Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Ilimin Kimiyya » Bayanai game da work done da kuma power

Bayanai game da work done da kuma power

 • A wannan makala dalibai za su ga yadda za a yi bayani game da work da kuma power dama yadda ake solving mathematical problems.

  Workdone ko work a physics yana nufin a yi multiplying na force da displacement. Sa’annan aikin yana gudana ne a direction na force. Idan har W ya kasance work, F kuma force, sa’annan S kuma distance ko displacement. Idan har babu distance da a kayi covering, to work done fa zero ne (0).

  Duk wani object da ke cikin wannan duniya ta mu ta earth yana samun influence na gravity. Wato shi force din yana jan object zuwa centre na earth. Sa’an nan shi earth’s gravitational field yana daga cikin misalan field force. Misali idan za a daga abu sama dole ne a yi aiki ta yarda za a yi overcoming force of gravity. work done is given as;

  Ta yadda m = mass na object, h = height da object ya tsaya, W = work da kuma g = acceleration due to gravity. Ana iya cewa work is done ne idan a kayi anfani da force aka tura object zuwa wani tazara/rata kuma ya kasance ya tafiya ta direction na force.

  Mene ne power?

  Power: Ana iya bayanin sa kamar haka; (a) shi time rate ne na work done. (b) ko kuma muce power shi energy expended a raba shi by time taken. (c) power na nufin work done ne da ya auku a cikin wani lokaci. S. I unit na power shine “watt”. Amma man yan unit kuma sun hada da horse power (h.p)

  Kilo watt (kW) da kuma mega watt (MW) dole ne fa unit unit na power a rubuta shi da manyan baki wato capital letter. Mathematically:

  Mai karatu na iya duba: Darasin physics akan motion force da kuma friction

  Misali na farko:

  A machine is rated 2500 watts. Calculate the power in horse power.

  Ga yadda zamu samo amsar:

  Tunda mun riga mun sani ewa 1h.p = 746W sai muce

   Xh.p =  2500W sai muyi abunda ake kira cross multiplication zamu samu

  1h.p ×2500W = Xh.p ×746W daga nan kuma sai mu samo X

  Aikin gida (Exercise) na daya

  1.How many Watt are in 8h.p.  2) Convert 36000Watt to h.p.

  Interchangeability of energy and work (ana iya anfani da energy a matsayin work).

  Energy da work ana iya  ba su ma’ana  daya. Unit nasu daya . Idan mutum na da energy  kaga zai iya yin wani aiki. Sa’annan kuma idan mutum zai iya yin aiki yana nuna yana da energy. Ba za a iya rabe tsakanin work da energy ba.

  Aikin gida (exercise) na biyu

  1. Define the following: work, energy and power and state their units.
  2. Can energy and work be used interchangeably? Explain.

  Calculation game da work da power

  Misali na biyu:

  A body of weight 300N climbs to the top of a hill of height 20m. What is the work done by the body against the force of gravity?

  Ga yadda zamu samo amsar:

  Da Farko weight = 300N, height (h) = 20m sai kuma muce

  Work = force × distance = mgh

  W = 300 × 20 = 6000j

  Misali na uku:

  An object of mass 12kg is held at a height of 10m above the ground for 15minutes. Calculate the work done within this period.

  Amsa:

  Da farko zamu fitar da abubuwa da aka bamu a tambayan mass(m) = 12kg, height(h) = 10m, time(t) = 15min = 15 × 60 = 900sec. Duk da abubuwa da aka bamu amma tunda object din an rike shi ne ba a bar shi freely ba, g = 0ms . Anan tunda mun sani cewa W = mgh = 12 ×0 ×10 = 0j. Anan zamu iya cewa work done din zero(0).

  Misali na hudu:

  Aikin gida (exercise) na uku:

  1. A 40kg girl climbs upastairs and expends energy at the rate of 50W. Calculate the

  time taken for her to reach a height of 20m.

  Amsa:

  Yadda zamu fara wannan shi ne, tunda mun san cewa potential energy na iya zama dai dai da kinetic energy.

  The greenhouse effect

  Zamu iya cewa greenhouse effect shi ne process by which absorption and emission of infrared radiation by Gases in the atmosphere warm a planet's lower atmosphere and surface. Wanda ya fara kawo magan shi ne Joseph Fourier a 1824, kuma John Tyndall ya gano gaskiyar zancen ne a 1860.

  Zaku iya duba sauran makalunmu kamar su: Bayanan farko-farko da dalibi ya kamata ya sani game da karanta physics, da darasi akan speed velocity da kuma acceleration da makamantansu.

  Rubutawa: Abu Ubaida Adamu

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Maza da mata jinsi ne guda biyu mabanbanta da ke da bambancin halaye. Maza da mata suna da yanayi daban-daban, amma da fatan wannan makalar za ta taimaka wajen fayyace abubuwa da samar da kyakkyawar fahimta game da irin wadannan bambance-bambancen.  Ya kamata maza da mata su yaba wa wadannan ba...
 • Ciwon sanyin mata wata babbar matsala ce da ke addabar mata. Akasarin mata na fama da wannan cutar, daga kauye zuwa birni, matan aure da yan mata. Kafin nayi wannan rubutun sai dana tattauna da mata da yawa akan wace cuta ce tafi damun mata a yanzu? Amsar dana samu kuma ita ce 'ciwon sanyi'. Mene n...
 • Mece ce cutar sikila (sickle cell disease)? Jini wanda ake gani a zahiri idan mutum ya ji ciwo ko kuma ya yanke jikinsa yana dauke da abubuwa iri daban – daban, kamar su plasma, Red Blood Cells (RBC), White Blood Cells (WBCs), Platelets da sauransu. Cutar sickler ko amosanin jini tana faruwa ...
 • Brain tumor wani tudun tsiro ne na abnormal cells (wato wasu kwayin halitta) da ke samuwa a kwakwalwan dan adam.  Akwai kala daba-daban na wannan brain tumor din. Wasunsu basa kaiwa ga kansa (benign) sanna wasunsu kuma sukan kai ga zama kansa (malignant). Brain tumor kan fara ne daga kwakwalwa ...
 • Matashiya Zazzaɓin Typhoid (taifod) cuta ce mai saurin yaɗuwa a jiki wacce wata bacteria ce mai suna Salmonella enterica serotype typhi ke haifarwa. Zazzaɓin taifod yana da alamomi wadanda suka shafi cutar kuma suke nunawa. Manya-manyan alamominta sun haɗa da zazzaɓi, da ciwon gaɓoɓin jiki, da yaw...
 • Yawancin alaƙar soyayya tana farawa, sannan ta haɓɓaka, har ta yi yadon da ba a san dalili ba.  Fadawa cikin soyayya abu ne mai sauki, amma alaƙar na iya zama abu mai matukar wahala duk da irin ababen da mu ke kallo a su Bollywood da Hollywood sai wasu ke ganin kamar babu wani kalubale a tatta...
View All