Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Ra'ayoyi da Tahalili » Da wa ka ke mu’amala a shafukan sada zumunta?

Da wa ka ke mu’amala a shafukan sada zumunta?

 • Abu guda da mutum zai yi a yau wanda zai yi matukar kyautata rayuwarsa shi ne sa ido tare da tantance irin mutane ko shafukan da muke hulda da su a kan shafukan sada zumunta.

  Saboda me? Saboda suna matukar tasiri a rayuwarmu ta yadda suke sauya mana tunani ba tare da mun yi la’akari da hakan ba. Kamar ya? Saboda suna daga cikin masu cika tankin ilimi da tunanin da muke da shi su kuma sa mu daukar matakan da suke shafar rayuwarmu ta yau da kullum.

  Saboda haka yin nazari kan wadannan shafuka da ra’ayoyin da ake wallafawa a kansu ba abin wasa ba ne.

  Annabi (SAW) ya ce misalin aboki na kwarai kamar mai sayar da turare ne, ko bai sam maka ba za ka sha kamshi. Shi kuwa abokin banza kamar makeri ne, in ba ka kone ba, ka kwashi warin hayaki.

  A wannan zamanin da muke wuni a kan shafukan sada zumunta, abota ba sai kuna zama a gari guda da mutum ba. Yau kana iya kulla abota da mutane a kowane sassa na duniya kuma su zamo tamkar abokanmu na zahiri ta yadda suke debe mana kewa su ilimantar da mu su kuma nishadantar da mu.

  To kamar yadda mutanen da kake zagaye da su a zahiri ke matukar tasiri a rayuwarka, haka ma wadanda ka zagaye kanka da su kan shafukan sada zumunta suke tasiri. Saboda haka ku duba ku gani, masu shirme kuka zagaye kanku da su ko masu nagarta? Don kamar abinci da muke ci ne; idan ka ci mai kyau zai nuna, idan marar kyau ne ma za a gani. Abin da ka shuka shi za ka girba.

  Masana dabi'un dan adam sun ce abu mafi sauki da mutum zai yi domin ya sauya rayuwarsa shi ne ya yi tunanin wane irin mutum kake son zama, sannan sai ka shiga zagaye kanka da mutane masu irin wannan halayya ko ilimin da kake bukata. Kana son zama marubuci ne? To ka kasance kana bibiyar marubutan da kake alfaharin zama kamarsu. Kana son zama dan kasuwa ne? Kasance da 'yan kasuwa. Kana son fahimtar inda duniya ta dosa? Kasance da manazarta masu sa ido a kan wannan harkar.

  Sannan ana yawan cewa mutum ya nemi mentors wato mutane wadanda za su haska mana rayuwa ta hanyar sharwarwari domin cimma wani burin da muka sa gaba. To yanzu shafukan sada zumunta sun saukake hanyar samun mentors. Yau idan akwai wani da ya ke burge ka kana iya saka shi a cikin jerin mutanen da kake kira mentors ba tare da ma ya sanka ba. Ta hanyar bibiyar shafukansa na intanet kana dibar ilimin da yake wallafawa akai-akai. Ni kai na ina da tarin mutanen da nake kira "long distance mentors" wadanda nake yawan bibiyar rubutunsu domin na karu. Kuma na karu matuka domin sun ba ni kwarin gwiwar ci gaba da yin rubutu.

  Sannan ka hado da mutane masu mabambantan ra'ayoyi ba sai masu ra'ayi iri guda da kai ba domin gudun daukar tsattsauran ra'ayi a game da kowace irin harka.

  A wata shawarar da wani attajiri daga jerin masu kudin duniya, Charlie Munger, ya bai wa wasu daliban wata jami'ar Amurka da ake yaye, yake cewa: Idan kuna son ku bunkasa a rayuwarku, to ku guji daukar tsattsauran ra'ayi da kafewa a kan kowane irin batu. Ya ce kafin ku dauki ra'ayi a kan wani abu, to ku tabbata kun fahimci manyan hujjojin da dayan bangaren suka dogara da shi.

  Yin hakan zai taimaka wajen samun cikakkiyar fahimta kafin daukar matakan da ka iya sauya rayuwarmu.

  A duniyarmu ta yau ilimi ke aiki saboda haka kada ku yi sakaci wajen neman ilimi mai inganci domin gane inda duniyar ta dosa. Idan ba ka taba tantance jama'ar da shafukan da kake mu'amala da su ko kuma ka dan kwana biyu ba ka biyo ta kansu ba, to ka tabbata yau ka fara. Ka raba jaha da mutanen da ba su da abin yi sai gulma, zagi, da duk wani shirme don gudun daukar dabi'ar da ba za ta amfane ka ba.

  Rubutawa: Maryam Bugaje, daga Washington DC, United States

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta labarin Afuwa ƙwaya Ce, Ka Shuka Ɗaya Ka Girbi Goma. An yi wani attajiri da ke da dukiya mai yawan gaske, ana kiransa Abu Tammamu. Saboda yawan dukiyarsa, bai san iyakacin abin da ya mallaka na daga gidaje da gonaki da dabbobi da bayi da sauran kadarori ba. B...
 • Ku latsa nan don karanta shafi na 12 da 13. SHAFI NA 14 Tana isowa ta dubi Mama tare da mika mata wayar "Ga mamansu Sumayya za kuyi magana." Mama ta amshi wayar ta saka akunne ta na fadin salamu alaikum jin shiru yasa ta dubi fuskar wayar tare da fadin "La kinga ta katse." Fati ta amshi wayar ta...
 • Zamantakewar aure, zamantakewa ce mai wahala, matuƙar wahala kuwa. Sai dai da zarar ka fahimci tana da wahalar, sai ta zama mai sauƙi a gare ka. Domin fahimtar tana da wahalar shi zai ba ka damar neman iliminta. Shi kuma iliminta sai ya ba ka damar samun sauƙin ta. A shirinshi da ya saba gabatarwa ...
 • An haifi Olufela Olusegun Oludotun Ransome-Kuti a ranar Asabar 15-10-1938, a Abekuta ta jihar Ogun. Iyayensa manyan mutane ne domin Mahaifiyarsa Fummilayo Ransome-Kuti, 'yar gwagwarmaya ce, mai fafutukar kwato 'yancin mata. Mahaifinsa Isra'el Olodotun Ransome-Kuti, babban limamin coci ne, shugaban ...
 • Idan aka ce Hepatitis, to ana nufin ciwon hanta kenan a Hausance. Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta na...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Dogaro Ga Allah Jari. Cikin ƙasashen Mongol an yi wani babban Sarki mai yawan jarumai ana kiran sa Bihikatu. Shi wannan Sarki jarumi ne amma mugu ne na ƙin ƙarawa. Tun da yake bai taɓa yin afuwa ga wanda ya saɓa masa ba. Ba a taɓa ganin dariyarsa ba s...
View All