Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Cutar Typhoid: Alamunta, hanyoyin kamuwa da kariya daga gare ta

Cutar Typhoid: Alamunta, hanyoyin kamuwa da kariya daga gare ta

 • Matashiya

  Zazzaɓin Typhoid (taifod) cuta ce mai saurin yaɗuwa a jiki wacce wata bacteria ce mai suna Salmonella enterica serotype typhi ke haifarwa.

  Zazzaɓin taifod yana da alamomi wadanda suka shafi cutar kuma suke nunawa. Manya-manyan alamominta sun haɗa da zazzaɓi, da ciwon gaɓoɓin jiki, da yawan ciwon ciki. Zazzaɓin taifod na ƙaruwar ne idan har ba a kula da shi ba. Idan ya yi yawa ya kan jawo zubar jini na hanji, da katsewar  hanji, da lalacewar ciki wanda waɗan nan na iya faruwa cikin wata guda.

  Mene ne zazzaɓin taifod?

  Zazzaɓin taifod wata ƙwayar cuta ce da ke iya yaɗuwa cikin jiki, wacce ke haifar da ciwon gaɓoɓin jiki, matsanancin ciwon kai da kuma yawan gudawa.

  Wata kwayar cuta ce da ake kira Salmonella enterica serotype typhi, ita ce ke haifar da taifod wacce ke da alaƙa da ƙwayoyin cuta waɗanda ke haifar da guban abinci na salmonella da kuma rashin lafiya mai tsanani, kwayar cutar tana yaɗuwa a cikin ruwa ko abinci. Zazzaɓin taifod yana yaduwa sosai.  Mutumin da ya kamu da cutar na iya fitar da kwayoyin cikin fitsari.

  Idan mutum ya ci abinci ko ya sha ruwan da ya gurɓata da ƙananan ƙwayoyin cuta, zai iya kamuwa da ƙwayoyin cuta kuma ya kamu da zazzaɓin taifod.

  Lamarin na zazzaɓin cutar taifod a Amurka ya ragu sosai tun daga farkon 1900s, lokacin da aka ba da rahoto a ƙasar, ƙasa da da mutane 400 ke kamuwa da cutar duk shekara, inda ƙasashe kamar su  Mexico da Kudancin Amurka su ma an samu ci gaba sosai na rage yawaitar masu kamuwa da cutar. Wannan ci gaban ya samo asali ne sakamakon kyakkyawan tsabtace muhalli da suke yi.  A duk duniya, zazzabin taifod yana shafar sama da mutane miliyan 21 a kowace shekara, inda kimanin mutane 200,000 ke mutuwa daga cutar.

  Ta yaya mutane ke kamuwa da zazzaɓin taifod?

  Ana daukan zazzabin taifod ne ta hanyar shan ko cin kwayoyin cuta a cikin gurɓataccen abinci ko ruwa.  Mutanen da ke fama da rashin lafiya da cutar taifod na iya gurɓata ruwan da ke kewaye da su ta hanyar bayan gari wanda ke ɗauke da ƙwayoyin cuta.  Gurɓatar ruwan sha na iya lalata abinci. Kwayoyin na iya rayuwa na tsawon makonni a cikin ruwa ko busasshen najasa.

  Kusan 3% zuwz 5% na mutane sun zama masu ɗaukar ƙwayoyin cutar bayan rashin lafiya mai tsanani. Wasu kuma suna fama da rashin lafiyar ne wanda ba a saurin ganewa. Waɗannan mutane na iya zama masu dauke da ƙwayoyin na tsawon lokaci - duk da cewa ba su da wata alama.

  Mai karatu na iya dubaKansar mafitsara: Ire-ire da hanyoyin kariya da kamuwa da ita

  Ta yaya ake gane zazzaɓin taifod?

  Cutar tana bayyana ne a jikin mutane ta hanyar zazzaɓi a wani lokacin.  Kwayar cutar ta kan mamaye mafitsara, tsarin biliary, da kuma kayan ciki na hanji.  Kwayoyin suna shiga cikin hanjin ciki kuma ana iya gano su ta hanyar gwajin samfuran da za a ɗauka. Idan sakamakon gwajin bai bayyana ba, za'a dauki jini ko samfurin fitsari don yin wani gwajin.

