Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Illar Furuci 1 Na Halima Abdullahi K/Mashi

Illar Furuci 1 Na Halima Abdullahi K/Mashi

 • SHAFI NA 1

  Direban motar ya fito da sauri ya bude bayan motar ya na dan dukawa alamun girmamawa, tare da fadin “Hajiya a fito a sannu.”

  Hajiyar ta fito ciki leshi na alfarma gami da mayafin da ya da ce da shi, ta gyara tsaiwar ta sannan ta kalli sauran masu fitowa daga cikin motor. Jummai yar aiki ce ɗauke da Afrah a kafaɗa. Hajiyar ta ce “Jummai bani Afra sai ki goyo Afrin tunda ta na bacci."

  “Tanti Dije mu barta a motar mana tun da ta na bacci mun huta da surutun ta.” Baba Bello ya fada lokacin da ya bude gaban motar ya fito.

  Tanti ta dube shi da sauri “Haba Baba Bello da kanka kake faɗin haka? Ko kai ma ka na taya Fatima faɗa da yan biyu na ne?” Ya ce “Kin san ra 'ayinmu ɗaya ko da yaushe, har na ƙara ƙosawa in ga Fatin Mamma na yi kewar Fatima.” Tanti ta ce “Ai yanzun nan za ka gan ta.” Suka jera direban ya na biye da su dauke da ƙatuwar darduma suka nutsa cikin makarantar Hassan gwarzo, wadda ke a garin kano dan ziyarar Fatima. Iyayen yara ko ina tare da 'ya'yansu guraren da aka ware dan ganawa. Fadila ce ta fara hango su, Tanti Dije ta zo da gudu ta na dariya “Oyoyo Momi!” Da hannu ɗaya Tanti ta rungumo Fadila ta na fadin “Fadila oyoyo.” Fatima cikin jin dadi ta nuna musu wani guri “Momi ga wani guri nan zaku sa kafet ne?” Habu direba ya shimfiɗa darduma suka zauna. Fadila ta miƙawa Afrah hannu "Zo mu je mu kira Aunty Fatima ." Afrah ta sa ke lafewa. Tanti ta ce “Dama Afrin ce za ta je wannan sarkin tsoro ce."

  Bello ya ce “Ni bari in zo mu je". Fadila ta ce “Ai baza a barka zuwa gurin mata ba, yanzu zan kirata ku dan yi hakuri.” Cikin sauri ta nufi kiran Fatima.

  Abin da Baba Bello ya yi tsammani shi ne ya ga Fatima da gudu za ta fada jikin Momi, ya san ta na ganinsa za ta fa sa, cikin ɗoki da ihu za ta fado jikinsa ya lumshe ido tare da kallon in da ya ke zaton ta nan za ta ɓullo. Fadila maimakon Fatima sai ya hango wata siririyar yarinya su na tafe tare da Fadila, yarinyar ta na tafiya tamkar mai tausayin kasa, fuskar ta sanye da gilashi wanda bai sani ba na ado ne ko kuwa na ƙarawa ido ƙarfin gani ne?

  Ya mai da kansa ga Tanti. Ya ce “Ba ta ga Fatimar ba ke nan?" Tanti ta kai duban ta ga su Fadila ta ce “Ga su nan tare.” Bello ya sake ware ido ya na kallon su cikin tsananin mamaki.

  “Baa Bellona!”

  Fatima ta fada tare da dafa kirji bayan ta tsaya turus. Ya mike tsaye tare da isa gaban ta ido ya zuba mata, kamar mai son ganin wani abu, cikin sauri ya waiwayo tare da duban Tanti yana faɗin “Hatta muryar ta ta canza me yasa?” Fatima ta yi ɗan murmushi “Ba Bello na sannu da zuwa, wacce tsaraba ka wo min?” Ya ce “Kin san dole in zo da Kwasam.” “Mamma kuma me ta ba da a kawo min?” Tanti ta katse su. “To ku zo nan mana ku yi maganar daga zaune.” Fadila ta ce “Bari in koma na bar su Aunty.” Tanti ta ce “Hajiyarku ta zo ne?” Fadila ta ce “A'a su Yayanmu ne da matarsa." ta ce “To ki gaida su.” Fadila ta ce "Ai za su zo nan ku gaisa kafin su tafi.”

