Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Cutar Kanjamau: Abubuwan da ya kamata ku sani game da cutar

Cutar Kanjamau: Abubuwan da ya kamata ku sani game da cutar

 • Matashiya

  A fadin duniya an ware ranar daya ga watan Disamba a matsayin ranar wayar da kai kan cutar AIDS ko Sida ko kuma cutar Kanjamau a duniya. Majalisar Dinkin Duniya ta ce rana ce da duka kasashen duniya za su hada kai don nuna goyon baya ga mutane masu fama da wannan cuta ta AIDS, sannan a tuna da mutanen da suka rasa rayukansu dalilin wannan cuta.

  Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mutum miliyan 38 ne ke rayuwa da cutar a duniya. Sannan mutum miliyan daya da dubu dari bakawi ne suka kamu da cutar a wannan shekarar. Sai dai ta ce akwai wasu mutum sama da miliyan 25 da ke da damar amfani da magungunan cutar Aids.

  Cutar Aids kan samu ne idan kwayar cuta ta HIV ta shiga jikin mutum ta raunana garkuwar jikinsa. Idan garkuwar jiki ta yi rauni, mutum zai yi saurin kamuwa da wasu cutukan kaman cutar TB da wasu nau'ukan daji. Ana kammuwa da cutar HIV ne ta hanyar saduwa ko ta jini. Misali amfani da allura ko reza ko wani abu mai tsini da mai dauke da cutar ya yi amfani da shi ya yanke. Ko ta rauni ko a jiki.

  Sai dai a shekarun baya, kwararru sun samar da magungunan da ke hana kwayoyin cutar HIV bunkasa a jikin mai dauke da ita.

  Ku ranta wannan Makala da ya yi bayani akan cutar asma

  Ma'anar Cutar Kanjamau.

   Da farko dai kalmar AIDS na nufin Acquired Immunodeficiency Syndrome, ma’ana cuta mai karya garkuwar Jiki da take yaduwa. Ita kuma kalmar HIV na nufin Human Immunodeficiency Virus (ma’ana Virus mai karya garkuwar Jikin dan Adam). Ita AIDS ita ce cutar, HIV kuma shine mai jawo cutar ko kuma virus din.

  Cutar AIDS ko Kanjamau cuta ce ta mutane mai karya garkuwar jiki (Immunodeficiency syndrome) wadda ta ke faruwa sakamakon shigar kwayar halittar HIV virus, a cikin jikin mutum.

  Alamomin da ake gani wajen masu wannan cuta

  Mafi yawan mutanen da su ka kamu da cutar HIV kan ji alamomin mura musamman makonni biyu zuwa shidda bayan daukar cutar. Bayan wannan, bincike ya nuna ba lallai a sake ganin wasu alamomi ba har sai bayan shekaru masu yawa. Alamomi sun hada da;

  • Zazzabi
  • Ciwon wuya
  • Ƙuraje a jiki
  • Kasala
  • Ciwon gaɓoɓi
  • Kaluluwa a wasu sassan jiki.

  Bayan wadannan alamomin na farko-farko sun bace, ba lallai a sake ganin wasu alamomi ba. Wanda daga karshe take kai ga mutuwar marar lafiya. Kuma tana yaduwa ta hanyar jima’I da mai dauke da cutar; haduwar jini (ko wani daga ruwan jiki kamar maniyyi) ta hanyar gurbatattun kayan aiki kamar reza, wuka, almakashi, allura, da dai sauransu. Amma dai, kamar yadda alkalumma suka nuna, kashi 95% na yaduwa ne ta hanyar jima’i da mai dauke da cutar.

  A wannan lokaci, kwayar cutar tana ci gaba da lalata garkuwar jiki. Da zarar garkuwar jiki ta durkushe, alamomin da za a iya ji su ne:

  • Rama
  • Gudawa ba kakkautawa
  • Zufa cikin dare
  • Yawan kuraje a jiki
  • Manyan cututtuka masu hadari

  Gano cutar HIV a kan kari na rage yiwuwar lalacewar garkuwar jiki. Sannan a shekarun baya, kwararru sun samar da magungunan da ke hana kwayoyin cutar HIV bunkasa a jikin mai dauke da ita.

  Ku karanta: Tambayoyi da amsoshi 10 game da cutar coronavirus

  Alamomi

  Bayyanar alamomin Cutar Kanjamau ya kan sha ban-ban a tsakanin mutane. Bayan shigar kwayar cutar virus na HIV, alamomi kan iya fara bayyana daga watanni kadan har zuwa shekaru goma ko sama da haka. Wannan kuma ya ta’allaka da yadda shi virus din ya habaka ya kara yawa, da kuma karfin garkuwar jikin mutum da kuma irin yanayin rayuwarshi. Amma dai alamomi na farko-farko sun hada da yawan gajiya, zazzafi ko masassara, ciwon kaluluwa (lymph nodes enlargement) ko kumburin hamata, kyuibi, mara, da kuma makwallato (sore throat).

