Makalu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Yadda al’adun aure ke gudana a kasar Nijar 1

Yadda al’adun aure ke gudana a kasar Nijar 1

 • Mun tattaro muku bayanan wannan makala ne daga shirin Mutum da Al’adunsa, wanda Nana Aicha Hamissou ke gabatarwa a Zauren Marubuta da ke Taskar Bakandamiya. Shiri ne da ke kawo bayanai mai zurfi game da al’adun mutane daban-daban a kasar Hausa da ma sauran kasashe da al’ummomi na duniya.

  A wannan karo ta yi bayani karon farko game da yadda al’ummar kasar Nijar, makwabtan Nigeria, ke gudanar da al’adun aure a kasarsu. Ta dauko tun daga tarihin yankunan kasar Niger sannan ta tsunduma cikin bayanan yadda saurayi ke gabatar da kansa ga gidan budurwa, da yadda ake kai kudin aure har kuma akai ga daurin aure da sauran al’adu da zai biyo baya.

  Ga bayaninta kai tsaye game da yadda ƙasar Nijar ke gudanar da shagulgulan aurensu.

  Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarkatuhu ƴan’uwa fatan na same ku lafiya.

  Barkanmu da warhaka barkanmu da saduwa da ku a cikin wannan shiri na Mutum da Al’adunsa, shiri da zai ke kawo musa bayanai na al’adun Hausa da sauran kabilu. A yau cikin shirin zan fara kawo muku al’adun aure a kasar Nijar.

  Kafin mu tsunduma cikin shirin zan kawo maku sunayen garuruwan Nijar da kuma wasu yarensu, sannan kowanne  gari da irin yarensu.

  Nijar ƙasa ce da take da garuruwa guda takwas da gunduma kimanin araba’in, ga su kamar haka: Niamey (Capital ta Nijar), Maraɗi, Zinder, Tahoua, Agadez, Diffa, Tillabery da Dosso.

  A cikin waɗannan garuruwan kowanne yana da yarensu, kamar misali Maraɗi gari ne wanda ya haɗa katsinawa da gobirawa, duk wanda yake ɗan asalin garin Maraɗi to Bakatsine ne ko kuma Bagobiri. Sai dai akwai sauran yaruka kamar Tagamawa, Adarawa, Arawa, Zabarmawa, Fulani da Buzaye, da sauransu. Kuma kowanne kabila idan suka tashi aure da irin al’adar da suke gudanarwa, zan kawo su daki-daki in sha Allah.

  Haka kuma Zinder gari ne na Damagarawa su ma da yadda suke al’adarsu.

  Niamey garin zabarmawa ne, amma gaban Niamey akwai wani gari mai suna Toroɗi can fulani ne, su ma da yadda suke al’adarsu ta aure.

  Dosso ma zabarmawa ne cikin garin amma dai suna da arawa cikin garin Dogon Dutci.

  Tillabery ma zabarmawa ne sai dai suna da fulanin Zabarmawa.

  Agadez garin Buzaye ne su ma da al’adarsu ta aure.

  Tahoua garin Adarawa ne suna da buzaye su ma.

  Diffa garin barebari ne su ma da al’adarsu ta aure.

  Sai dai gabadaya waɗannan garuruwan guda takwas na Nijar babu inda babu Hausawa a ciki sai kamar gari uku (Niamey, Dosso da Tillabery) su ne Hausawa suka yi ƙaranci a can, dan wasu ma babu abin da suka iya a Yaren Hausa, sannan kuma duk yarensu ɗaya ne wato zabarmanci.

  Wasu Hausawan in suka tashi aure suna daukar al’adar garin da suke ko da ba tasu ba ce, wasu kuma suna amfani da al’adarsu ta Hausawa domin gudanar da shagalin aurarrakinsu.

  Bari mu fara da Maraɗi kai tsaye. 

  Maraɗi

  Maraɗi gari ne wanda ya haɗa Katsinawa da gobirawa, da sauran wasu kabilu kamar: tagamawa, adarawa, fulani, buzaye, arawa, shuwa arab, zabarmawa, da barebari, gwarawa da sauransu.

