Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Abubuwan da ya kamata ku sani game da zazzabin cizon sauro

Abubuwan da ya kamata ku sani game da zazzabin cizon sauro

 • Mene ne zazzabin cizon sauro?

  Zazzabin cizon sauro wato malaria cuta ce da ta ke damun mutanen duniya, musamman mutanen Afrika, kuma wannan cuta tana daya daga cikin cututtukan da suke damun mutanen Nigeria. Tana iya shafar yara, manya, tsofaffi, maza da kuma mata.

  Ma'anar maleriya

  Maleriya cuta ce wadda take saka zazzabi da ciwon jiki, wadanda za muyi bayaninsu a nan gaba kadan.

  Yadda ake kamuwa da maleriya

  Asalin abinda ya ke janyo cutar shi ne shigar wata kwayar halitta da ake kira “plasmodium” cikin jinin mutum. Ita wannan plasmodium ba ta shiga jinin mutum kai tsaye sai ta hanyar sauro. Ma’ana dai, sauro shi ne wanda ya ke yada wannan kwayar halittar (plasmodium).

  Shi sauro yana yada wannan cutar ne a tsakanin mutane (daga mutum zuwa wani mutum daban) a yayin da ya ke neman abinci, wato jini. Ma’ana dai, abincin sauro shi ne jini.

  Alamomin cutar maleriya

  Idan sauro ya ciji mutum, kuma ya saka masa wannan plasmodium din a cikin jininsa, to ba a lokacin zai fara jin alamun ciwon ba, har sai bayan wasu kwanaki.

  Alamomin ciwon sun hada da:

  • Zazzabi
  • Ciwon kai
  • Jiki yana ciwo
  • Gabobi suna ciwo
  • Kasala
  • Amai

  Idan tayi tsanani, zata iya haddasa:

  • Fita daga hayyaci
  • Jijjiga
  • Karancin jini
  • Rasa rai….Da sauransu.

  Hanyoyin kariya daga cutar malaria

  Kamar yadda aka yi bayani a baya, ita wannan cuta dai sauro ne ya ke yada ta. Don haka duk wata hanya da mutum zai bi don yakar sauro, to wannan hanyar zata iya kare shi daga samun wannan cutar.

  Waɗannan hanyoyi sun haɗa da:

  1. Hana sauro haihuwa
  2. Ka hana sauro ya cije ka (ya sha jininka)
  3. Kashe sauron.

   Hanyoyin hana sauro haihuwa:

  1. Gyara kwatoci: A daina barin ruwa yana zama a cikin kwatoci ba tare da ya na gudana ba. Sannan kuma a rufe kwatocin.
  2. A daina barin ruwa ya dade a bude a cikin muzubi

  Yadda za ka hana sauro ya cije ka

  Amfani da gidan sauro (wato Insecticide net), ma’ana kwana a cikin gidan sauro.

  Yadda za’a kashe sauro

  Amfani da maganin sauro na fesawa ko kuma na hayaƙi.

  Abinda ya kamata mutum ya yi idan ya ji alamun cutar

  1. Idan akwai zazzabi, musamman a yara kanana, to sai a samu tsumman zani ko tawul a tsoma shi a ruwa (ba ruwan zafi ba, ba kuma ruwan sanyi ba), kamar dai ruwan fanfo. Sannan sai a matse ruwan, sai a cirewa yaron rigar sa, sannan sai a rika dan daddana jikakken tsummman a jikin yaron (ko ina da ina) musamman inda yafi zafi. Za’a yi ta maimaita haka, har sai jikin ya yi sanyi (zazzabin ya sauka).
  2. Ai maza a garzaya asibiti.

