Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Kansar mafitsara: Ire-ire da hanyoyin kariya da kamuwa da ita

Kansar mafitsara: Ire-ire da hanyoyin kariya da kamuwa da ita

 • Kansar mafitsara na daga cikin ire-iren kansa da su ka yawaita a cikin al’umma. Ita kansar mafitsara kamar yadda sunanta take ta na farawa ne daga cells din mafitsaran mutum. Mafitsara dai kamar yadda muka sani wani ma’aji ne a can kasan cikin mutum wadda amfaninsa shi ne adana fitsari.

  Yawayawan lokaci kansar mafitsara na farawa ne daga cells (urothelial cells) da ke kewaye ta cikin ita wannan mafitsaran. Su waddannan irin cells din na Urothelial cells din ana samun su ne a koda (kidney) da kuma maguda (tubes) da suka hada koda din da mafitsaran. Saboda haka wannan kansa (urothelial cancer) ta kan iya samuwa ma a koda ko kuma a wannan maguda (tube) amma dai ta fi faruwa a mafitsara.

  Yawanci ana gano kansar mafitsara da wuri ne wato daga ta fara kama mutum, a lokacin idan aka yi jinyarta za ta warke. To amma mu sani cewa ko da an gano kuma aka yi jinyar ta da wuri ta kan iya dawowa. A sabili da wannan dalili mutanen da suka taba kamuwa da irin wanan kansar ko da sun warke ne, to ana son su ci gaba da bibiyar kwaji na ‘yan shekaru domin kaucewa dawowarta. Har idan ta dawo a sake dakusheta da wuri.

  Hakkin mallaka: Mayo Clinic

  Alamun kansar mafitsara

  1. Jini a cikin fitsari (hematuria). Jini a cikin fitsari kan saka fitsarin ya yi kalar jaja mai haske ko kuma kamar kalar coca cola haka. Sannan wani lokacin ma mutum ba ya ganin jinin da idonsa sai dai idan an gwada a lab ake iya ganin jini a ciki.
  2. Yawan yin fitsari
  3. Jin zafi ya yin fitsari
  4. Ciwon baya

  Yaushe ya kamata a ga likita?

  Idan mutum ya ga fitsarinshi ya yi kala-kala kamar na jini, ko da kuwa kana kokwanto ne, to garzaya ka je ka ga likita domin a duba. Sanna ba wai kawai sai ka ga alamun jinin ba ko da kuwa wasu daga cikin alamun da muka lissafo ne a sama mutum ke ji ko gani to a je a ga likita.

  Duba: Cutar kansar mama: Hatsarurruka da hanyoyin kariya daga cutar

  Abubuwan da ke kawo cutar kansar mafitsara

  Kansar mafitsara na farawa ne idan cells suka fara canzawa (mutations) a DNA su. DNA na cells suna tattare da wasu abu kamar instruction ne da su ke shaidawa cells ga abinda za su yi. To wannan canji da ke faruwa kan shaidawa cells cewa su karu sosai domin su rayu ya yin da wasu lafiyayun cells za su mutu. Saboda da haka, su abnormal cells sai su taru su yi forming tumor wadda za su tarwatsa normal body tissue. A dan lokaci sai wadannan abnormal body tissue din su tarwatsa su bazu a cikin jiki.

  Hakkin mallaka: Mayo Clinic

  Ire-iren kansar mafitsara

  Cells iri daban-daban ne da ke cikin mafitsaran mutum wadda za su iya rikidewa su zama kansa. To irin cells na mafitsara (type of cell) da kansar ta fara kamawa shi ke determining irin kasar mafitsaran da zai samu mutum. Likitoci na amfani ne da waddanan bayanai domin tantance irin jinyan da ya kamanci mutum. Iri-iren kansar mafitsaran sun hada da:

  1. Urothelial carcinoma. A da ana kiran wannan da suna transitional cell carcinoma, ta na faruwa ne da cells din suka kewaye cikin mafitsara. Urothelial cells suna saka mafisara ya budu ne a lokacin da ya ke cike, sannan yana motsewa ne a yayin da ba komai a cikin mafitsarar. Saboda haka wadannan cells na urothelial cells din da suke haduwa su yi layi a cikin mafitsarar su ke forming kansa. Wannan irin kansar ta fi ko wani irin kansar mafitsara yawa a Amurka.
  2. Squamous cell carcinoma. Ita wannan squamous cell carcinoma ana danganta ta ne da tsananin irritation na mafitsara, misali daga infection ko kuma tsayin amfani da abin tsiyayo fitsari wato urinary catheter. Kansar mafitsara na squamous cell ta na da karanci a kasar Amurka. Ta fi yawa a bangaren duniya da su ke da wasu irin parasitic infection (schistosomiasis) wanda yawanci ana samun shi ne a wurin wanka da yara suke yi tun suna kanana sai can bayan sun girma sai abun ya zama irin wannan kansar.
  3. Adenocarcinoma. Wannan irin kansar mafitsaran kan fara ne daga cells masu fidda abu kamar majina da ke mafitsara wato mucus secreting glads. Ita ma wannan kansar tana da karanci kwarai.

