Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Rayuwa da Zamantakewa » Matakan da masoya kan fuskanta kafin aure

Matakan da masoya kan fuskanta kafin aure

 • Yawancin alaƙar soyayya tana farawa, sannan ta haɓɓaka, har ta yi yadon da ba a san dalili ba. 

  Fadawa cikin soyayya abu ne mai sauki, amma alaƙar na iya zama abu mai matukar wahala duk da irin ababen da mu ke kallo a su Bollywood da Hollywood sai wasu ke ganin kamar babu wani kalubale a tattare da soyayyar. Sai ka shiga cikinta ka ga ashe duk ba haka abun yake ba. Wasu masoyan su kan yi nasarar shawo kan guguwar da babu makawa ta taso a zamantakewar su yayin da wasu kuwa ba su da yanda za su yi face su bar wannan soyayyar ta taɓarɓare. 

  Ko wace soyayya tana wucewa ta hanyar wasu matakai wadanda ba mu cika damuwa da su ba, mu kan yi kacibus da su sai dai ba kasafai muke yawan gane su ko bambance su ba.  Akwai matakai da su ka zama  wajibi a kowace soyayya a fuskance su, sai dai kowa da irin yanda ya ke riskarsu duba da cewa mu mutane muna da bambancin halayya.  Wasu matakai suna ɗaukar lokaci fiye da wasu kamar yadda na fada a farko ya danganta da waye ka ke tare da shi, za ku ga wasu mutane suna ɗaukar lokaci mai tsawo a kowane mataki.  

  A cikin wadannan matakai na soyayya, zaku kasance cikin zumudin juna da shakuwa mai karfi da za ta shiga tsakanin ku,wato a lokacin da soyayyar take sabuwa kenan.

  Fahimtar matakan soyayyarku ku da abokin tarayyarku na iya taimaka muku wajen kewaye waɗannan matakai daban-daban ba tare da kun samu matsala ba.  

  Na samu zantawa da wasu daga cikin matasa inda suka bayyana mun irin kalubalen da suka fuskanta a irin wannan matakai.

  Malam Shafi'u ya ce "gaskiya farkon fara soyayya da wacce zan aura abin gwanin ban sha'awa. Mu ka shafe awanni muna fira da juna. Kulawa sosai mu ke ba junanmu. Yanzu kuwa ta kai bai fi mu yi waya sau biyu a rana ba, abu kadan sai ya hada mu fada, sai mu yi kwanaki ba mu yi ma juna magana ba kuma unguwar mu daya. Idan na dawo aiki ko zan fita sai na wuce ta gaban gidansu. Farkon soyayyar mu kullum sai na tsaya mun gaisa in dai tana nan haka idan na dawo. Kulawar da take ba ni ya ragu sosai. Kuma muna son junanmu. Amma yanzu babu wannan dokin kamar farkon fara soyayyar mu. Sai mu yi kwanaki ba mu ga juna ba, kuma biki sai kara matsowa yake. Wani sa'in har ina tunanin ko ta daina so na ne, ta kuma tabbatar mun cewa tana so na".

  Na ji ta bakin wata baiwar Allah da ta bayyana mun irin salon na ta matakan kafin su yi aure da mijinta.

  Amirah ta ce "Shekarar mu hudu muna tare kafin mu yi aure, mun yi soyayya sosai ba wanda bai san shi ba matukar kana tare da ni. Kin san farko ana marmarin juna za a yi ta waya da tura sakonni kala-kala. To da zama ya yi zama sai halin kowa ya fito fili. Farko ban san cewa yana da saurin fushi ba. Ga shi an sa mana rana abun duniya ya dame ni, mun yi wani fada da har sai da muka shafe wata biyu ba mu magana da juna har mahaifiya ta na sa mu akan cewa ni na fasa auren ma. Don basu san mi ke faruwa ba ina makaranta. Mu ka dawo aka shirya. Dole na sama raina cewar matukar ina son shi dole inyi hakuri da wasu halayen kuma shi ma akwai halaye na da baya so. Gashi yanzu muna zaune lafiya sai abinda ba a rasa ba. A lokacin baya da na biye ma zuciya da an fasa auren".

