai tab'a kula da abunda yake sa shi fad'awa wannan aiki ba bare ya hana kansa ba, tunaninsa gaba ɗaya ya zauna a kan in ya yi aure komai zai wuce.

  A yanzu da yake hada-hadar biki, baya samun lokacin kansa bare ya afka, sai dai mafi yawan lokaci in ya shiga wanka, abubuwa masu yawa na faruwa, wanda shi baya ɗaukansa a laifi babba.

  Ranar Asabar, ya kama daidai da ranar da za a kai kayan auren Juwairiyya. Sati biyu ya saura zuwa bikinsu a wannan lokaci.

  Dangin Abdulwahab ta wurin uwa da uba suka had'u mak'il, ko wani ɓangare na ji da kud'i da wayewa. 

  Binciken da mahaifiyar Abdulwahab ta yi a kan Juwairiyya da iyayenta bai sa ta karaya da ƙin auren ba, sai dai ta ji dad'in irin zab'en ɗan nata, yarinya daidai da martabarsu da ajinsu a cewarta, sai dai ta yi ƙank'anta, bata so ɗan nata ya ƙare a kanta ba.

  Ƙarfe hud'un yamma suka isa gidan cikin motoci na alfarma. 

  Surayya da ta kasance 'yar aiken mahaifiyar Abdulwahab, bata bar abu guda ya wuce ba tare da ta gani ba dan kai rahoto.

  Tun daga farfajiyar gidan, da tarban da suka samu na karamci, hatta kayan da mahaifiyar Juwairiyya ke sanye da shi sai da ta rik'e dan samun dad'in zance. 

  Tabbas ta jinjinawa zab'in Abdulwahab, ba dan kayan da suka kawo na alfarma bane, da girmansu ya zube a wannan gida a nata tunanin, ganin cima da kayan alatu da ya ƙawata gidan. 

  MashaAllah take furtawa tana jin dad'in zancen da zata je ta zuba wa uwar ɗakinta.

  Akwatuna ne mak'il da kaya set biyu, wanda Mahaifiyarsa ce ta darje ta zab'o duk abunda aka sa cikin wad'an nan akwatuna, bayan ta gama darjewa wurin zab'an akwatunan.

  Ko ba komai ta sayi girma wurin iyayen har ma da matar ɗan nata.

  A ranar Abdulwahab da Juwairiyya sun aminta da samun muradinsu, sun samu zuciyoyinsu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

  Abdulwahab bakin nan nasa ya kasa rufuwa, ya tabbata ya samu Juwairiyya, babu abunda zai shiga tsakaninsu.

  Tuni ya sake dulmiya cikin hidimarsa, wanda shi da abokinsa suke da tabbacin biki ne da baza su manta ba, na kece raini da baza kud'i yanda ya dace.

  Juwairiyya ta kwantar da hankalinta, ta sa hankali wurin gyaran da ake mata, duk da wani ɓangare na zuciyarta na karyewa da sanin cewa bazata iya zama macen nan da bata tab'a samun kanta cikin halin istimna'i ba.

  Ta kan karaya, ta kan zube a gwiwowinta tana rusa kuka cikin rasa makama, da kuma neman abu guda da ya sa ta ɗaura rayuwarta cikin wannan hali. 

  Mafi yawan lokuta tana jin sanar da Abdulwahab zai rage mata wannan tsoro da fargaba, amma shin zai karb'eta a yanda take? Zai bata daraja da mutuncin nan da yake bata a yanzu?

  Ta kan hana kanta furta masa, saboda bata san halin rayuwa ba, wata k'ila ma bazai gane ba. Amma in ya gane ya tunkareta fa? Ta kan amsa wannan tambayar da cewa "Sai in sanar dashi".

  A haka tsoro ya ci gaba da bibiyarta, har satin aure ya kankama, aka shiga shagalin biki na manya, aka watsa kud'i aka yi ɓarinta kamar daga bishiya suka tsinko tsabar dala.

  Kayan sawan amarya da ango kad'ai yana ihun kud'i, barin takalma da hular angon da ya sha bugu irin na Borno mai design na "Akhaiye".

  "Alhamdulillah"

  Take furtawa cikin ranta, ta yi dace, ta samu muradin ranta, ta samu kamilallen miji mai ƙaunarta, ta samu cikar rabin addininta, babu abunda zata sake nema da ya wuce wanda mahaliccinta ya damk'a mata, duk da laifinta garesa.

  Ɓangarensa shima hakan yake, ya yi hamdalan, ya yi addu'an har ma ya nuna tsantsar farin cikinsa a fuskarsa da ya kasa daina ajje murmushinsa a saitinta, idonsa na kanta, duk wani motsi nata yana jinsa har cikin zuciyarsa.

