Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Cutar kansar mama: Hatsarurruka da hanyoyin kariya daga cutar

Cutar kansar mama: Hatsarurruka da hanyoyin kariya daga cutar

 • Kansar mama ko cutar daji cuta ce ta kansa da take yaduwa a cells din nonuwar mace (breast). Baicin kansar fata (skin cancer), kansar mama ita tafi ko wacce irin kansa da mata ke dauke da ita a kasar Amurka. Kansar mama na iya kama mace ko na miji amma ta fi kama mata nesa ba kusa ba akan maza.

  Yadda shirye-shiryen wayar da kai da kuma kudade da ake kashewa wajen bincike game da wannan cutar ya sa anci gaba kwarai ainun wajen ganowa da kuma jinyar wannan cuta. Mutane da suke warkewa daga wannan cutar sun karu sosai. Sannan yawan mutuwa daga cutar ya yi kasa, yawanci sabili da ana gano suna dauke da cutar da ake yi da wuri da kuma sabon hanyar da ake bi na jinya da kuma ci gaba na fahimtar cutar.

  Ire-iren cutar kansan mama

  1. Angiosarcoma
  2. Ductal carcinoma in situ (DCIS)
  3. Inflammatory breast cancer
  4. Invasive lobular carcinoma
  5. Lobular carcinoma in situ (LCIS)
  6. Kansar mama na maza (male breast cancer)
  7. Paget’s disease of the breast
  8. Kansar mama da kan tafi ta dawo (recurrent breast cancer)

  Alamomin kansar mama

  Alamomin cutar kansar mama sun hada da:

  1. Dan gudaji ko wani kauri (lump or thickening) da za a ji shi wadda ya yi daban da sauran bangaren maman
  2. Canji na girman mama, ko fasalin shape na shi ko kuma yanayin maman
  3. Canji na wani bangaren fatan maman kamar kan maman wato nipple
  4. Shiga ciki ko lotsewar bakin mama (inverted nipple)
  5. Barewa fatan nono, ko bambarowar fatan ko kuma zuban burdi-burdin fatan mama ko kuma na bakin maman
  6. Canzawar kalar fatan nono zuwa dan ja-ja haka kamar bawon lemu.

  Yaushe ya kamata a ga likita?

  Idan aka ji dan gudaji-gudaji ko dunkule(lump) ko wani canji na daban a mama (ko da an taba yin gwaji ba da jimawa ya nuna ba komai). A garzaya zuwa asibiti domin a sake dubawa.

  Dalilan da ke kawo cutar kansar mama

  Likitoci su kan san cutar kansar mama ta shiga ne idan cells na nono suka fara karuwa ba yadda ya kamata ba (abnormal growth of breast cells). Su wadannan cells su kan rarrabu ne akai-akai su ta taruwa suna yawa fiye da yadda normal cells su ke rarrabuwa. A sakamakon wannan taruwa na yawan cells din sai a sami lump ko gudaji a nono. Sannan cells za su iya yaduwa daga mama zuwa lymph nodes (wasu hanyoyi ne da ke jikin dan adam masu tace sinadarai da ke cutarwa a jiki). Ko kuma su yadu zuwa wasu fannoni daba-daban na jiki.

  Yawa yawanci kansar mama na farawa ne da cells a cikin bututun da ke kawo ruwan nono (invasive ductal carcinoma). Wani lokacin kuma ta kan fara ne da ga wani tissue da ake kira da Turanci, lobules (invasive lobular carcinoma), ko kuma a wasu tissue ko cells na daban da ke cikin nono.

  Masana masu bincike sun gano cewa wasu dalilai kamar hormone, ko yadda mutum ke tafiyar da rayuwarsa da kuma muhalli suna iya kara hatsarin kamuwa da cutar kansar mama. To amma har yanzu an gagara gano hakikanin dalilan da ke sa mutane da ba su da wadannan hatsari ke iya kamuwa da wannan cutar, sannan wasu kuma da ke da wanndan nan hatsari ba su kamuwa da ita. Saboda haka masana suke gani watakila dai cutar kansar mama ta na samuwa ne idan aka samu hulda mai sarkakiya (complex interaction) na kwayoyin halittan mutum da kuma muhallinsa.