  Wanda duk ya kasance ɗan asalin Maraɗi ne to zai tabbatar maka da bakatsine ne ko kuma Bagobiri. Katsinawa suna da sarkinsu wato Alhaji Ali Zaki (wanda ake kiransa da sarkin katsinar Maraɗi marewa Alhaji Ali zaki) wanda gidansa yake cikin garin Maradi.

   Haka suma Sarkin Gobirawa yana a cikin garin Tibiri-gobir wanda yake kilo meta uku (3) daga Maraɗi a hanya mai zuwa Yamai gaban asibiti wanda ake kira uwa da ɗanta (Mère et Enfant a faransanci) mai garinsu sunansa mai martaba Alhaji Abdu Bala Marafa.

  Gabaɗaya Tibiri gaskiya gobirawa ne ba kamar Maraɗi ba da ake samun sauran kabilu sai dai haka waɗanda aiki ya kawo nan garin.

  A Al’adar auren waɗannan mutanen waɗanda suke ƴan sarki akwai yadda suke gudanar da shagalin bikinsu na gargajiya, wasu sun bari wasu kuma suna kan bakansu har gobe suna yi.

  Za mu fara gabatar da al’adar aure ga waɗanda ba ƴan gidan sarauta ba kamar na sauran wasu yare da suke Maraɗi wato mu kenan.

  A wannan zamanin da muke ciki yawanci samari idan sun ga  budurwar da ta yi masu, wasu kafin su tunkareta da suna sonta sai sun fara yin bincike a kanta sannan su fara zuwa neman izinin zance a wajen iyayenta, wasu kuma kawai fara zuwa suke yi har sai sun daidata sannan su turo iyayensu a nema masu auren budurwa. Kowanne dai da yadda yake yi. Wasu kuma in har ba su tashi aure ba kuma suna son budurwa to sai su aika da kuɗin tambaya gudun kar wani ya riga su. Idan har saurayi yana son budurwa to kafin auren duk lokacin sallah ƙarama farkon azumi sai ya kai sikari(sugar) da kuɗin kayan sallah gidansu budurwa har zuwa lokacin da za a yi aurensu.

  Yadda ake kai kuɗin aure

  A nan Maraɗi in za a kai kuɗin ana kai wa gidan yayan uba, ko kuma gidan su amarya ɗin. Wasu da dare suke kai kuɗin auren wasu kuma da yamma.

  Idan za a kawo kuɗin aure a gidansu amarya ana dafawa dangin ango abinci mai rai da lafiya kamar kaji da lemo haka. Idan ma akwai hali irin sosai ɗin nan wasu har rago suke yankawa. Ya dangata dai daga halin gidan su amaryar. Ko kafin dangin ango su iso an gyara masu abincinsu an zuba cikin manyan kuloli an jere masu kuma an tanadar masu lemo.

  In dangin ango sun iso kamar iyayensa maza da mata da abokansa kuma duk suke zuwa cikin motoci.

  Za su zo da goro da kuɗi (kuma masu yawa fa tunda yawanci masu ƙaramin ƙarfi ne ma suke kai jikka ɗari biyar wanda ya kai kuɗin Nijeriya nera ɗari uku da wani abu, wasu kuma suna kai millions ya danganta dai daga halin miji), da kuma akwati. Wasu kuma suna kawo lefe cikin akwatina, wasu kuma suna kawo akwatina babu komai sai su ba wa amarya kuɗi ta siyi kayan da take so da kanta ta zuba ciki.

  Idan sun gama ba da kuɗi da komai sai a ba su abincin da aka dafa masu da kuma lemo su tafi da shi gida haɗe kuma da kuɗi wanda kamar tukwici ne haka.

  Yawanci waɗanda suke kawo kuɗi da dare to gidan amarya ba su wannan dafa abincin sai dai kuma su bayar da kuɗi tukwici ga waɗanda suka kawo, amma dai wasu suna dafawa.

  A nan za mu dakata sai kuma wani makon in Allah Ya kai mu. Mai gyara ko kuma ƙarin bayani ƙofa a buɗe take

  Taku, Real Nana Aisha Maradi

Comments

1 comment