Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Mece ce cutar eclampsia?

Mece ce cutar eclampsia?

 • Eclampsia cuta ce mai matukar wahala. Yanayi ne mai wuya da tsanani wanda cutar hawan jini ke haifarwa a lokacin da mace ta ke da ciki. Cuta ce da kan  saka girgizan jiki mai ƙarfi wato seizure. Cutar eclampsia tana shafar kusan daya cikin mata 200.

  Mene ne alamun cutar eclampsia?

  Saboda pre-eclampsia na iya haifar da eclampsia, ƙila kina da alamun ko yaya ne. Wasu alamun cutar na iya zama saboda wasu matsaloli, kamar cutar Ƙoda ko ciwon sukari.  Yana da mahimmanci ki gayawa likitanki game da duk yanayin da kike ji.

  Wasu daga cikin alamu na yau da kullun game da wannan cutar eclampsia

  1. Hauhawar jini
  2. Kumburi a fuska ko hannun
  3. Ciwon kai
  4. Tashin zuciya da amai

  Me ke kawo cutar eclampsia?

  Eclampsia sau da yawa yana bin pre-eclampsia, wanda ya ke zuwa tare da hawan jini lokacin da mace ke da ciki sannan ya kan sauka bayan haihuwa.  Ana iya yin bincike kamar su furotin a cikin fitsari. Idan pre-eclampsia ya yi yawa ya kan shafi kwakwalwarka, sannan kuma eclampsia ta biyo baya.

  Hawan jini

  Pre-eclampsia shine lokacin da karfin jini ya yi yawa a bangon jijiyoyi hakan sai ya lalata sauran hanyoyin jini.  Lalacewar jijiyoyin sai yasa a samu ƙunci na rashin gudanar jini. Hakan zai iya samar da kumburi a cikin jijiyoyin jini, a kwakwalwar da kuma ga jaririn dake kwance a mahaifar uwa.

  Proteinuria

  Ciwon ciki mai tsanani wanda zai shafi ƙoda har aikinta yai rauni.  Protein a cikin fitsarin, wanda aka fi sani da proteinuria, alama ce da ke nuni da wata matsala. 

  Yawanci, koda ita ke tace datti daga cikin jinin kuma su fitar da fitsari daga waɗannan dattin, kuma su  riƙe abubuwan da zasu taimaka wajen gina jiki a cikin jini, kamar furotin, don sake rarrabawa ga jikin. Idan wasu abubuwa da ake kira glomeruli, sun lalace, furotin na iya zubewa ta cikinsu kuma sai a samu fitsari.

  Ku duba wannan Makala: Yadda za a rage sugar a cikin jini ba tare da shan magani ba

  Mene ne maganin eclampsia?

  Likita zai yi la’akari da tsananin cutar da kuma yadda girman jaririnki ya ke yayin bada shawarar lokacin haihuwa.

  Conditions of eclampsia

  Idan likita ya binciko cewa akwai pre-eclampsia, zai yi ƙoƙari da kula da yanayin matar sai a bata magani don hana shi juyawa zuwa eclampsia.  Magunguna da kuma kulawa su za su taimaka kiyaye yawan hawan jini da za a dinga samu har zuwa lokacin da jaririn ya isa haihuwa. Babu dacewa a bar mace mai fama da irin wannan matsala gida dole ta kasance asibiti don bata kulawar da ya kamata.

  Eclampsia na da wasu associated conditions wato wasu yanaye-yanaye waɗan da mai fama da ita zai iya gabatar da su  as symptoms ko standard alone condition.  Waɗan nan alamomi sun haɗa da:

  Edema: Kumburin jiki wanda ke haifar da tarin ruwa a cikin  takarda.  Wannan zai sa ka ga mutum ya samu swelling ga extremities ɗinsa

  Pulmonary Edema: Yana haifar da taruwar fluid ga huhu, wanda ke  haifar da wahalar numfashi (difficulty in breathing).

  Ciwon kai: Wannan ciwon kai hawan jini ne ke haifarwa saboda eclampsia

  Gestational diabetes: Alamomin da ya ke nunawa saboda samuwar juna biyu tare da haɗuwar canjin abinci da magani.  Kamar yadda aka fada a baya, kowane lamari na eclampsia daban yake. 