  Mene ne alamomin zazzabin typhoid?

  Lokacin shiryawa yawanci makonni 1-2 ne, kuma tsawon lokacin rashin lafiyar yana kusan makonni 3-4. Kwayar cutar sun hada da:

  1. Rashin cin abinci
  2. Ciwon kai
  3. Zazzaɓi ya kai digiri 104 na Fahrenheit
  4. Rashin nutsuwa
  5. Gudawa

  Yadda cutar ke yaduwa

  1. Kwayar cutar Salmonella ta typhi za ta kasance a makewayin gidan mai cutar. Idan ba sa wanke hannayensu da kyau daga baya, za su iya gurɓata duk abincin da suka taɓa. Duk wanda ya ci wannan abincin shima yana iya kamuwa da cutar.
  2. Haka kuma, idan mai dauke da cutar ya riƙe abinci ba tare da ya wanke hannayensa yadda ya kamata ba bayan ya gama fitsarin, zai iya yada cutar ga wani wanda ya ci gurbataccen abincin.
  3. Mutanen da ke shan gurɓataccen ruwa ko cin abincin da aka wanke a cikin gurɓataccen ruwa na iya kamuwa da zazzaɓin taifod.

  Sauran hanyoyin da za a iya kamuwa da zazzaɓin taifot sun haɗa da: Amfani da banɗaki wanda ya gurɓata da ƙwayoyin cuta da taɓa bakinka kafin ka wanke hannunka, cin abincin teku daga tushen ruwa wanda gurɓataccen kwaya ko baƙo ya kamu da shi, cin danyen kayan lambu, gurbatacciyar madara wacce ba a dafa ba, yin jima'i ta baka ko ta dubura tare da mutumin da ke ɗauke da ƙwayar Salmonella typhi da sauransu.

  Wadanda suka fi hatsarin kasancewar suna dauke da cutar

  Kusan 1 cikin mutane 20 da suka tsira daga zazzaɓin taifot ba tare da an yi musu magani ba za su zama masu ɗauke da cutar. Wannan yana nufin kwayoyin cutar ta Salmonella typhi suna ci gaba da rayuwa a cikin jikin mai dauke da ita kuma ana iya yaɗata  kamar yadda aka saba a cikin fitsari, amma mai ɗauke da cutar ba shi da wasu alamun yanayin.

  Yadda kwayoyin ke shafar jiki

  Bayan cin abinci ko shan ruwan da ya gurbata wadda ke dauke da Salmonella typhi, ƙwayoyin suna sauka kasa cikin tsarin narkewar abinci, inda za su yi saurin ninkawa. Wannan yana haifar da zazzaɓin mai zafi, ciwon ciki da maƙarƙashiya ko gudawa.

  Idan ba a kula da shi ba, ƙwayoyin za su iya shiga cikin jini su yaɗu zuwa wasu sassan jiki. Wannan na iya haifar da alamun cututtukan zazzaɓin taifod don ƙara muni cikin makonni bayan kamuwa da cutar.

  Idan gabobi suka lalace sakamakon kamuwa da cutar, zai iya haifar da matsaloli masu tsanani, kamar zub da jini ta ciki ko wani ɓangare na hanji ya tsage.

  DubiBayanai game da lalurar autism spectrum disorder (galhanga)

  Gwajin cutar taifod

  Ana iya tabbatar da cutar zazzaɓin taifod yawanci ta hanyar bincika samfuran jini, ko bayan gari (stools) ko fitsari. Wadannan samfura za'a bincikasu ne a ƙarƙashin tabarau don ganowa ko mutum kwayoyin Salmonella typhi waɗanda ke haifar da yanayin.

  Ba koyaushe ake gano kwayoyin ba a karon farko, saboda haka ana iya buƙatar yin jerin gwaje-gwaje. Gwajin samfurin bayan gari (stool) shine mafi ingantacciyar hanyar gano cewa mutum na ɗauke da wannan cuta ta zazzaɓin taifod.

  Amma samun samfurin abu ne mai cin lokaci kuma mai raɗaɗi, saboda haka yawanci ana amfani dashi ne kawai idan wasu gwaje-gwaje basu cika ba.

