Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Addini da Tarbiyya » Hukuncin kauracewa Musulmi

Hukuncin kauracewa Musulmi

 • Bismillahir Rahmanir Rahim

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, mai juya zukata yadda Ya so. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ya kwadaitar kan hadin kai, kuma ya hana rarrabuwar kawuna. Kuma ina shaidawa lalle Annabi Muhammad bawan Allah ne, kuma manzonsa ne, wanda ya sanya imani da son juna sababi ne na shiga Aljanna, kuma ya yi hani kan hasada, da kiyayyar juna, da gaba da juna, da juyawa juna baya, da kauracewa juna tsakanin musulmai.

  Haramcin kauracewa Musulmi

  Allah madaukakin sarki Ya umurci Musulmai da su hada kan su, su so junan su, kuma Ya yi hani kada su kauracewa junan su. Saboda haka ne Ya kwadaitar akan duk abinda zai karfafa yan uwantaka tsakanin mutane ta hanyar yada sallama, yin musafaha, kyawawan dabi'u, bada kyaututtuka, ziyartan juna, biyawa mutane bukatunsu, har ma ya sanya yin murmushi ga mutane sadaka ne, za'a samu lada akan yin hakan.

  Haka kuma, musulunci yayi gargadi kan duk abinda zai raba tsakanin musulmai, da kuma abinda zai sanya gaba a tsakanin su, don haka ne ya haramta zagi, da aibantawa, da munana mu'amala, da yin rada, da annamimanci, da mummunan zato, da kauracewa juna, da juya baya ga juna, da sauransu.

  Lalle kauracewa Musulmi yana iya kaiwa ga matakin manyan zunubai, saboda baya halatta Musulmi ya kauracewa dan uwansa Musulmi fiye da kwana uku. An karbo daga Nana Aisha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Baya kasancewa ga Musulmi ya kauracewa Musulmi sama da kwana uku, idan ya hadu da shi sai ya yi masa sallama sau uku, idan duk bai amsa masa ba, to zai koma da zunubi". Abu Dawud ne ya rawaito shi.

  Kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya bayyana cewa wanda ya fara neman sulhu tsakanin masu gaba da junan su, to zai rabauta da samun matsayi mai girma da lada a wurin Allah madaukakin sarki. An karbo daga Abu Ayyub Al-Ansari (Allah Ya yarda da shi), lalle Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Bai halatta ga mutum ya kauracewa dan uwansa sama da kwana uku ba, in sun hadu wannan ya juyawa baya, wancan ma ya juya baya, kuma mafi alherin su shine wanda ya fara (yiwa dan uwansa) sallama". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

  Idan shi da ake gaba da shi ya amsa sallama, to dukkan su zasu yi tarayya cikin lada. Idan kuma ya ki amsa sallama, to shi wanda yayi sallama zai samu ladansa, dayan kuma zai koma da zunubi.

  An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: Lalle Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Bai halatta ba ga mumini ya kauracewa mumini sama da kwana uku, idan kwana ukun sun shude masa, sai ya hadu da shi, to ya masa sallama, idan ya amsa masa, to sun yi tarayya a lada, idan kuma ya ki amsa masa, to hakika zai koma da zunubi, shi kuma mai sallama zai fita daga (laifin/zunubin) kauracewa". Abu Dauda ne ya rawaito shi.

  Masu kauracewa junan su ana haramta musu gafarar Allah lokacin da ake bijiro da ayyukan bayi ga Allah mai girma da dauka a duk ranar Litini da Alhamis. An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: Lalle Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Ana bijiro da ayyuka duk ranar Alhamis da Litini, sai Allah mabuwayi da daukaka Ya gafartawa duk mutumin da baya yin shirka, sai mutumin da ya kasance akwai gaba tsakanin sa da dan uwan sa. Sai a ce: Ku jinkirtawa wadannan har sai sun yi sulhu, ku jinkirtawa wadannan har sai sun yi sulhu". Muslim ne ya rawaito shi.

  A wata riwayar: Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Ana bude kofofin Aljanna duk ranar Litini da Alhamis, sai a gafartawa duk bawan da baya yin shirka, sai mutumin da ya kasance tsakanin sa da dan uwansa akwai gaba, sai a ce: Ku saurarawa wadannan har sai sun yi sulhu, ku saurarawa wadan nan har sai sun yi sulhu, ku saurarawa wadan nan har sai sun yi sulhu".

  Wasu mutane sukan kauracewa junan su na tsawon watanni, ko shekaru, alhali basu sani ba ana jinkirta gafarta musu zunubansu, saboda duk ranakun Litini da Alhamis ana cewa: "Ku saurarawa wadannan har sai sun yi sulhu". Wasu mutane kan gaji gaba daga iyaye da kakanni akan abinda bai taka kara ya karya ba, la haula wa kuwwata illa billahi!!! Lalle duk wanda aka tsayar da gafarta masa zunubansa saboda gaba da yake yi da dan uwansa Musulmi, to yayi asara mai yawa.

  Yanzu da ace misali: ma'aikaci ne aka dakatar da albashinsa na tsawon wata guda, ko na tsawon shekara daya, me kuke tsammanin zai yi don ganin an sako masa albashin sa? Babu shakka zai aikata duk abinda zai iya don ganin an sako masa albashim sa.