  Za ka ga mutum ya gaza aikin da da can yakan yi shi cikin sauki! Idan cutar ta ta’azzara, toh, sauran kwayoyin cuta kamar su bacteria da fungi (hunhuna) da kuma tsutsotsin jiki (parasites and worms) za su samu dama su habaka, saboda garkuwar jiki ta yi rauni. Karshe cutuka kamar tarin Fuka, amai da gudawa, kurajen jiki, da kuma kurajen al’aura duk za su bayyana. Akwai dai alamomi barkatai, da za su iya shan banban daga mutum zuwa mutum.

  Yaya ake gane mutum yana da AIDS

  Ana iya ganewa da tabbatarwa ne ta hanyar yin bincike a dakin binciken asibiti, kuma a tabbatar da hakan daga bakin kwararren likita!

  Magani

  Maganar gaskiya, har yanzu ba’a samar da shakikin maganin cutar Kanjamau ba. Sai dai akwai magunguna masu karfi da suke rage kaifin cutar, kuma su hana kwayar virus habaka. Amma dai basu kawar da cutar gaba daya. Wani hanzari ba gudu ba, su ma kuma magungunan, suna da illa mai tsanani, domin su kan haifar da wasu cutuka idan aka yawaita shansu. Kuma dole ne a sha su, in har ana son mun dan sauki-sauki.

  Riga kafi

  Haka kuma, kamar yadda ake yi wa cutar kyanda, sankarau, polio riga-kafi, ita Cutar AIDS ba a mata riga-kafi, duk da cewa har yanzu ana kan bincike akan hakan. Amma dai babban riga-kafi da kuma kariya daga Kanjamau sun hada da:

  • Barin yin alakar jima’i da karuwai, matan banza ko mazan banza
  • Tabbatar da kiyaye hakkin juna tsakanin matar aure da mijinta kamar yadda addini ya shinfida
  • Yin awo a asibiti don tabbatar da kubuta daga wannan cuta. Musamman ga mutanen da suke da niyyar aure, don kawar da zargi (idan har zargi zai iya shiga ciki. Wannan mas’ala ce wadda malamai sun yi bayani akan halaccinta).
  • Tabbatar da tsabtace kayan aikin asibiti kafin a yi aiki da su akan wani mutum daban.
  • Zubar da sirinji da taallura da sauran kayyayakin amfani-daya (disposable)a cikin shara tare da kone su a cikin wuta.
  • Nisantar yawan musayar kayan aiki kamar reza, wukar aski, clipper, alkamakashin yankan farce, har sai bayan an tsaftace su da wuta ko da Dettol ko makamantansau.
  • Nisantar duk abinda zai kai mutum aikata zina ko wani makamancin haka.

  Cutar HIV ita ce take zama AIDS kuma tana yakar garkuwar jiki mai kare mu daga cututtuka. Kanjamau dai ba'a santa a da ba, sai shekaru 40 da suka wuce, an gano cewa virus ke jawo ta.

  Dubi: Abubuwan da ya kamata ku sani game da zazzabin cizon sauro

  Alamomin da ke nuni da wata kila cewa mutum na dauke da wannan cuta

  • Zazzabi da ya ki ci ya ki cinyewa. Idan ana jin hakan har makonni bayan shan magani a je a yi tes na cutar kanjamau.
  • Ciwon makoshi, wanda ake kira sore throat, idan ya hadu da sauran alamu, a binciki lafiya.
  • Kurarraji a fata.
  • Gumin dare bayan mutum na cikin ni'ima
  • KalKaluluwa
  • Yawan ciwon jiki da gabobi.
  • Gajiya da raki, bayan ba'a yi aikin komai ba.
  • Barkewar zawo.
  • Yawan ciwon kai, maras dalili
  • Amai ko tashin zuciya.

  A kula: Ba wai kawai don mutum na daya ko biyu daga cikin wadannan wai lallai yana da cutar ba, a'a. Kawai dai idan sun hadar wa mutum farat daya a jika, masana kan ce a je ayi bincike, ko a tari cutar da wuri, idan har ita ce.

  Anan zan tsaya. Ina rokon Allah Ya bamu lafiya da zama lafiya, Ya kuma kare mu da duk al’umma daga kamuwa da muyagun cututtuka, Amin.

  Rubutawa: Maryam Haruna, Registered Midwife, daga Zamfara, Nigeria

Comments

0 comments