  Kuna iya duba wannan makala da ta yi sharhi akan yadda ma’aurata za su bullowa rashin jituwa a Tsakani.

  Kadan kenan daga cikin ra'ayoyin mutane game da wadannan matakai da soyayya kan shiga kafin a yi aure, wanda da mafi yawan mutane ba su ganewa har ta kai ga ana iya rabuwa da juna a kan wannan gabar.

  Ga bayanin matakan nan daya bayan daya.

  - Matakin shauki: Matakan sabuwar soyayya suna farawa ne lokacin da kuka fara haɗuwa da wani. Mafi yawan mutane sun fi la'akari da suffa da kuma yanayin da suke ji game da mutum, sauran abubuwa kan biyo bayan a mataki na gaba.

  A irin wannan matakin kuna ganin cewa mai ƙaunarku ba shi da wani aibu a tattare da shi, a lokacin kuna jin cewa ai duk wani abu da ku ke bukata a abokin zama sun cika shi.  Sai ku ji ai rayuwar ma kamar ba zata yiwu ba tare da wannan abokin rayuwar ba. Sannan ba ku gane halin mutum na banza a lokacin ko ka gane ma shaukin soyayya ba zai bari ya yi tasiri ba. 

  A wannan lokacin za ka iya fada da kowa a kan masoyinka matukar su ka nuna adawar su a kan masoyinka.

  A matakan soyayya wannan matakin shine mafi soyuwa a zukatan masoya.

  Shawarar a nan masoya su yi amfani da wannan mataki ta hanyar da ta dace, da ga zarar an fita wannan matakin ba fa zai dawo ba. A wannan matakin ne ya kamata masoya su fahimci junan su sosai, su san da wa suke tare da gujewa kalubalen da za a fuskanta a gaba.

  A yi binciken da ya kamata game da wanda ka ke tare da shi. Sannan kar a yi saurin yanke hukunci a irin wannan gabar da ake cikin matsananciyar soyayya da ba kasafai ake ganin laifin juna ba. A tuna da cewa wannan jin dadin na lokaci ne kankani, masana ba bada shawarar a yi bincike a kuma fahimci juna sosai a kan wannan gabar.

  - Matakin Shakka da Musu: Mataki na biyu na dangantaka shi ne da Shakka da Musu, wanda a lokacin  ne aka fara lura da bambance-bambancen da ke tsakaninmu da abokanmu. 

  Mun farka daga mafarkin so da kauna. A wannan lokacin ne halayen mu ke bayyana. Sai ya zamo kana tunanin wanda kake ganin za ku gina rayuwar ku a tare ta fito da wani sabon hali da ka kasa gane kansa. Wannan saurayin na ki mai fara'a mai nuna tsantsar kulawar shi a kanki yanzu ya canza, sai ki ga kamar ba shi ba.

  Yawan kiran da yake ma ki a waya ya ragu da kaso hamsin, daga nan sai ki fara tunanin ko dai ya daina sonki ne ko wata ce ta dauke ma shi hankali. Daga nan sai shakku ya shigo ciki a fara zargin juna wasu hakan kan kai su ga rabuwa da juna.

  Ya kamata masoya su fahimci wannan matakin ta hanyar yi ma junan su uzuri don samun kwanciyar hankali kowane bangare.

  Karanta alamomi 8 da za ki gane namiji da gaske ya ke.

  - Matakin rushewa: Mataki na uku na soyayya a tsakanin saurayi da budurwa shi ne matakin Rushewa. Wannan shi ne lokacin tsanani a soyayya, wanda zai iya zama kamar ƙarshen hanya ne ga wasu masoyan. A wannan lokacin, gwagwarmayar ce tsagwaronta, a yi fada da juna a shirya wani fadan ya dau lokacin kafin a shirya har ya zamo kamar ba za a kara kasancewa da juna ba. A wannan lokacin ya kamata a yi amfani da ƙaunar da ake ma juna don a samu sassauci na kalubalen da a ke fuskanta. Sai an jajirce sannan kuma an nuna sadaukantaka, dole daya ya sakko a yayin da ake cikin wannan mataki musamman idan aka zo gargarar aure.

