Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake vanilla cupcakes

Yadda ake vanilla cupcakes

 • Vanilla cupcake kalar cupcake ne da yara kar harma manya su ke so sosai. Na san muta ne da dama suna sha'awar koyon yadda za a sarrafa shi. Saboda haka a yau muka kawo muku yadda ake yinsa domin mai sha'awar koyo. Wannan recipe idan kin bi shi yadda ya ke, za ki samu cupcakes guda 20 ne dai dai.

  Abubuwan hadawa

  1. Flour kofi 2
  2. Baking powder tsp 2
  3. Gishiri tsp ½
  4. Butter kofi 1 (mai laushi sosai wato softened)
  5. Sugar kofi 1 (confectioners)
  6. Coconut milk kofi 1
  7. Kwai 4
  8. Vanilla na gari tsp 2/3

  Yadda ake hadawa

  1. A cikin bowl ki zuba kayan hadinki busassu; flour da baking powder da kuma gishiri da garin vanillarki. Sai ki juya su su hadu da kyau.
  2. Ki saka butter da sugar a bowl ki yi ta juyawa da electric mixer sai sun hadu. Amma idan ba ki da electric mixer za ki iya amfani da whisk (ko wani abin da zai yi mixing da shi) na ki har sai komai ya hudu sun yi laushi.
  3. Ki kawo kwanki ki zuba daya idan kin juya kadan sai ki zuba dayan ma ki juya. Haka har ki kare kwanki guda hudu.
  4. Idan sun dan hadu sai ki kawo coconut milk na ki, ki zuba kadan ki juya sai ki zuba hadin filawarki kadan ki juya. Haka za ki ta yi har sai filawarki da coconut milk sun kare tas. Ki tabbatar kin hada komai sun hadu sosai.
  5. Idan kin gama, ki rika diban kullinki kin a zubawa a cikin cupcake cups na ki. Ki saka daidai, kar ki cika, ki sa ya kai kamar rabi da kwata na kofin din. Sai ki saka a preheated oven na ki (350).
  6. Sai ki sauke bayan minti 20 ko kuma idan kin duba da tsinke ya fita sumul.

  Whip cream

  Abubuwan hada whip cream

  1. Whip cream powder (sachet 2)
  2. Madara na ruwa (full fat) kofi 1
  3. Vanilla na gari tsp ½
  4. Colored sprinkles (cikin hannu)

  Yadda ake hadawa

  1. Ki samu bowl tsukakke mai zurfi, da whisk, da madara, da kuma garin whip cream na ki ki saka su cikin fridge su yi sanyi sosai.
  2. Bayan sun yi sanyi sosai sai ki hada su duka da vanillarki cikin wannan bowl mai sanyi ki ta whisking na su har na tsawon minti 4 ko sai kinga yadda ki ke so.
  3. Ki yi amfani da pipping bag ki yi decorating na cupcakes na ki yadda ki ke so.
  4. A karshe ki watsa sprinkles na ki a kai daidai yadda ki ke so.

  Mai karatu na iya duba girke-girkenmu na baya, kamar su: Yadda ake yoghurt in fruits mix da yadda ake red velvet cake.

  Rubutawa: Rahmatu Lawan

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Maza da mata jinsi ne guda biyu mabanbanta da ke da bambancin halaye. Maza da mata suna da yanayi daban-daban, amma da fatan wannan makalar za ta taimaka wajen fayyace abubuwa da samar da kyakkyawar fahimta game da irin wadannan bambance-bambancen.  Ya kamata maza da mata su yaba wa wadannan ba...
 • Ciwon sanyin mata wata babbar matsala ce da ke addabar mata. Akasarin mata na fama da wannan cutar, daga kauye zuwa birni, matan aure da yan mata. Kafin nayi wannan rubutun sai dana tattauna da mata da yawa akan wace cuta ce tafi damun mata a yanzu? Amsar dana samu kuma ita ce 'ciwon sanyi'. Mene n...
 • Mece ce cutar sikila (sickle cell disease)? Jini wanda ake gani a zahiri idan mutum ya ji ciwo ko kuma ya yanke jikinsa yana dauke da abubuwa iri daban – daban, kamar su plasma, Red Blood Cells (RBC), White Blood Cells (WBCs), Platelets da sauransu. Cutar sickler ko amosanin jini tana faruwa ...
 • Brain tumor wani tudun tsiro ne na abnormal cells (wato wasu kwayin halitta) da ke samuwa a kwakwalwan dan adam.  Akwai kala daba-daban na wannan brain tumor din. Wasunsu basa kaiwa ga kansa (benign) sanna wasunsu kuma sukan kai ga zama kansa (malignant). Brain tumor kan fara ne daga kwakwalwa ...
 • Matashiya Zazzaɓin Typhoid (taifod) cuta ce mai saurin yaɗuwa a jiki wacce wata bacteria ce mai suna Salmonella enterica serotype typhi ke haifarwa. Zazzaɓin taifod yana da alamomi wadanda suka shafi cutar kuma suke nunawa. Manya-manyan alamominta sun haɗa da zazzaɓi, da ciwon gaɓoɓin jiki, da yaw...
 • Yawancin alaƙar soyayya tana farawa, sannan ta haɓɓaka, har ta yi yadon da ba a san dalili ba.  Fadawa cikin soyayya abu ne mai sauki, amma alaƙar na iya zama abu mai matukar wahala duk da irin ababen da mu ke kallo a su Bollywood da Hollywood sai wasu ke ganin kamar babu wani kalubale a tatta...
View All