Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Abubuwan da ya kamata mu sani game da cutar brain tumor

Abubuwan da ya kamata mu sani game da cutar brain tumor

 • Brain tumor wani tudun tsiro ne na abnormal cells (wato wasu kwayin halitta) da ke samuwa a kwakwalwan dan adam.  Akwai kala daba-daban na wannan brain tumor din. Wasunsu basa kaiwa ga kansa (benign) sanna wasunsu kuma sukan kai ga zama kansa (malignant). Brain tumor kan fara ne daga kwakwalwa ko kuma cutar kansa kan fara daga wani sassan jiki can na daban sai ya yadu zuwa kwakwalwar.

  Yadda brain tuma kan yadu da sauri ko rashin sauri ya danganta ne kwarai. Yadda saurin yaduwansa zai kasance da kuma bangaren jiki da wannan tumor din ya ke su za su iya nuni ga yadda zai shafi aikin nervous system na mutum.

  Jinyar brain tumor duk sun alaka ne da irin kalar tumor din da mutum ke fama da shi, da kuma girman shi tumor din ko inda ya ke zaune a cikin jiki.

  Ire-iren brain tumor

  Muna da ire-iren brain tumor da dama. Ga su kamar haka:

  1. Acoustic neuroma
  2. Astrocytoma
  3. Brain metastases
  4. Choroid plexus carcinoma
  5. Craniopharyngioma
  6. Embryonal tumors
  7. Ependymoma
  8. Glioblastoma
  9. Glioma
  10. Medulloblastoma
  11. Meningioma
  12. Oligodendroglioma
  13. Pediatric brain tumors
  14. Pineoblastoma
  15. Pituitary tumors

  Mai karatu na iya duba: Cutar typhoid: Alamunta, hanyoyin kamuwa da kariya daga gare ta

  Alamomin brain tumor

  Alamu na wannan cuta na brain tumor sun banbanta. Banbancin su na samuwa ne idan aka samu banbanci girman tumor, ko kuma wajen da shi tumor ya ke a jiki ko kuma yanayin saurin/rashin saurin girmanshi.

  Ga dai wasu daga cikin ire-iren alamun da kan iya samuwa a ko wani irin brain tumor:

  1. Sabon yanayi na ciwon kai. Wato ciwon kai da zai kasance daban da wadda mutum ya saba fama da shi.
  2. Ciwon kai da a hankali a hankali ya ke zama mai tsanani da kuma kuntatawa
  3. Tashin zuciya ko amai da mutum bai san mene ne ya ke haddasa shi ba
  4. Matsala ta gani, kamar ganin dishi-dishi ko kuma mutum ya rika gani double-double haka nan
  5. Rasa jin motsi ko wani sensation a hannu ko kafa
  6. Matsalar daidaituwa (difficulty with balance)
  7. Matsalar magana (speech difficulties)
  8. Fiskantar rikicewa a al’amuran yau da kullum (confusion in everyday matters)
  9. Canji na personality ko halayyan mutum
  10. Samun seizures (wato irin fisga mai kama da jan wutan lantarkinnan) musamman ga mutumin da bai da tarihin irin wannan matsalar
  11. Samun matsala ta ji

  A yaushe ne mutum ya kamata ya ga likita?

  Mutum ya yi kokarin ganin likita da gaggawa idan ire-iren alamun cutar suna faruwa da shi akai-akai.

  Dalilan da ke kawo brain tumor

  Brain tumor da ke farawa a kwakwalwa

  Asalin brain tumor (wato primary brain tumor) yana farawa ne a kwakwalwar ko kuma a tissue da ke kusa da kwakwalwar, kamar a membrane da ke rufe da kwakwalwa, ko kuma a cranial nerves, ko pituitary gland ko pineal gland.

  Irin wannan brain tumor din na faruwa a yayin da kwayin hallita wato cells suka samu matsala da ake kira da mutation a DNA na su. Wannan mutation din yana saka cells su girma sannan su rarrabu suna karuwa, sannan su ci gaba da rayuwa a yayin da cells masu kyau ke mutuwa. Sakamakon hakan shi ne taruwan wadannan cells marasa kyau din wanda shi zai haifar da tumor.

  Brain tumor da ke farawa daga kwakwalwa bai da yawa sosai a wajen manya, ba kamar yadda secondary brain tumor (wadda ke farawa daga wasu sassan jiki na daban) ya ke da yawa a wurinsu ba.