  SHAFI NA 2

  Tanti Ta ce “Ban san za su zo ba ai da mun taho tare.” Fadila ta ce “Ai su a Kaduna su ke.” Tanti ta ce “Allah sarki.” Fatima ta zauna kusa da Tanti ta na faɗin “Ina Daddy haka mu ka yi da shi fisabilillahi?

  Momy harfa alkawari ya yi min ba wani uzri!” Tanti ta kalli Habu direba wanda ke zaune can gefe, ta ce “Dan Allah Malam Habu a fito da kayan motar nan ku je da Baba Bello.” Fatima ta tura baki ta na cewa “haka Daddy ya min ko?” Tanti ta ce" "Ina waya ta in kira shi , ya fada miki da kansa taro ne na gaggawa ya taso ya na Lagos, ina ta kin zancan amma kin nace, Bello zo ka faɗa mata sakon shi.” Fatima ta matse kafaɗa “Ni ba zan ji ba ai mun yi da shi babu uzuri.” Bello ya ce “Shagwabar ce kawai ba ta can za ba.”

   Habu direba ya ce uwar ɗakina ina ta miko gaisuwa tun ɗazun.” Fatima Ta dube shi “Sorry Malam Habu an zo lafiya ban ji ba ne.” “Lafiya lau.” Ya amsa daidai lokacin da su ke tafiya dan kwaso kaya a mota.
  Fatima ta ballawa Afrah harara wadda ke kwance jikin Momi tare da faɗin “Ke ku ma kallon fa?” Momi ta ce “Zaki fara ko Fati! Ina laifin wanda ya zo ya duba ka?” Fatima ta ƙara sakar ma Afrah harara “Allah Momi haushi suke bani...” “Kar in kuma jin haka ko kunyar ido na ba kya ji?” Fatima ta kuma tura baki cikin shagwaba ta na hararar Afrin. Bello ya zauna bayan ya aje kwalin hannun sa, ya ciro kwasam daga wata jaka Fatima ta amsa da sauri ciki kaguwa ta bude ta kalli Bello.

  “Ba Bello na kana son ka birge ni, kuma ka birge ni.” Ta soma ƙwalƙwala kamar ruwa ga ma abocin kishi. Bello wanda zuciyarsa ke cike da tambayoyi ya dubi Tanti “Wai Tanti wannan gilashi na idon Fatin Mamma fa?” Ya yi tambayar tare da cire gilashi. Fatima ta saki robar madarar tare da sa hannu ta rufe fuskar ta, Bello ya mike cikin tsananin Faɗuwar gaba ya na faɗin me zan gani haka? Me ya samu idanun Fatima?”

  Tanti ta yi saurin cewa “Me ka gani! Ya za ka cire mata gilashin ta Bello? Me ye hakan kuma?” Fatima ta soma zubo da hawaye Bello cikin sauri ya ce “Yi hakuri Fatima ban zo dan in ba ta miki farin cikin ki ba.” Tanti wadda ke harararsa ta ce na nawa kuma?” Ta janyo Fatima zuwa jikin ta.

  “Yi hakuri bari in kira maki Daddy amma sai kin yi shiru.” Fatima cikin shashshekar kuka ta ce “Shike nan Momy ni idona ya lalace ke nan?” Tanti hankalin ta ya kuma tashi, ta ce "In jiwa? Shi ma Bellon wasa ya ke miki fa ko Bello?” Bello cikin in ina ya ce “Ni ni babu komai fa ni kawai ban san ki da gilashin nan ba ne, amma ki yi haƙuri ga idonki babu komai.” Sai lokacin Jummai 'yar aiki ta yi magana, "Haba Aunty Fati kin ga su Afrin sai kallon ki su ke yi, gashi kin ta da wannan ma da ga bacci.”

