Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » Illar Furuci 4 Na Halima Abdullahi K/Mashi

Illar Furuci 4 Na Halima Abdullahi K/Mashi

 • Ku latsa nan don karanta shafi na 8 da na 9.

  SHAFI NA 10

  Kaduna

  Fatima kwance a falo ta na kallon tashar wakokin turanci, har kullum ta na son ta kara gogewa a fannin rawa domin nan gaba kadan ta na son ta fara wakarta ta kanta, wannan dalilin yasa ta matsawa kanta a duk lokutan da take gida kuma Mama bata nan, ta na amfani da wannan damar ta kalli tashar rawa ko da kannanta za suyi zuciya su bar mata falon. Kamar yau ma suna kallon wani cartoon wai shi Oscar osis sai, kawai ta zo ta canza tasha. Nafisa Ta ce "Haba Yaya Fati dan Allah wannan fa ba adalci ba ne fa." Fati ta ce " Ku baza ku gane ba, kunfi son kallo mara amfani gara ku bari in koyi abinda ya kamata harka ce ta girma, kuma TV dai sai an saka shi a kowane daki a gidan nan." Faruk ya tafi da dan kukansa dakin Mama ya nufa, Nafisa ta ce "garama ka hakura domin ba lallai Mama ta amshi uzrinmu akan Yaya Fati." Haka kuwa ya na cewa Mama kinga Yaya Fati muna kallon Oscar ta zo ta can... "Ka gama Homework din ka ne?" Mama ta katse shi da tambaya. Ya ce "Ai ana gamawa zan yi." ta ce to, je kayi."

  Wayar Fati ta yi ringing ta duba da sauri kawarta Sumayya ce.Ta daga tare da fadin "Shegiya Sumy ina kika shige kwana biyu?" Daga can Sumy ta amsa da cewa "Teema Celebrity ina kika shiga ne?" Fati ta ce " kin san yanzu na ke tunanin kiranki in fada miki munfa buga wakar nan, kuma zamuyi Videos kwanannan, an kusa haska ni." Sumy ta saki shewar murna sannan ta ce " Ke Teema kira na yi in fada miki gidan hoton nan na kan titin Isa kaita sun manna hotunan nan da mukaje muka dauka, amma na ki kadai suka manna a bangon gidan hoton ta kan titi."

  Ihun murna ta saki wanda ya sa Mama fitowa da sauri gami da rawar jiki ta na zaton ko wani abinne ya samu Fatin. Sai ta ji ta na fadin "Dole inzo ki raka ni in gani, gaskiya sun min komai wallahi na ji dadi sosai, kin ga nasara ko Sumy ina ji a jikina zan cimma burina zan zama tauraruwa." Juyin da ta yi cikin rawa sai suka hada ido da Mama, take ta ji gabanta ya fadi. Mama fuskar ta babu fara a ta ce "Menene aka miki da ki ke fadin za ki je ki gani?" Cikin in ina ta ce "Wannan ce fa da mukayi test ita ce na cinye Sumayya ke fada min ta amso min ne shine zan je in gani." Mama ta ce "Ban gamsu ba domin Sumayya yanzu ba a makarantarku ta ke ba, F.G.C Malali ta ke sannan ba Islamiyyarku da ya ba." Fati cikin fargaba ta ce Mama a Computer fa ni ke magana kinsan ta shiga makarantar ba na fada miki ba tun kwanan baya." Yadda Fatin ke magana ci ke da karfin gwiwa, sai uwar ta shiga waswasi kamar sunyi zancan. Ganin haka sai Fati ta samu kwarin gwiwar ci gaba da fadin. Test mukayi to shine ta ke min albishir." Mama ta ce Allah ya ba da sa a ni danaji kina fadin burinki har na tsorata domin na jima da sanin ki na son zama shahararriya amma ban san a wane fanni zaki zama ba. Na ce likita ko lauya ko malama duk kin ce ba daya. Ta ce "A computer zan zama." Mama ta ce "Allah ya taimaka, to kannanki kuma da kika canza musu tasha ki ka sa arnan nan kina kallo fa?" Ta ce "Na yi musu alkawarin TV kowa da tasa." Tsaki Mama ta ja sannan ta dauki remote ta canza zuwa sunna tv sannan ta ce ban da abin ki Mamana kina dalibar ilmi me zai hada ki da kallon rawa da waka?" Ki ke yin abin da kannanki za su koya. Fati ta ce "To Mama ni ce Uwarsu wata rana tunda ni ce babbar yaya.ko" Mama ta yi murmushi ta re da fadin "Insha Allahu" ta koma dakinta."