  Abubuwa masu mahimmanci

  • Yana da kyau mutane su sani cewa malaria daban typhoid daban. Zanyi bayanin zazzabin typhoid nan gaba. Amma dai ya kamata a sani cewa malaria ba daya take da typhoid ba.
  • Typhoid ta yi karanci a cikin al’ummar mu matuka da gaske musamman idan aka kwatanta ta da malaria.
  • A guji yin allura da zarar ana zazzabi. An fiso a sha kwayar magani idan ana zazzabi saboda yin allura kan iya haifar da wasu matsalolin.
  • A guji yin allurar jijiya idan ana yin zazzabi. Allurar jijiya tana da hadari kwarai da gaske. Tana iya haifar da matsaloli iri daban-daban. Idan aka yi kuskure, mutum zai iya rasa ransa.
  • Sai an samu kwakkwaran dalili, likita ya ke umarni a yi allurar jijiya, kuma idan za ayi, to sai kwararren me yin allurar ne zai yi (nurse ko likita).

  Karin bayani

  Wasu cututtuka da sauro ke jawowa baya ga maleriya. An bayyana sauro na daya daga cikin kwari mafi hatsari a doron kasa. Hakan kuwa ya faru ne saboda ganin cewa shi ne ya ke jawo cututtuka munana irin su zazzabin maleriya da ke kashe miliyoyin mutane a faɗin Afirka da sauran kasashe masu tasowa.

  Kazalika, baya ga maleriya, akwai wasu munanan cututtukan da cizon sauro ke iya jawowa. Ga wasu daga cikinsu:

  Ciwon tundurmi (elephantiasis)

  Bincike ya gano cewa nau'o'in sauro daban-daban ke yada wadannan tsutsotsi ko tanoni. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kusan mutum miliyan 893 ne a kasashea faɗin Afirka wannan cutar ke yi wa barazana. Ciwon tundurmi na sa kafar mutum ta kumbura suntum, sakamakon samun wajen zama da tana ko wasu kanana tsutsotsi ke a kafar mutum.

  Sauro yana iya sanya wa wani cutar ta hanyar baza masa wannan tana da ya dauko daga jikin ami dauke da ita.

  Bincike ya gano cewa nau'o'in sauro daban-daban ke yada wadannan tsutsotsi. Idan wanann tana ta shiga jikin mutum, sai ta samu hanyar shigewa can cikin jikin mutum inda take hayayyafar miliyoyin ƴaƴaye da ake kira 'microfilariae' a hanyar da jini ke bi.

  Wannan yanayi na ci gaba da yaduwa ta yadda zai haifar da tana da yawa a jikin mutum. Daga nan sai tanar ta taru ta je ta toshe babbar jijiyar jini.

  Toshewar ce ke jawo kumburi a sassan jiki da abin ya shafa kamar su ƙafafu da hannaye da sauran su.

  Wani bincike na Jami'ar Stanford University sun gano cewa, “ba a iya warkewa daga cutar tundrmi gaba daya sai dai a yi ta magani don samun sauki.”

  Amma dai ana iya shan magunguna don rage karfin ciwon da rage yawan kwayar cutar a cikin jini. Hakan zai hana kumburin da kuma rage barazanar yada cutar ga wasu.

  Cutar Shawara

  A watan Nuwamban 2020 an samu barkewar cutar shawara da ta yi sanadin mutuwar mutum 15 a wasu yankunan jihohin Delta da Enugu a kudancin Najeriya. Sauro dangin Aedes da Haemogogus ne su ke yada cutar shawara. Irin wannan nau'in sauron sun fi cizon mutum da rana.

  Ƙwararru sun ce mutum zai fara rashin lafiya bayan kwana uku zuwa shida da kamuwa da cutar, kuma idan ba a gano ta da wuri ba, mutum na iya mutuwa bayan kwana bakwai zuwa 10.

  Ana bai wa marar lafiyan kulawa da magani da sa ido a kansa har sai cutar ta tafi.

  Babu wani takamaimen maganin cutar shawara, amma ana yin riga-kafin hana kamuwa da ita, kwana 10 bayan haihuwar mutum.

  A Najeriya ma akwai dokar da aka saka cewa babu wanda zai yi tafiya zuwa wata kasar ba tare da shaidar cewa an yi masa riga-kafinta .