  Mata da dama kan fuskanci wannan kalubalen. A tattaunawar da na yi da wata, ta bayyana mun cewa; "Tun da biki na ya gabato mu ka fara samun matsala da wanda zan aura. Ko wayar shi na daina dagawa sai dai su yi magana da kanwata ko mahaifiyata a kan batutuwan da suka shafi aurenmu, kuma ba wai don bana son shi ba. Gabaɗaya ya zamo haushi yake ba ni. Da yake mutum ne mai fahimta idan na hau sama shi sai ya sakko har aka yi biki. Yanzu haka diyar mu daya".

  A gefe daya na ci karo da wani sako a shafin Instagram inda wani ke korafin yanda wadda zai aure ta daina ba shi kulawar da ta dace, abu kadan sai ta fara daga murya duk tabi ta daga hankalinta wanda shi abun na damun shi. Har yake tambayar shin haka mata suke yi idan an kusa auren su?

  Alal hakika a irin wannan mataki ya zama wajibi su ba juna iska, sannan kar su jingine duk wata matsala ba tare da sun tattauna ta ba. Domin a wannan lokacin akan samu matsaloli daban-daban da ke bukatar ku warware su iku-iku domin a samu bakin zaren matsalar.

  Mu sani cewa kowace dangantaka ana gwada ta ne ta hanyar jerin rikice-rikice da hadarin da ta kan shiga  a lokuta daban-daban a rayuwa. 

  Sanin matakan nan na soyayya na matukar taimaka ma masoya wajen  fahimtar abubuwan da su ke ji game da junansu da kuma alakar da ke tsakanin su. Hakan zai rage yawan matsalolin da ake samu kafin a yi aure, za a fahimci juna a kuma ba juna uzuri a irin wannan mataki.

  Rubutawa: Ayeesh Chuchu, daga Katsina, Nigeria

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • SHAFI NA DAYA Direban motar ya fito da sauri ya bude bayan motar ya na dan dukawa alamun girmamawa, tare da fadin “Hajiya a fito a sannu.” Hajiyar ta fito ciki leshi na alfarma gami da mayafin da ya da ce da shi, ta gyara tsaiwar ta sannan ta kalli sauran masu fitowa daga cikin motor. ...
 • Mene ne zazzabin cizon sauro? Zazzabin cizon sauro wato malaria cuta ce da ta ke damun mutanen duniya, musamman mutanen Afrika, kuma wannan cuta tana daya daga cikin cututtukan da suke damun mutanen Nigeria. Tana iya shafar yara, manya, tsofaffi, maza da kuma mata. Ma'anar maleriya Maleriya cuta ...
 • Maza da mata jinsi ne guda biyu mabanbanta da ke da bambancin halaye. Maza da mata suna da yanayi daban-daban, amma da fatan wannan makalar za ta taimaka wajen fayyace abubuwa da samar da kyakkyawar fahimta game da irin wadannan bambance-bambancen.  Ya kamata maza da mata su yaba wa wadannan ba...
 • Ciwon sanyin mata wata babbar matsala ce da ke addabar mata. Akasarin mata na fama da wannan cutar, daga kauye zuwa birni, matan aure da yan mata. Kafin nayi wannan rubutun sai dana tattauna da mata da yawa akan wace cuta ce tafi damun mata a yanzu? Amsar dana samu kuma ita ce 'ciwon sanyi'. Mene n...
 • Mece ce cutar sikila (sickle cell disease)? Jini wanda ake gani a zahiri idan mutum ya ji ciwo ko kuma ya yanke jikinsa yana dauke da abubuwa iri daban – daban, kamar su plasma, Red Blood Cells (RBC), White Blood Cells (WBCs), Platelets da sauransu. Cutar sickler ko amosanin jini tana faruwa ...
 • Brain tumor wani tudun tsiro ne na abnormal cells (wato wasu kwayin halitta) da ke samuwa a kwakwalwan dan adam.  Akwai kala daba-daban na wannan brain tumor din. Wasunsu basa kaiwa ga kansa (benign) sanna wasunsu kuma sukan kai ga zama kansa (malignant). Brain tumor kan fara ne daga kwakwalwa ...
View All