  Ta kammalashi, ta zame masa sarauniya, ita ce sanyin idaniyarsa, abar alfaharinsa da kuma farin cikinsa.

  Daidai kunnenta ya duk'a, dan ba zai iya jure abunda yake ji game da ita ba.

  "You are my happiness. I love you more than life itself".

  Idanunsa ta ɗago idanunta ta kalla, ba sai ta nemi tabbaci da kuma gaskiyar kalamansa ba.

  Idanunsa da ke yalk'i na jifanta da kallon da yake tabbatar mata da gaskiyar sirrin zuciyarsa. 

  Bata haufin soyayyarsa gareta, bata haufi akan duk wani abunda Abdulwahab yake ajjewa a setinta, ita ce dai matsalar, ta kasa ajje masa inda ko wani namiji yake ɗauka da muhimmanci a gangar jikin matarsa, ya zata yi da alhak'in bawan Allahn nan da ta ɗauka?

  Hawaye ta ji yana barazanar sauk'o mata. Hakan yasa ta yi hanzarin kawar da idanunta sannan ta yi ƙok'arin ajje murmushi saman leb'b'anta.

  Haka aka gama wannan shagali cikin kwanciyar hankali.

  Wanda bayan nan aka gangaro ranar ɗaurin aure.

  Da misalin ƙarfe goma da rabi na safiyar Asabar aka ɗaura auren Abdulwahab da Juwairiyya.

  A lokacin da sak'on Abdulwahab ya shigo wayarta, tana duk'unk'une cikin bargo, tsoron daren yau take, tsoron tarwatsewar farin cikinta. Addu'anta bai wuce wannan tabon ya goge daga babin rayuwarta ba, Allah ya ji ƙanta yasa kada ya gano nakasu a wannan ɓangare nata.

  "I love you more. Ameen"

  Kawai ta iya tura masa, bayan ta gama karance dogon sak'on soyayyarsa, farin cikin samunta da kuma addu'ar da ya yi musu na samun zaman lafiya mai ɗorewa.

  Ku biyo ni a ci gaban wannan labari in Allah Ya so.

  Alkalamin Maryamerh Abdul

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Mene ne zazzabin cizon sauro? Zazzabin cizon sauro wato malaria cuta ce da ta ke damun mutanen duniya, musamman mutanen Afrika, kuma wannan cuta tana daya daga cikin cututtukan da suke damun mutanen Nigeria. Tana iya shafar yara, manya, tsofaffi, maza da kuma mata. Ma'anar maleriya Maleriya cuta ...
 • Maza da mata jinsi ne guda biyu mabanbanta da ke da bambancin halaye. Maza da mata suna da yanayi daban-daban, amma da fatan wannan makalar za ta taimaka wajen fayyace abubuwa da samar da kyakkyawar fahimta game da irin wadannan bambance-bambancen.  Ya kamata maza da mata su yaba wa wadannan ba...
 • Ciwon sanyin mata wata babbar matsala ce da ke addabar mata. Akasarin mata na fama da wannan cutar, daga kauye zuwa birni, matan aure da yan mata. Kafin nayi wannan rubutun sai dana tattauna da mata da yawa akan wace cuta ce tafi damun mata a yanzu? Amsar dana samu kuma ita ce 'ciwon sanyi'. Mene n...
 • Mece ce cutar sikila (sickle cell disease)? Jini wanda ake gani a zahiri idan mutum ya ji ciwo ko kuma ya yanke jikinsa yana dauke da abubuwa iri daban – daban, kamar su plasma, Red Blood Cells (RBC), White Blood Cells (WBCs), Platelets da sauransu. Cutar sickler ko amosanin jini tana faruwa ...
 • Brain tumor wani tudun tsiro ne na abnormal cells (wato wasu kwayin halitta) da ke samuwa a kwakwalwan dan adam.  Akwai kala daba-daban na wannan brain tumor din. Wasunsu basa kaiwa ga kansa (benign) sanna wasunsu kuma sukan kai ga zama kansa (malignant). Brain tumor kan fara ne daga kwakwalwa ...
 • Matashiya Zazzaɓin Typhoid (taifod) cuta ce mai saurin yaɗuwa a jiki wacce wata bacteria ce mai suna Salmonella enterica serotype typhi ke haifarwa. Zazzaɓin taifod yana da alamomi wadanda suka shafi cutar kuma suke nunawa. Manya-manyan alamominta sun haɗa da zazzaɓi, da ciwon gaɓoɓin jiki, da yaw...
View All