  Kauracewa dan uwanka Musulmi babban zunubi ne daga cikin manyan zunubai, saboda akwai alkawarin shiga wuta ga mai aikata shi. An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: Lalle Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Baya halatta ga Musulmi ya kauracewa dan uwan sa Musulmi sama da kwana uku, duk wanda ya kaurace sama da kwana uku sai ya muku, to zai shiga wuta". Abu Dawud ne ya rawaito shi.

  Haka nan, duk wanda ya kauracewa dan uwansa Musulmi na tsawon shekara, to kamar ya kashe ran mumini ne, ina kuma ga wanda yake kauracewa dan uwan sa ko makwabcinsa na tsawon shekaru masu yawa? Ya ya gwargwadon laifin sa zai kasance?

  An karbo daga Abu Khirash As-Sulami (Allah Ya yarda da shi) ya ce: Na ji Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yana cewa: "Duk wanda ya kauracewa dan uwansa na shekara guda, to kamar ya zubar da jininsa ne". Abu Dawud ne ya rawaito shi.

  Idan kauracewa juna ya faru tsakanin yan uwa na jini, to zunubin yana karuwa, saboda ya hada zunubin kauracewa dan uwansa Musulmi, da kuma zunubin yanke zumunci.

  Don haka, ya kai dan uwana musulunci,  ka yi gaggawar neman sulhu da dan uwan ka, hanzarta ka masa sallama, kar ka ce; "ni ne mai gaskiya, shine mai laifi", kuma kar ka ce; "ni ne babba akan sa", da sauran hujjoji mara kan gado. Ka sani mganar gafarta zunubai da karban ayyuka da batun wuta da aljanna ake yi.

  Dan uwa, kaskantar da kan ka, ka yafe abinda aka maka, ka manta da abin ya wuce ka binne shi, kasance mai gaggawa zuwa ga alheri, don ka rabauta da lada mai yawa, in ba haka ba kuma ka kasance cikin wadanda za a rika cewa a hakkinsu duk ranar Litini da Alhamis: "Ku jinkirtawa wadannan har sai sun yi sulhu". Ka gode Allah da ajalinka bai zo ba kana mai husuma da wani daga cikin Musulmai ba tare da wani dalili na shari'a ba.

  Ku duba falalar yan uwantaka a Musulunci.

  Halaccin kauracewa Musulmi

  Musulunci ya haramta Musulmi ya kauracewa dan uwan sa fiye da kwana uku ba tare da wani dalili na shari'a ba. Amma idan an samu sababi na shari'a, to ya halatta a kaurace masa, kamar kauracewa mai aikata sabo, saboda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kauracewa wadanda suka ki zuwa yakin Tabuk. Haka kuma ya halatta namiji ya kauracewa matar sa da take bijire masa.

  Kammalawa

  Muna rokon Allah Ya hada kawunan mu, Ya sanya mu cikin masu son junansu don Allah, Ya kawar mana duk wani abinda zai jawo mana rarrabuwar kai, Ya tsarkake mana zukatan mu.

  Rubutawa: Dr. Kabiru Adamu Lamido Gora

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Kansar mafitsara na daga cikin ire-iren kansa da su ka yawaita a cikin al’umma. Ita kansar mafitsara kamar yadda sunanta take ta na farawa ne daga cells din mafitsaran mutum. Mafitsara dai kamar yadda muka sani wani ma’aji ne a can kasan cikin mutum wadda amfaninsa shi ne adana fitsari. ...
 • Kansar mama ko cutar daji cuta ce ta kansa da take yaduwa a cells din nonuwar mace (breast). Baicin kansar fata (skin cancer), kansar mama ita tafi ko wacce irin kansa da mata ke dauke da ita a kasar Amurka. Kansar mama na iya kama mace ko na miji amma ta fi kama mata nesa ba kusa ba akan maza. Yad...
 • Bismillahir Rahmanir Rahim Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, mai juya zukata yadda Ya so. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ya kwadaitar kan hadin kai, kuma ya hana rarrabuwar kawuna. Kuma ina shaidawa lalle Annabi Muhammad bawan Allah ne, kuma manzonsa ne, wanda y...
 • A karkashin ilimin kimiyyar lissafi wato (physics), yau zamu yi karatu ne akan wata maudu’i mai matukar mahimmanci. Wannan maudu’in kuma ba wata ba ce face heat. Idan muka tuna a makalar da ta gabata mai suna energy mun ce heat nau’i ne daga cikin nau’ukan energy. A yau zamu ...
 • A wannan makala dalibai za su ga yadda za a yi bayani game da work da kuma power dama yadda ake solving mathematical problems. Workdone ko work a physics yana nufin a yi multiplying na force da displacement. Sa’annan aikin yana gudana ne a direction na force. Idan har W ya kasance work, F kum...
 • Vanilla cupcake kalar cupcake ne da yara kar harma manya su ke so sosai. Na san muta ne da dama suna sha'awar koyon yadda za a sarrafa shi. Saboda haka a yau muka kawo muku yadda ake yinsa domin mai sha'awar koyo. Wannan recipe idan kin bi shi yadda ya ke, za ki samu cupcakes guda 20 ne dai dai. Ab...
View All