  Idan an tabbatar da zazzaɓin taifod, wasu daga cikin dangin na mutum ma na buƙatar a gwadasu idan har su ma suna ɗauke da ita.

  Yaya ake magance zazzaɓin taifod?

  Yawanci zazzaɓin Typoid ana iya magance shi cikin nasara tare da shan maganin rigakafi. Yawancin lokuta ana iya magance ta a gida, amma kuma an fi so mutum ya je asibiti idan yanayin ya kasance mai tsanani.

  Jinya a gida

  Idan aka gano cutar zazzabin taifod a farkon shigansa, za a iya tsara hanyar alluran rigakafi. Yawancin mutane suna buƙatar ɗaukar waɗannan kwanaki 7 zuwa 14.

  Wasu nau'ikan kwayoyin cutar Salmonella ta typhi wadanda ke haifar da zazzaɓin taifod sun samar da juriya ga nau'i daya ko fiye na maganin rigakafi. Wannan yana ƙara zama matsala tare da cututtukan taifod da suka samo asali daga kudu maso gabashin Asiya.

  Duk wani samfurin jini, ko na bayan gari (stool) ko fitsari (urine) da aka ɗauka yayin binciken galibi ana gwada su a cikin dakin gwaje-gwaje don sanin wane nau'in cutar da ke tattare da mutum, don haka za a iya yin magani tare da maganin rigakafi wanda ya fi dacewa.

  Tabbatar ana samun hutun da yawan  shan ruwa mai tsabta kuma a ci abinci akai-akai. Ana iya samun sauƙi wajen cin abinci mai sauƙi sosai da yawa, maimakon cin mai nauyi sau 3 a rana.

  Hakanan yakamata a kiyaye tsabtar muhalli da ta jiki kamar wanke hannuwa ko yaushe da sabulu da ruwan dumi, don rage haɗarin kamuwa da cutar ga wasu. Tuntuɓar likitan da wuri-wuri idan alamun na daɗa ƙaruwa.

  Alamun cutar ko kamuwa da cuta na iya sake dawowa ga kashi kalilan daga wadda suka taba kamuwa da cutar.

  Mafi yawan mutanen da ake yiwa maganin zazzaɓin taifod na iya komawa bakin aiki ko makaranta da zarar sun fara samun sauki. Sai dai waɗanda ke aiki wajen sarrafa abinci, da aikin kula da mutane marasa ƙarfi, kamar yara 'yan ƙasa da shekaru 5, tsofaffi da waɗanda ba su da lafiya.

  Maganin asibiti

  Yawanci ana ba da shawarar ajiye mutun ne a asibiti idan kana da alamomin zazzaɓin taifod, kamar su amai, zawo mai tsanani ko kumburin ciki.

  Sannan a matsayin riga-kafi, yara kanana da suka kamu da zazzaɓin taifod ana kama su (admitting) a asibiti.

  A asibiti, za a iya bada allurar rigakafi kuma za a iya bada ruwa da abinci mai gina jiki kai tsaye a cikin jijiya ta hanyar karin ruwa wato drip.

  Idan har ta yi tsanani har tiyata za a iya yi, kamar zub da jini na ciki ko ɓangaren tsarin narkewar abinci da ya rabu. Amma wannan ba safai ake samun mutanen da ake yiwa maganin riga kafin ba.

  Ci gaban da aka samu game da cutar taifod

  Kafin amfani da maganin rigakafi na cutar taifod, yawan mutuwa saboda wannan cuta ya kasance kashi ashirin ne cikin darin. Mutuwa tana faruwa ne daga lokacin da cutar ta tsananta a jikin mutum. Alamun tsananin cutar kamar ciwon huhu, zubar jini na hanji. Amma saboda tashi tsaye da aka yi wajen bada gudunmawa da aka bada maganin rigakafi da kulawa na tallafi, an rage mace-mace zuwa 1% -2%.

  Allah Ya bamu lafiya da zaman lafiya, amin.

  Rubutawa: Maryam Haruna, a registered midwife, daga Zamfara, Nigeria

Comments

0 comments