  Wasu kuma kansar mafitsaran sun kun shi cell types fiye da daya.

  Mai karatu na iya karanta: Mene ne ku ka sani game da covid-19 antibody test

  Dalilan da ka iya jefa mutum ga a hatsarin kamuwa da kansar mafitsara (risk factors)

  1. Shan taba. Shan taba sigari da danginsa zai iya kawo cutar kansar mafitsara saboda yana tara chemicals masu cutarwa a cikin fitsari. Idan mutum ya sha taba jikinsa na processing chemical da ke cikin hayakin sannan ya fitar da wasu da ga cikin fitsari. Su wadannan chemicals din kan yi wa mafitsaran illa wadda hakan ke iya jefa mutum cikin hatsarin kamuwa da kansa.
  2. Idan shekaru na karuwa. Hatsarin kamuwa da cutar kansar mafitsara na karuwa idan mutum na girma. Duk da cewa cutar na iya kama mutum ako da yaushe, ammam yawancin mutane da ake samu da cutar kansar mafitasra sun dara shekaru 55 a duniya.
  3. Kasancewa mutum na miji ne. Maza sunfi zama cikin hatsarin kamuwa da cutar kansar mafitsara fiye da mata.
  4. Idan mutum ya zama expose da wasu chemicals. Kamar yadda muka sani kodarmu ta na da matukar muhimmanci wajen tace chemicals masu cutarwa da ga hanyar jini zuwa mafitsara. T amma saboda wannan aiki da koda ke yi ana gani wannan ya sa shiga hatsarin kamu da cutar kansar mafitsaran ya karu. Chemicals da ake alakanta su da cutar kansar mafitsara sun hada da, arsenic, chemicals da ake amfani da su don yin dyes, da roba, da leda, da kayan textiles da kuma kayan fenti.
  5. Jinyar kansa da ta wuce: Idan mutum ya taba amfani da maganin kansa irin cyclophosphamide to ya na hatsarin kamawu da kansar mafitsara. Sannan haka mutane da aka musu radiation treatment na pelvis na wata cutar kansar da ta gabata to lallai wannan mutumin na da hatsarin gaske na kamuwa da wannan irin kansa na mafitsara.
  6. Tsananin kumburin mafitsara (chronic bladder inflammation). Tsanani ko jeka-ka-dawo na urinary infection ko kumburi wato inflammation (cystitis) wadda ke saka mutum ya ta amfani da bututun fitsari (urinary catheter), na tsayin lokaci, zai iya jefa mutum a hatsarin kamuwa da kansar mafitsara na squamous cells.
  7. Idan mutun ko zuri’an shi su na da tarihin kansa. Idan mutum ya taba kamuwa da cutar kansar mafitsara to yana da hatsarin sake samun cutar. Sannan idan wani daga cikin zuri’an mutu, kamar iyaye, ko kanne’ ko yayyu, ko ‘ya’ya, sun taba kamuwa da wanan cuta, to hatsarin kamuwa da cutar ya kan karu akanka. Duk da cewa dai ita wannan kansar ba ta fiye bin zuri’a ba. Sannan idan zuri’an mutum suna da tarihin cutar nan da ake kira da lynch syndrome (hereditary nonpolyposis colorectal cancer) yana karawa mutum hatsarin kamuwa da kansa mafitsara.

  Hanyoyin kariya

  Duk da cewa ba wani hanya da za a iya cewa lallai-lallai zai kare mutum da kamuwa da cutar kansa mafitsara, to amma mutum na iya bin wasu matakai na rage hatsarin kamuwa da cutar. Ga wasu daga cikin hanyoyi kamar haka:

  1. Mai shan taba ya bar sha, wadda kuma bai fara ba kar ya fara.
  2. A kiyaye hulda da chemicals. Idan kuma aikin mutum ya danganci hulda da chemicals to abi duk hanyoyin kariya na amfani da wannan chemicals din.
  3. Chin kayan itace da ganyayyaki daban-daban. Antioxidant da ke cikin kayan itace da kuma ganyayakin na iya kare mutum da shiga hatsarin kamuwa da kansar mafitsaran.

  Daga karshe, kamar kullum kar ku manta muna kawo muku ire-iren wannan makala ne domin karuwan ilimi da kuma wayar da kai. Idan mutum na fama da ciwo ko ya ga wani alamu na ciwo, to likita shi ne kadai zai duba ka kuma ya baka magani. Allah Ya mu lafiya da zaman lafiya.

  Ku dubaCutar asma: Alamominsa, illolinsa da kuma hanyoyin kariya daga cutar

  Don karanta wannan makala da harshen Turanci latsa nan

Comments

4 comments