  Cutar zika

  Cutar zika na ta sa a haifi jariri da dan karamin kai. An fara gano kwayar cutar zika ne a jikin birrai a Uganda a shekarar 1947. Daga baya aka gano ta a jikin dan adam a shekarar 1952 a Uganda da Tanzaniya.

  Wani sauro nau'iin Aedes ne ke yada ta, amma kuma ana iya yada ta ma ta hanyar jima'i, sannan uwa na iya yada ta ga jaririnta.

  Cutar zika tana yin lahani ne ga kwakwalwar jariri tun yana ciki, a inda take tsumburar da ita ta kuma sa a haife shi da dan karamin kai.

  A lokacin da aka samu barkewar cutar a Brazil a shekarar 2016, an samu kusan mutum 200,000 da suka kamu da ita, inda aka yi ta haifar jarirai da tawaya.

  Sabbin shawarwari a kan cutar zika

  Kegel: Motsa jikin da masana suka ce yana kara wa mata ni'ima da karfin jima'i ga maza

  Saura cututtukan da sauro ke jawowa sun hada da:

  Zazzabin dengue da zazzabin chikungunya da zazzabin west nile, kuma sun samo asalin sunayensu ne daga yankunan da aka fara gano su. Sannan suna da kamaceceniya ta yin zazzafan zazzabi da kuma zubar jini.

  Masu binciken sun samo halittun a yammacin Kasar Cambodia wadanda suke da bambanci da sauran halittun a kasashen duniya.

  Wadannan halittun sun sami damar jurewa maganin artemisinin daga waraka - maganin da aka fi amfani da shi wajan yakar cutar zazzabin cizon sauro. Rahotannin kin jin magani a yankin ya bayyana ne a shekara ta 2008.Matsalar kuma tuni ta watsu zuwa sauran yankin Kudu maso Gabashin Asia.

  Masanan sun bayyana Yammacin Cambodia a matsayin wurin da aka fi samun kin jin maganin cutar zazzabin cizon sauron.

  Yanzu masana kimiyyar na damuwa saboda kin jin maganin artemisinin din da halittar kwayoyin cutar zazzabin cizon sauron ke yaduwa. Wannan maganin dai ana amfani da shi kusan a fadin duniya kan maganin zazzabin cizon sauro.

  Maganin dai yana warkar da cutar a 'yan kwanaki kadan yayin da aka yi amfani da shi da wasu magungunan. Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce ya zama wajibi a hana yaduwar kin jin maganin da halittar kwayoyin zazzabin cizon sauro ke yi.

  Karanta: Abubuwan da ya kamata mu sani game da cutar brain tumor

  Yadda za ku kare kanku daga cizon sauro

  1. Ku dinga tabbatar da tsaftace muhallinku kuma kar ku dinga barin kwata. Yawanci sauro na hayayyafa ne a cikin kwata ko ruwan da ba ya tafiya.

  2. Ku dinga amfani da mayukan shafawa a jiki da ke kore sauro sanna ku dinga sanya tufafin da za su rufe muku jiki duka

  3. Ku dinga amfani da maganin kashe sauro, amma ku kula kar ku yi amfani da wanda zai cutar da ku.

  4. Ku dinga kwana a cikin gidan sauro kamar yanda na fada da farko cutar zazzabin cizon sauro cuta ce da ta addabi mutanen Africa. A kowane lokaci ko kuma dakika sai an samu wanda ya mutu ta dalilin cutar malaria.

  Don haka mu kare kanmu daga kamuwa da wannan cuta sannan kuma mu guji yin allura (ta jijiya da ta tsoka) da zarar an fara zazzabin

  A nan zamu tsaya. Allah Ya bamu lafiya da zaman lafiya. Sai mun hadu a makala ta gaba. Amma kafi nan ina son inji ra’ayinku game da wannan maudu’i a comment section.

  Rubutawa: Maryam Haruna, a registered midwife, daga Zamfara, Nigeria

Comments

1 comment