Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » Illar Furuci 2 Na Halima Abdullahi K/Mashi

Illar Furuci 2 Na Halima Abdullahi K/Mashi

 • Ku latsa nan don karanta labarin shafi na 1 zuwa 4.

  SHAFI NA 5

  Cikin farin ciki yarinyar ta sauka a kofar gidan su su ka yi sallama da BY, lokaci kannanta sun dawo da ga masallaci sallar isha i. Faruk Ya ce "Yaya Fati ashe bakya zuwa makaranta, to Baba ya na ciki ya na jiranki." duk da cewa gabanta ya yi mummunar faduwa amma sai ta da ke, ta zabga masa harara tare da fadin "Zan mare ka Faruk! Ni tsararka ce?" Ya sa yatsunsa guda biyu ya kama lebunansa. Ta ja tsaki sannan ta nufi ciki. Ya bi ta a baya ya na fadi a hankali "Wata za ta sha fada." Dakin Mama ta nufa kai tsaye, ta samu Mama ta na salla dan haka ita ma sai ta nufi dakinsu dan ta yi salla. A dakinsu ta samu Nafisa ta na salla, sai da ta sha rawarta sannan ta zo za ta wuce ta gaban Nafisar, cikin sauri ta yi alamar karta keta mata gaban salla. Ta ce "Sorry sannan ta koma ta bayanta ta fada bandaki dan dauro alwala. Ta idar da salla sannan ta sake nufar dakin mama dan tabbatar da abinda Faruk ya fada mata. Sam ba ta son duk wani abu da zai bata ran Mama.

  Tana fitowa bakin kofa mama ta na isowa, dan haka su ka yi kicibis a bakin kofa. Gaban Fati ya fadi. Ta ce " Mama sannu da gida, na dawo ki na salla ne. Mama ta ce "Muje ciki." Ta kalli Nafisa wadda ke karatun azkar dinta na yamma. Ta ce " Ki je ki zuba wa su Faruk abinci kema ki sa, zanyi magana da yayarku. Nafisa ta mike a hankali ta fita. Mama ta kalli Fatima. " Kinsa bana son karya ko kame kame ?" Fati ta ce " Na sani Mama." Ta ce " To fada min gaskiya ina ki ke zuwa da sunan makaranta?" Fati ta zaro ido "Ina kuwa za ni Mama." Mama ta daga murya "Amsa za ki ba ni Fatima ba ki jeho min wata tambayar ba."

  Cikin Fati ya kada domin in ba yau ba Mama ba ta taba kama sunanta tsirara haka ba. Duk da ba ta son yiwa Mama karya dole ne ta yi ko don ta baiwa burinta kariya na zama shahararriya Domin tasan yanzu mama za ta ka tse ma ta burinta hakuri kawai Mama za ta yi. " Bangane hakuri zanyi ba." Fati ta zaro ido ko dai ba a zuci take nazarin ba. Mama ta ji dukkan tunaninta ke nan! Inko haka ne lamari ya baci.

  Mama ta tashi ta dawo kusa da Fati ta zauna ta tausasa murya tare da dafa mata kafada. "Uwata na shede ki bakya karya ki fada min ko kin fara bin wani ne?" Da sauri ta dubi mahaifiyar tare da fadin Allah ya tsare ni Mama karki min wannnan fatan." Mama ta ce to " 'Ya ta fada min ina ki ke zuwa?" Fatima ta sunkuyar da kai "Makaranta na ke zuwa Mama, waye ya ce ba na zuwa?" Mama ta ce "Babanku ya je har makarantar fa." Fatima ta ce "Mama kin san Baba fa kullum ya na neman laifina ne, ga su Nafisa nan ba ya cewa ga abinda sukayi, ni bànsan dalili ba Baba ba ya so na." Uwar ta kama hannun yar "Haba 'ya ta, kin taba ganin uban da baya son 'yar sa? Ke ce kin cika rawar kai dole ya sa ido sosai a kanki, kuma na hanaki yin zantukan rashin ladabi ga mahaifinki." Fati ta ce "To kiyi hakuri Mama gaskiyar magana ina zuwa makaranta." Mama ta mike "Shike nan amma ki kula sosai kuma ki dage."

  SHAFI NA 6

  Fati ta shiga rawa bayan fitar Mama bata da matsala in dai Mama ba ta fushi da ita, sai dai kuma ta san dole ne wata rana asiri ya tonu, dan gaskiya duk rintsi sai ta yi halinta domin karya fure ta ke amma ba ta 'ya'ya.