  Ku karanta: Kansar mafitsara: Ire-ire da hanyoyin kariya da kamuwa da ita

  Akwai ire-iren brain tumor da ke farawa a kwakwalwa da yawa. Kowannen su ya samo sunan shi ne daga irin cells din da ke haifar da shi. Ga wasu daga cikin misalansu:

  1. Gliomas. Wannan irin tumor din na farawa ne daga kwakwalwa ko a spinal cord
  2. Meningiomas. Wannan kuma tumor ne da ya samo asalinsa daga membrane da ke kewaye da kwakwalwa da kuma spinal cord. Yawancin irin wannan tumor suna zama kansa.
  3. Acoustic neuromas. Wannan wani tumor ne da bai da karfi wadda ke samuwa daga nerves da ke controlling daidaituwa da kuma ji (hearing) wadda ke farawa daga cikin kunne zuwa kwakwalwa.
  4. Pituitary adenomas. Wannan ma tumor ne da bai da karfi wadda ke samuwa a pituitary gland da ke mafarin kwakwalwa.
  5. Medulloblastomas. Wannan tumor ne dake haifar da kansa sosai kuma ya fi yawa a wajen yara kanana. Yana farawa ne a kasan bayan gefen kwakwalwa sanan ya kan yadu zuwa spinal cord. Wannan irin tumor ba a cika samun shi ga manya ba.
  6. Germ cell tumors. Wannan irin tumor kan fara ne tun yaranta yadda ya ke haifar da testicles ko ovaries. Amma wasu lokutan wannan irin tumor din kan shafa wasu sassan jiki na daban, misali kwakwalwa.
  7. Craniopharyngiomas. Wannan irin tumor wadda baya haifar da kansa ya kan fara ne kusa da pituitary gland na kwalkwalwa wadda ke kasan wasu hormone da ya ke controlling aikin sassa daba-daban na jiki.

  Cutar kansa da kan fara daga wasu sassan jiki ya bazu har izuwa kwakwalwa

  Abin da ake cewa secondary brain tumor shi ne brain tumor da ba na asali ba, ma’ana wadda ya faro daga wani sashin jiki na daban sai daga baya ya bazu zuwa kwakwalwa.

  Secondary brain tumors sunfi samuwa ga mutanen da ke da tarihin cutar kansa. Amma a wasu lokuta, da bai cika faruwa ba, wasu sukan kamu da irin wannan cutar cansar ko in ce irin wannan tumor.

  Wannan irin brain tumor yafi faruwa da manya nesa ba kusa ba, fiye da yadda suke kamuwa da primary brain tumor (brain tumor na asali).

  Ko wani irin kansa na iya bazuwa har izuwa kwakwalwa. Amma wadanda suka fi yawan faruwa sun hada da:

  1. Kansar mama (breast cancer)
  2. Kansar hanji (colon cancer)
  3. Kansar koda (kidney cancer)
  4. Kansar huhu (lung cancer)
  5. Melanoma

  Dalilan da suke karawa mutum shiga hatsarin kamuwa da brain tumor

  1. Exposure to radiation. Wato mutanen da su ka shiga ko kasancewa kusa da irin iskan nan na radiation kamar ionizing radiation suna iya shiga hatsarin kamuwa da brain tumor. Misalan irin wannan ironizing radiation sun hada da jinyan nan da ake cewa radiation therapy domin maganin cutar kansa ko kuma radiation na atomic bonbs.
  2. Tarihin cutar brain tumor a zuri’an mutum. Kadan daga cikin masu kamuwa da brain tumor sun na da tarihin cutar a zuri’ansu ko kuma suna da genetic syndromes (cututtukan kwayoyin halittan) wadda ke kara musu hatsarin brain tumor din.

  Wannan shi ne abin da ya sauwaka wadda za mu kawo muku game da cutar brain tumor. Kar ku manta, kamar kullum, muna kawo muku makalun akan kiwon lafiya ne domin karuwan ilimi da wayar da kawunanmu. Idan mutum na da matsala ya yi gaggawan zuwa gurin likita domin neman magani, domin likita shi ne kadai ke da kwarewar ba da magani. Allah Ya bamu lafiya da zaman lafiya, amin.

  Domin karanta wannan makala cikin harshen Turanci, latsa wannan daga Mayo Clinic

  Hakkin mallakan hoto: Live Science

Comments

0 comments