  Masu bincike ba su gano ainihin dalilin wannan yanayin ba.  Kowane al'amari na eclampsia daban ne, kuma mace mai ciki na iya kamuwa da waɗan nan alamomin ko kuma wasu can daban.

  Idan kuka duba a wannan makala da muka yi a baya game da wannan lamari za ku ga cewar mun mai da hankali ne kan ƙayyade abubuwan haɗarin kamuwa da cutar tun da wuri don hanawa ko hango ci gaban yanayin daga baya.

  Abubuwan masu hatsari ga cutar pre-eclamsia da eclampsia

  Abubuwa masu haɗari ga cutar Pre-eclampsia da eclampsia zasu bambantai.  Abubuwan da suka kamata a kula dasu sune:

  1. Pregnancy History: Yawancin lokuta lalurar eclampsia na faruwa a farkon ɗaukar ciki. Poor outcome na iya ƙara haɗarin kamuwa da cutar eclampsia.
  2. Patient age: Mata masu ciki da basu haura shekara 12-22 (Teenage years) da sama da 35 suna da haɗarin kamuwa da cutar eclampsia.
  3. Family history wato: Matsalolin preeclampsia ko eclampsia a cikin dangi na iya nuni da matsalar ce ta gado.
  4. Obesity: Mata masu kiba suna da haɗarin kamuwa da cutar eclampsia fiye da kowa
  5. Hypertension: Marasa lafiya da ke fama da cutar hawan jini na dogon lokaci suna cikin haɗarin kamuwa da cutar eclampsia.

  Symptoms (alamun bayyanan cutar)

  Alamomin cutar eclampsia na iya ɓulla ko wane lokaci yayin daukar ciki.  Hakanan akwai wasu alamun ƙalilan, waɗan da ke haifar wa mace da ciwon eclampsia ba tare da likitocin kiwon lafiya sun gano ta ba. Mafi yawan alamun cututtukan mace mai ciki sun haɗa da, tashin zuciya, da amai, ko ciwon ciki, da hada kiba lokacin juna biyun wadda kan wuce 2 pounds cikin sati biyu, da kumburin hannu, da ƙafa, da kuma fuska.

  Idan cutar pre-eclampsia ta tsananta har ya zama eclampsia, alamomin zasu iya haɗawa da: Ciwon jiki haka wato muscle pain da fisfisgewa wato seizure

  Babu magani ga cutar Pre-eclampsia sai haihuwar jariri.  Idan an samo shi da wuri, ana iya maganin hawan jini.  Hakanan za'a iya amfani da magungunan hana yaduwar cuta don hana kamuwar cutar daga Pre-eclampsia zuwa eclampsia.

  Jinyar cutar eclampsia

  A baya, matan da ke fama da rikice-rikicen cuta saboda eclampsia masana kiwon lafiya suna umurtarsu da aspirin a kullum bayan makonni 12 na ciki.

  Hanya guda daya tak da za a warkar da alamun eclampsia ita ce lokacin haihuwa. Barin ciki ya ci gaba ba tare da an fitar da yaro a mahaifa ba ga matar da ke da cutar eclampsia na iya haifar da matsolili masu hatsarin gaske.

  A mafi yawan lokuta alamun eclampsia suna warwarewa tsakanin makonni 6 bayan haihuwar jariri.  A wasu lokuta ba safai ba, ana iya samun lalacewar wasu vital organ, wanda shine dalilin da ya sa ya ke da mahimmanci ga mata su dinga faɗawa masu kula da su idan sun ji ko ga wata alama.

  Idan wata ta ji irin alamomin da aka lissafa a sama, yana da muhimmanci a yi saurin sanar da likita don ɗaukar matakan gaggawa.  Ya kamata mata su san abubuwan da ke tattare da haɗarin da ke tattare da eclampsia kuma su tabbata cewa sun faɗa ma likita su.

  Babban burin shine a sami ciki mai lafiya kuma a haifi ɗa lafiyayye.  Amma ba za a samu haka ba sai an ɗauki matakai na kariya daga kamuwa da cutuka. Allah Y aba mu lafiya da zama lafiya.

  Mai karatu na iya duba: Abubuwan da ya kamata ku sani game da cutar mantuwa na amnesia

  Rubutawa: Maryam Haruna, a registered midwife, daga Zamfara, Nigeria

Comments

0 comments