  Uban ya jima tsaye ya na kallon yadda Fati ke rawa a kan gado tare da rera wakar da su ka yi dazu. "Subahanallahi! Fatima ta tsaya can cikin fargaba. Ya ce " Lallai kullum shedancin ki ga ba ya ke yi, to ko koyon rawar ki ke zuwa ne ki ke karya cewa kina zuwa makarantar koyon computer? " Ta soma kir kirar kukan karya. "Can ni ke zuwa Baba kila ba gurin kaje ba." Ya shiga dakin a fusace ya yin da ta nufi bandaki da gudu. Ya ce " Inje in yi miki rijista da hannu na amma ki na fada min cewa ko ba can na je ba! Nufin ki gurin ya ma ba ce min kenan? Sun fada min cewa tun da aka sa ki a makarantar ba ki yi zuwa ya kai biyar ba. Ta ce "Karya su ke min gobe mu je tare tunda karya za su yi min." Ya ce "Ke za ki fada min a bin da ya kamata inyi? Uwarki ta goye miki baya dole ki ce kina zuwa abinda ki ke so shi ki ke yi, dan haka ba zan dauki rashin mutunci da zub da mutunci a idon duniya ba. Ya juya ya fita ya na me ci gaba da fada.

  Da safe duk su ka fito cikin kayan makarantar boko na Kaduna Capital school Fatima ce babbarsu ta na aji biyu na babbar sakandire Nafisa ta na aji uku na karamar sàkandire, Faruk ya na aji daya, sukuwa Amir da Kabir duk yan primary ne. Kabir ya shige gaban mota shi da Amir. Nafisa ta ce " Baba ba ka bamu rasit din da ka biya mana kudi ba, yau za a iya ha na mu shiga aji. " Ya ce "Ai kuwa gara da ki ka tuna min Faruk yi gudu ka ce Mamanku ta duba kan durowar gefen gadona ta dakko maka. Ya tafi da gudu ya yin da shi kuma Baban ya dubi Fatima zan dawo daukarku zanje ajujuwanku da kai na kuma ni zan kai ki computer school din za ki ga ne kurenki. Fatima ta zaro ido ta tuna in har Baba zai je ajinsu yanzu to kuwa akwai matsala. Domin ta gudu a ajin kusan so hudu a satin nan su na zuwa gurin kallon daukar wasu sabbin wakoki da za a fitar da video din su domin ta na son ta samu kwarewa so sai, in sun tashi daukar na su ta riga ta gogu. Nafisa ta yi murmushi "Baba zan ji dadi in ka je da kanka ka kai rasit din ba sai munbi layi ba, in iyayen yara su ka zo anfi kula su. " Faruk ya ce " E mana." Fatima dai ta kasa magana sai zaro ido take cikin far gabar abinda zai je ya dawo.

  Abuja

  Tanti Dije ta na fitowa wanka cikin sauri ta shirya ba ta son mijinta ya karaso ba tare da ta shirya ba, domin Habu direba ya tafi dakko shi da ga filin jirgin sama, ya dawo da ga Lagos. Ta na fesa turare ta jiyo muryarsa ya na fadin "Hadiza!" Cikin sauri ta nufi dakinsa Indi ta jiyo muryarsa da ga can. Ta shiga ta samu ya na kokarin cire malun-malun , cikin sauri ta nufe shi ta na fadin "Sannu da zuwa yallabai sannunka da hanya." Ya shafi kumatuta "Sannu da wanka Hadiza kina ta kamshi." Ta kama hannunshi "Bari in ta ya ka cire kayan domin na san kaima wankan ka ke muradin yi ko?" Ya ce " "Ba ni ne zanyi ba, matata ce za ta yi min don na gaji ." Ta ce "Aiki na ne mijina muje in maka yanzu." Bayan ta gama masa ta baro shi ya na alwalla domin dab a ke da kiran magariba, ta kalli ledojin da ke zube a kan gado duk kayan tarkace ne na tsarabar yaran, kayan zaki da kayan wasa. Ta yi murmushi " Oga kenan shi dai duk inda ya je sai ya yo wa yan biyu tsaraba." Ta nufi gurin da ya ke aje jallabiyunsa ta ciro masa daya mai gajeran hannu da gajeran wando ta feshe su da turaruka masu kamshi ta aje a kan durowar gefen gadon wadda ke daf da kofar bandakin, ta ciro Laptop din sa daga cikin jaka ta aje gurin da ya yi mata mazauni. Ya fito ya na saka kayan gami da tambayar "Ina yan biyu na?" Ta ce "Za ka gaji da su yau domin sun sha baccin rana."