  Fatima ta kalle su cikin harara sun zuba mata ido fuskar su ɗauke da rashin jin dadin ganin ta ta na kuka. Tanti ta ɗauki robar kwasam din tare da “Faɗin sha kayan ki kin ji.” Fatima ta amsa ta riƙe a hannu, Tanti ta buɗe jakar ta ta ciro tissue ta soma share mata guraren da madarar ta ba ta a jikin ta. Bello cikin son ya kawar da damuwar ya ce “Bari in ɗauko miki tsarabar Mamma ta ce kici ki ba wanda ki ke so.” Ya kai ƙarshen maganar ya na kallon fuskarta. Ta ɗauki gilashin ta ta mai da sannan ta ce "Momi kira min Daddy." Tanti ta ɗauko wayarta yayin da shi kuma Bello ya ci gaba da rarrashi ta har ta saki.

  Sun ci sun sha Tanti ta ba wa Fatima abubuwan da suka kawo mata har da ƙawayanta, musamman Fadila wadda kusan komai tare a ka kawo musu. An kira Daddy In da ya yi ta lallashin Fatima ta re da faɗin “Uwata kiyi hakuri lokaci na gaba zan zo ni kaɗai.” Cikin shagwaba Fatima ta ce “Jarabawa fa za mu fara, sai dai in hutu a ka yi mana ka zo ka tafi dani.” Ya ce dole na in zo Uwata, sannan in ki ka yi ƙoƙari zan kai ki duk kasar da kike son ki je hutu.” Fatima ta saki dariya ta ce, “Mu je zuwa.”

  SHAFI NA 3

  “Ummara zan je Daddyna.” Ya ce “An gama Uwata.” Fatima sai murna ta manta da damuwa sai farin ciki.
  Haka nan wan Fadila da matar sa su ka zo su ka gaida Tanti, sannan su ka yi godiya su ka tafi. Fadila da sauran kwayansu su ka yi ta ɗaukar hotuna da kyawawan yan biyu, waɗanda in su ka ga waya za a yi hoto shi kenan babu sauran kiwa. Fatima dai cewa ta yi ba za ta ɗauki hoto da su Afrah ta ce ba za ta yi da su ba, dan ita ba sa'ar su ba ce.

  Sun ɗauka da Ba Bello sosai, ta ce “Jummai ki fita sabgar yaran nan ki zo mu yi hoto.” Jummai Ta ce “Uwar ɗakina ina ni ina fita sabgar iyayan ɗakina? A yi hakuri mu ɗauki hoton nan da su ko sa ƙara mana kwar jini a idon duniya." Cikin zolaya Jummai ta ke maganar. Fatima ta ce “To ba zamu yi da ku ba, Momi ki zo mu dauka.” Momi ta ce nima dai in ba bu yarana zan iya hakura.” Fatima ta tura baki tare da faɗin “To karsu tsaya kusa da ni.” Jummai ta ce “Uwar ɗakina yi murmushi mana fushi ba ya yi miki kyau, sai ki ke kama da mutanan Hindiya, amma in kina murmushi tamkar larabawan Chaina ko na Dubai.”

  Dariya Fatima da su Fadila suka saki. Fatima ta ce “Wai ke Jummai me ya haɗa chaina da larabawa?” Jummai ma cikin dariya ta ce “To koma dai su wane ne tun da dai na saka ki dariya ai shi kenan ,yanzu sai mu sha hoto.” Wannan ya na da ga cikin dalilan da suke sa Tanti ke son Jummai mai aiki, domin mace ce mai barkwanci da raha, kuma ta kan shawo mata kan Fatima da yan biyu a duk lokacin da suka soma rigimarsu ta shagwaba.