  Cutar kansar mama ta gado

  Likitoci sun yi kiyasin cewa kamar kashi biyar ne izuwa kashi goma na masu kamuwa da cutar kansar mama suke gado daga iyaye ko ma kankanninsu.  

  An gano wasu ‘yan kwayoyin halittan gado da ke bin zuri’a (inherited mutated genes) wadanda aka alakanta su da jefa masu shi hatsarin kamuwa da cutar kansar mama. Wadanda aka fi sani su ne breast cancer gene 1 (BRCA1) da kuma breast cancer gene 2 (BRCA2). Dukka wadannan biyun suna jefa masu shi hatsarin kamuwa da cutar kansar mama da ovarian cancer.

  Saboda haka idan mutum na da tarihi na yawan masu dauke da cutar kansar mama a zuri’ansu to likita kan sa a yi gwajin specific mutations in BRCA or other genes wadanda aka gado daga iyaye da kakanni.

  Kwararu na ba da shawaran cewa, mutum ya bukaci likitansa ya tura shi (referral) wajen genetic counselor, wadda zai taimaka ya bincika tarihin lafiyar zuri’an mutum. Shi wannan censelor din zai tattauna da mara lafiya game da amfani, da hatsarurukan da kuma iyakokin gwajin kwayar halitta (genetic testing) domin taimakawa mara lafiya wajen daukan mataki.

  Mai karatu na iya karantaBayanai game da lalurar autism spectrum disorder (galhanga)

  Karin dalilan da ke kara hatsarin kamuwa da cutar kansar mama (risks factors)

  Duk wani dalilin da ke karawa mutum shiga hatsarin kamuwa da cutar kansar mama shi ake kira da breast cancer risk factor. Amma don mutum na da wani ko ma wasu risks factors ba yana nufin cewa lallai-lallai mutum sai ya kamu da wannan cuta ba ne. Da yawa da ga matan da suka kamu da cutar kansar mama ba su ma da wani hatsarin da aka sani yana haddasa cutar kansa sai dai kawai kasancewar su mata ne.

  Hatsarurruka da ake alakantawa idan mutum na da su to yana da high breast cancer risk factors sun hada da:

  1. Kasancewar ke mace ce. Mata su suka fi kamuwa da cutar kansar mama fiye da maza nesa ba kusa ba.
  2. Yawan shekaru. Yawan shekaru na kara shigar da mutum hatsarin kamuwa da cutar kansa
  3. Idan mutun na da tarihin ciwo ko wani condition da ya shfi mama. Idan mutum ya taba yin abinda ake kira da breast biopsy kuma aka sami abin da ake kira da Turanci lobular carcinoma in situ (LCIS) ko atypical hyperplasia of the breast, to akwai hatsarin kamuwa da cutar kansar mama.
  4. Idan mutum na da tahirin kansar mama shi karan kansa. Misali idan mutum na da kansar a daya nono to saura daya nonon ma na da hatsarin kamuwa da kansar.
  5. Tarihin cutar kansar maman a zuri’an mutum. Idan mahaifiyar mutum, ‘yar mutum, ko kanwar mutum sun taba cutar kansar, musamman idan suna da karancin shekaru lokacin da aka gano, to mutum na da hatsarin kamuwa da cutar.
  6. Gadon wasu irin kwayan halitta: Wasu kwayin halitta idan mutum ya gaje su to yana iya shiga hatsarin kamu da cutar kansar mama. Gene mutations da ake fi sani, kamar yadda muka fada baya, masu shigar da mutum hatsarin kamuwa da kansar mama su ne BRCA1 AND BRCA2.
  7. Kasancewar mutum ya taba zama exposed to radiation. Idan an taba yi wa mutum jinya da radiation a kirji, musammam idan mutum na yaro ne ko dai matashi ne shi to hatsarin kamuwa da cutar kansar mama ya karu a gare shi.
  8. Kiba fiye da kima (obesity). Kiba fiye da kima na karawa mutum hatsarin kamuwa da cutar kansa.
  9. Fara al’ada da wuri. Idan yarinya ta fara al’ada kasa da shekara sha biyu, to wannan zai kara mata shiga hatsarin kamuwa da cutar kansar mama.
  10. Jinkirin barin yin al’ada (menopause). idan mace ta yi jinkirin barin al’ada, to hatsarin kamuwar kansar mama ya karu a gare ta.
  11. Haihuwan fari a shekarun girma (older age). Mace da ta haifi danta na fari a lokacin da ta ke sama da shekaru 30, to hatsarin kamuwa da cutar kansar mama ya karu.
  12. Macen da ba ta taba ciki ba. Idan mace ba ta taba ciki ba a rayuwar ta, to wannan dalili na iya saka ta a hatsarin kamuwa da cutar kansar mama fiye da wacce ta taba yin ciki koda sau daya ne.
  13. Jinya ko shan magani don gyaran hormone lokacin barin al’ada (Postmenopausal hormone therapy). Matan da ke shan magani mai dauke da sinadarin estrogen da progesterone lokacin menopause suna shiga hatsarin kamuwa da breast kansa. Sannan lokacin da suka bar shan wannan magani ma hatsarin kuma na karuwa.
  14. Shan giya. Mutum mai shan giya na kara shiga hatsarin kamuwa da cutar kansar mama.

  Duba wannan:Coronavirus: Mece ce ita kuma ya ya za a kare kai daga kamuwa da ita

  Hanyoyin kariya daga kamuwa da cutar

  Kula ta yadda ya kamata da yanayin da ake rayuwa na iya ragen hatsarin kamuwa da cutar kansar mama. A kula da:

  1. Yin magana da likita don sanin lokacin da ya kamata mutum ya fara breast cancer screening. Ku tattauna da likita domin sanin lokacin da ya kamata a yi screening exam da test kamar su clinical breast exams da mammograms. Ku yi magana da likita akan amfani da kuma hatsarin da ke tattare da screening. Sannan sai ku yi deciding kai/ke da likta akan zabin abinda ya dace.
  2. Sanin yadda nononki ya ke da kanki ta hanyar dubawa da kuma kula da shi. Yin haka zai sa idan akwai wani canji za ki iya ganowa da wuri kuma ki nemi taimako.
  3. Rage shan giya ga masu shan giya.
  4. Motsa jiki a yawancin kwanaki (exercise most days of the week)
  5. Mace ta rage yawan yin postmenopausal hormone therapy. Idan mace na bukatan yi to ta nemi shawara sosai na kwararrun likitoci.
  6. A tabbatar da an kula da hada kiba fiya da kima
  7. Cin abinci masu amfani da lafiya (healthy diet)

  Kariya ga mata masu hatsari sosai (high risk factors) na kamuwa da cutar kansar mama

  Idan likitan ki ya duba tarihin zuri’arki ya tabbar kina da hatsarin kamuwa da kansar mama sanan kuma akwai wasu dalilai na kamuwa da cutar kansar to yana da kyau mace tattauna da likita domin ganin ta bi yanyoyin da suka kamata domin kariya. Wasu daga cikin hanyoyin sun hada da:

  1. Yin maganin kariya (preventive medications or chemopreventions)
  2. Yin tiyatar kariya (preventive surgery). Tiyatar cire nono mai lafiya domin kariya da sauransu.

  Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya. Ga mai sha’awar karanta wannan Makala da Turanci, dubi wannan.

Comments

1 comment