  SHAFI NA 7

  Ta zauna a bakin gadon tare da janyo ledojin "Kai kam ko ina kaje sai kayi tsaraba?" Shima ya zauna. "Wannan tsarabar da ga Hajiya Maimuna taki ta ke, ta ce a kaiwa yan biyunta." Ta daga ta na fadin lallai Hajjaju, ta gidan ka bi ke nan?" "Ya ce " Ba na fada miki na je duba Hajiyar Alhaji Kabiru da jiki anyi mata aiki a ido ba, kinsan ta na gidan sa gurin Hajiya Maimuna." Ta ce "Ai ka kyauta dubi lokacin da Mamma tayi ciwon nan shi ne har Maradi ya je duba jikinta." Ya ce "Alhaji Kabiru ya wuce aboki sai dai dan uwa na jiki." Ta ce "Tabbas haka ne tamkar dai ni da Hajiya Maimuna." Ya mike tare da fadin bari in dawo daga masallaci insha labarin Uwata Fatima na san ta sha fushi banje ba." Ta saki dariya tare da fadin "Kai Uwarnan ta ka da fitina ta ke, gashi Bello ya so ya tsokalo mana sama da tsinke ya cire mata gilashi ya na neman ba a sin yaya a ka yi idanunta su ka koma haka!" Ya rike baki "Tofa!" Ta bi bayansa ta na bashi labarin har su ka sauka kasa, ta raka shi har kofar falon kasa ya nufi masallaci.

  Da kanta Tanti Dije ta ke jera kayan abincin Jummai me aiki ta na miko mata daga katon tiren da ta jero su. Duk da shekaru sun ja sam Tanti ba ta wasa da kula da mijinta wan da ta ke kallo kamar jiya aka daura musu aure, burinta guri ya yi tsaf kafin ya dawo salla dan in ya fita magriba sai bayan isha i ya ke dawowa domin su na daukar karatu a tsakanin magriba da isha 'i a gurin limamin masallacin wanda ya kasance makocinsu ne, duk da ba su da yawa bawan Allahn ya jure gurin samun ladansu, haka suma sun jure koyo matsawar su na gari.

  Aka kwankwasa kofar falon ta dubi Jummai wadda ta kawo su Afra da Afrin sun sha gayu cikin wasu tsadaddun riguna da takalma sai ka ce za su je gidan shi a ni. Ta ce "Ki duba ana kwankwasa kofa."
  Ya shigo sanye cikin kananan kaya ya yi kyau dan matashi Ashir kenan dan wan Tanti Dije ne. Ta kalle shi da fara a "Ashir daga ina haka kamar an jeho ka?" Ya nufi kujera daidai lokacin da su Afrin su ka ruga su ka kama kafafunsa su na fadin "Oyoyo Yaya!" Ya dora su a hannuwa kujerar da ya zauna gefe da gefe ya na fadin "Daga gida nike Mami ina yini."

  Nan suka gaisa, ya mikawa yanbiyu wayarsa da su ke ta kokarin amsa da ga hannusa, sannan ya soma antayo korafinsa ga kanwar mahaifin nasa. "Mami ba dole inzo a wannan lokacin ba, don Allah mami ban ji dadin yadda kuka min ba." Ta tattara hankalinta gareshi. "Me a kayi ne dana fadamin inji." "Kuka tafi ziyarar Fatima bayan kin san na ce zanje." Ta yi dan tsaki gami da sakin dariya. "Har ka fadarmin da gaba, na zaci wani abu ne daban da na ga duk ka marairaice." Ya ce "Mami kin san dai ina son Fatima sosai zan iya rasa rai na a kanta bana son a samu matsala ne Mami dan Allah." Ta danne rashin jin dadin kalaman nasa ta yi dan yake. "Ka gane ko Ashir ka bi a hankali na fada maka ka saurara da wannan zancan domin fa sanin kankane Fatima ta tsani jinsin maza musamman wanda zai kusanto ta, ina son ka sani Fatima ta na da mabanbancin ra ayi da sauran mata in har ka yi kuskuran bayyana manufarka har ta gane to babu shakka za ta yi maka tsana mai tsanani....

  Ku latsa nan don ci gaban labarin.

  Taku, Halima Abdullahi K/Mashi

Comments

0 comments