  Amina Sidi Ali ƙawar su Fatima sai sha'awar su Afrah ta ke yi, ta na faɗin "Ina ma a ce waɗanna ƙannai na ne masu kyau haka? Fatima maimakon ki na ji da su." Ko ta kan Amina Fatima ba ta bi ba bare har ta ba ta amsa. Sai ma cewa ta ke. " Momi ina kika samin sauran Madara ta Kwasam da kilishina, dan babu wadda zan sammawa.” Tanti ta du beta " harda Fafilarki? " Ta ce "Har ita Ba Bellona da Mammata su ka kawo min fa, kuma Fadila ko kallon Ba Bello ba ta yi ba bare ta gaida shi ya zo tun daga Maraɗi dan kawai ya ganni.” Fadila ta ce "Lah! Ashe shi ne? To ai laifin ki ne da baki gabatar min da shi ba, sannu da zuwa Ba Bellonmu." Yadda ta yi abin sai a ka sa dariya har shi Ba Bello.

  Amina Sidi Ali ta ce “Ina miki maganar yan biyu kin min banza." Fatima ta ce “Hakan zai sa ki fahimci ni ɗin ba na son zan can ne.” Amina zata yi magana Fadila ta riga ta da cewa “Ke Amina kin fi ye da mu.” Bello ya ce “Ke ce babbar ƙawarmu ko?” Fadila ta ce “Aminiya dai.” Tanti ta katse musu hirar da faɗin “Kun ji mafi sauki ka wai mu yi sallah, mu kama hanya.” Fatima ta ɓa ta fuska tare da faɗin “Haba Momy ku kwana mana, anjima in lokaci rufe ziyara ya cika ba sai ku je Tahir guest ba, tun da lokacin da zaku kawo ni, ai a Tahir din kuka yi ta kwana sai da a ka gama min komai.” Momy ta ce, “Amma lokacin yan biyu suna jarirai.”

  SHAFI NA 4

  “Daddy dai ba ya son tafiyar dare, na sani ko yanzu ba da yawun sa za a yi wannan tafiyar ba.” Bello cikin dariya ya ce “Fatin Mamma kin fi Tanti gaskiya, mu ne mi masauki kawai.” Tanti ta ce “Ai dole in hakura tun da kun fini baki.” Haka dai suka zauna har zuwa lokacin da aka tsara cewa lokacin ziyara ya ƙare, dan haka suka kama hanya suka shiga cikin gari, dan neman masauki kafin washegari su kama hanya.

  A hanya ne Bello ke nuna wa Tanti mamakin shi na canzawar Fatima matuƙar canzawa. Tanti ta ce “Ai kullum girma ta ke yi, kuma wannan makarantar ta su ƙwarai ta taimaka, karatun addini su ke yi sosai sauka da hadda kamar yaro ya na gaban iyayansa, ga tsafta kuma ladabi abin har mamaki ya ke ba ni, na sama ya na tausayin na kasa, shi kuma na kasa ya na girmama na sama, kuma abinci kamar na gida. Kifi, nama, kayan marmari, irin su lemo da ayaba, kankana, kai hatta da agwaluma Fatima ta ce min in lokacin ta ya yi ana kawo musu.”

  Bello ya ce “Gaskiya makarantar ta yi, su na da tsari da kula ga tarbiyya, amma duk da haka na yi matuƙar mamakin canzawar Fatin Mamma, to kuma me ya samu idanun ta?” Tanti ta yi saurin duban sa ta ce “Bello dan Allah ka dai na yin zancan nan musamman a gaban Fatima.” Haka Bello ya sake yin shiru zuciyarsa cike da tambayoyi, amma babu wanda zai bashi amsa.

  ******

  KADUNA

  Cikin sauri yarinyar ta fito daga wanka, daure da tawul dogon gashinta nade a cikin karamin tawul, da rawa gami da waka ta fito daga banɗakin, gaban madubi ta zame tare kallon kanta, ta na ci gaba da rawar, wakar ta na tashi daga cikin wayarta, wadda ke aje a kan gado ta ke bi.