  SHAFI NA 11

  Washegari Fati ta nemin iznin Mama ta nufi gidan su Sumayya, da ke Unguwar dosa dan suje gurin mai hoto don ta ga hotunanta. Suna isa masu gidan hoto su ka amshi Fati cikin fara 'a da murna domin hotunan ta sun kawo musu mutane kowa ya zo kalolin salonta su ke yi. Sun bukaci in za ta yarda su kuma daukarta wasu kaloli amma da kaya irin na al 'adun yarukan kasar nan irin na Hausa Igbo Yoruba da sauran su.

  Take ta amince musamman da mamallakin shagon ya fada mata cewa zata iya samun talloli da ga kamfanoni in suka ga hotunan.Dama da kayansu nan suka nemi mai kwalliya, cikin sa'a ta na kusa, dan haka tazo ta shiga zayyanawa Fati kwalliya ciki gwanin ta. Haka duk shigar da ta yi sai ayi mata ado irin na kabilar sai kaga ta tashi tamkar su.An daukii hotuna sosai kuma sun amshi lambarta za su tura mata a wayar ta dan ta samu damar sawa a shafukanta sun ce za ta iya samu tallar ko da ga bangaren ta ne wa su za su tuntube ta.

  Sai kusan magariba sannan su ka bar shagon Sumayya ta na ta mitar za ayi mata fada. Suna fita Sumayya ta hauta da fada, ta ce amma gaskiya Teema ke banza ce, har yaushe zaki bari suyi miki hotuna ba tare da sun biya ki ba!" Ta zungure mata kai tare da ci gaba da fadin "Kudi fa za su nema da ke!" Fati ta yi shewa sannan ta ce " Nima suna zan samu ta dalilinsu, ki gane mana kawata nasara ke bina taurarona ya soma haske in ya fara kyalli, wayyo Allahna Sumayya nan gaba kadan cikin alfahari za ki ke fadin Teema Celebrity kawata ce lokacin ma wasu za su ce karya ki ke yi, amma in lokacin ya yi ki kira ni zan fidda ke in ce sa a hand's free in fada musu Sumy aminiyata ce."

  Tsaki Sumayya ta ja, "Ina tausayin ki duk ranar da Mama ta san abinda kike ciki." Fati ta gatsina fuska. "Na zaci zaki ce ya zanyi yanzu na yi dare, domin nan gaba din ai ba ta zo ba tukunna ko?" Sumayya ta ce ni dai ki raka ni gida ki fiddani a gurin Mamanmu." Fati ta ce nan fa daya, kowa tashi ta fishheshi nima fadan zanci, amma ga shawara, kawai ki ce bani da lafiya nima zance baki da lafiya." Sumayya ta ce "Ba zancan karya hoto na raka ki haka zan fada kema ya rage naki ko ki fadi gaskiya ko ki yi karya ita fure ta ke ba ta 'ya'ya." Haka dai suka rabu su na yiwa juna tsiya.

  Fati ta na isa gida ta shirga wa mahaifiyarta karya wai Sumayya ba bu lafiya har da su karin ruwa shi yasa ta kasa dawowa. Nan kuwa Mama ta tausaya wa Sumayya harma ta ce lallai ya kamata ta kira Sumayya ta yi mata sannu.Sai Fati ta ba da uzrin cewa wayarta ta mutu amma in ta yi chaji za ta ciro mata lambar Sumy din."

  Zan lumfasa a nan. Ku latsa nan don ci gaban labarin.

  Halimarku K/Mashi

Comments

0 comments