  Cikin yanayin rawa da waka ta yi duk shirinta, tun daga shafar mai har zuwa saka kayanta matsatstsun riga da wando ta saka tare da daure gashinta a tsakiyar kai ta kuma fesa turaruka, ta tsugunna ta na daura takalma masu dogayen igiyoyi har kwaurinta, sannan ta dauki ƙaramin mayafi ta yane kanta, tare da kallon madubi sannan ta ware manyan idanunta ta kalli suffarta, daɗi ya rufe ta ta sumbaci yatsunta ta hura a madubin tare da faɗin, “Gaskiya na yi kyau! Ina da kyau! Allah na gode maka ina son kai na.” Ta faɗa cikin murna da farin ciki, tana ɗaukar wayarta ta na soka earpiece a kunnuwan ta, sai ga kira ya shigo cikin sauri ta ɗaga ta na “Faɗin oga BY gani nan fitowa ."

  Daga ɗayan ɓangaren ya ce “Yawwa dan Allah ki yi sauri yau studio ɗin akwai mutane da yawa.”
  “Toh! Gani nan zuwa.” Ta dire maganar, tana nufa kicin in da mahaifiyarta ke shirin dora girkin dare. “Mama na tafi makaranta sai na dawo.” Ta faɗa daidai lokacin da ta ke gyara yar igiyar jakarta, da akewa lakabi da wankan gefe.

  Tun daga sama Uwar take kallon ta har kasa, ta ke fuskarta ta canza. "Amma na hanaki saka kananan kayan irin haka ki fita ko da kofar gidan ko?” Ɓata rai ta yi tare da turo baki ta ce “Haba Mama yanzu ina laifin kayan nan? Kin gani fa ko ina nawa a rufe ya ke.” “Wuce ki je ki saka hijabi ki zo in gani.” Uwar ta faɗa a fusace.

  Ciki ta koma ta na ƙunƙunai “Ita Mama ba ta ganewa ta ya ya mutum zai zama tauraro, in ba ya na shigar suwaga irin haka ba?” Ta sako katon Hijabi sannan ta koma cikin kicin din tana cewa “Gashi na saka.”

  Murmushi ta yi tare da kallon ta ta ce “Ko ke fa Mamana! Wannan ita ce shigar mutunci da addininmu ya amince, waccan shigar da ki ka yi irin ta marasa tarbiyya ce.” Ƙare tamke fuska ta yi, cike da jin haushi hatta maganar da ta yi ma ciki-ciki ta yi shi “To ni na wuce.”

  “Allah ya tsare Mamana, ki kula da kanki ki nutsu ki fahimci karatunki.” Da gudu ta fita ta na fadin “To Mama.” Sakamakon rurin da wayarta ke yi ta san oga BY ne ta daga ta na faɗin “Gani a bakin Gate.” Da gudu ta isa tare da bude gaban motar, cikin azama ta fada tare da rufe ƙofar, ta dube shi daidai lokacin da ya figi motar “Yi hakuri babban Yaya na bar ka tsaye.” Ya ce "Haba babu komai ina son dai mu yi beating tima ne, dan sun fada min akwai mutane kin gane ai?” Ya yi maganar cikin irin salonsu na matasa, yan wanka kuma sabbin mawakan hip hop. Ta cire hijabin jikinta ta wurga a kujerar bayan motar tare da faɗin “Mama ta matsa.” Ya ce “Sunan hijabin kenan?” Suka tuntsire da dariya a tare. Ta ce “Yanzu dai na raɗa masa.” Ya ce “To ni dai na yi mamaki a ce ke ce cikin wannan hijabin har ƙasa, farko ma da kika shigo na so in tsorata.” Suka ƙara tintsirewa da dariya, suka saki sauti suna bi su na rausaya.
  Kai tsaye daga Unguwar Malali suka nufi Mogadishu, in da studio da za su buga wakar yake maimakon makarantar koyon na'ura mai kwakwalwa...”

  Ku latsa nan don ci gaban labarin. Ku bi labarin a sannu dan yanzu muka soma.

  Taku har kullum

  HALIMA K/MASHI

  Na gode.

Comments

1 comment